A karo na farko ne gwamnatin kasar Sin ta bayar da "takardar bayanin manufar kasar Sin dangane da harkokin Afrika a ran 12 ga wata. A cikin sama da rabin takardar bayanin nan, an bayyana yadda kasar Sin za ta kara karfin hadin guiwa a tsakaninta da Afrika daga manyan fannoni hudu wato harkokin siyasa, da na tattalin arziki, da aikin ba da ilmi da kimiyya da al'adu da kiwon lafiya da zamantakewar al'umma, da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Takardar bayanin ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai wajen kara bai wa kasashen Afrika taimako don sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasar Sin, za ta sa kaimi ga masana'antun kasar Sin da su zuba jari a kasashen Afrika, musamman ma idan halin ya yi, kasar Sin tana son daddale yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci a tsakaninta da kasashe da shiyyoyi na Afrika.
Shehun malami Lu Tingan, shugaban sashen nazarin Afrika na Jami'ar Beijing ya bayyana cewa, akwai albarkatun halittu masu rinjaye da ke shimfide a karkashin kasar Afrika tare da manyan kasuwanninsu, wannan yana da matukar muhimmanci ga kasar Sin don neman samun kasuwanni a fannoni daban daban da samun ci gaba mai dorewa. A bangare daya kuma a sakamakon ci gaba da kasashen Afrika suka samu wajen kara tabbatar da zaman karko a fannin harkokin siyasa cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasashen Afrika suna bukatar samun taimako daga wajen sauran kasashe don bunkasa harkokin tattalin arzikinsu.
Daga alkaluman da hukumar kwastan ta kasar Sin ta bayar, an gano cewa, a cikin shekarun nan biyar da suka gabata, jimlar kudade da aka samu daga wajen ciniki a tsakanin Sin da Afrika ta yi ta karuwa daga biliyan 10 zuwa biliyan 40 a ko wace shekara. Kasar Sin ta yi ta samun gibin kudi wajen yin ciniki a tsakaninta da Afrika a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ta haka kasashen Afrika sun sami makudan kudaden musaya.
Bayar da wannan takardar bayani zai taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika don samun moriya tare, musamman ma a wajen kara zuba wa juna jari mai yawa.
Bayan haka takardar bayanin ta nuna cewa, bisa bukatu da kasashen Afrika ke yi, kasar Sin za ta kara zuba makudan kudade wajen horar da Afrikawa a fannoni daban daban, alal misali aikin ba da ilmi da aikin soja da na hukuma da na likitanci da kuma yaki da bala'i da dai sauransu.
Kasar Sin ta riga ta kara kashe makudan kudade wajen horar da Afrikawa a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. A gun taron ministoci na biyu na dandalin hadin guiwa tsakanin Sin da Afrika wanda aka shirya a watan Disamba na shekfarar 2003, kasar Sin ta taba daukar alkawarin cewa, za ta horar da kwararru Afrikawa a fannoni daban daban da yawansu ya kai dubu 10 a cikin shekaru uku masu zuwa. A hakika dai, jimlar kwararru da kasar Sin ta horar da su domin kasashen Afrika ta kai 6400 a cikin shekarar 2004 da ta 2005 kawai.
Madam He Wenping, shugabar kungiyar binciken harkokin Afrika ta kasar Sin ta bayyana cewa, nan gaba wadannan kwararrun za su ba da sabon taimakonsu ga raya nahiyar Afrika.
Takardar bayanin ta kara da cewa, ya kamata, a sa kaimi ga yin ma'amala a tsakanin kungiyoyin jama'a na Sin da kasashen Afrika musammam ma tsakanin matasa da mata ta yadda jama'arsu za su kara fahimtar juna da amincewar juna da kuma hadin guiwarsu.
Malam An Yongyue, shugaban kungiyar nazarin harkokin Afrika ta kasar Sin wanda kuma ya dade yana aikin diplomasiya a Afrika ya bayyana cewa, ziyarar da manyan kusoshi na kasar Sin da kasashen Afrika suka yi wa juna da ma'amala da jama'ar ke yi ta yi a tsakaninsu sun kara zurfafa dangantakar dankon aminci da hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, akwai larduna da birane na kasar Sin sama da 50 wadanda suka daura abuta a tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen Afrika sama da 60. Irin wannan ma'amala da ake yi a tsakanin jama'a zai sa kaimi ga yin hadin guiwarsu a fannin zaman rayuwar jama'a da tattalin arziki da al'adu da sauran fannoni da yawa don samun ci gaba tare. (Halilu)
|