Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-13 20:14:52    
A karo na farko  gwamnatin kasar Sin ta bayar da takarda dangane da manufarta kan Afrika

cri
A ran 12 ga wannan wata, a karo na farko gwamnatin kasar Sin ta bayar da takarda dangane da manufar da kasar Sin take aiwatarwa a kasashen Afrika, takardar ta tsara shirin yin hadin guiwar sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen siyasa da tattalin arziki da al'adu da zamantakewar al'umma da sauran fannoni, ta kuma gabatar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokari don kulla da yalwata sabuwar huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare. Ina dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta bayar da irin wannan  takardar a farkon sabuwar shekarar 2006? Wadanne  abubuwa ne  takardar take kunshe da su? Kuma manyan al'amuran da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika nawa ne za su faru wajen yin ma'amalarsu? To ga cikakken bayani. 

Takardar nan takarda ce da ta bayyana cikakkun manufofin da kasar Sin take aiwatarwa domin kasashen Afrika a karo na farko tun lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, kuma takarda ta biyu ce da gwamnatin kasar Sin ta bayar dangane da manufata ta harkokin waje bayan da ta bayar da manufarta domin kawancen kasashen Turai a shekarar 2003 .Mataimakin ministan harkokin waje Lu Guozen ya bayyana cewa, an bayar da takardar a farkon shekarar da muke ciki, shi ne saboda ta cika shekaru 50 da soma huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Ya bayyana cewa, ran 30 ga watan Mayu na shekarar 1956, rana ce da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya a  tsakaninta da kasar Masar, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya  tsakaninta da kasashen Afrika, daga nan ne kasar Sin ta soma aikin da take gudanarwa kan  kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da kasashen Afrika. Kasar Sin ta zabi lokacin nan don bayar da takardar nan ne domin makasudinta shi ne  bayyana wa gamayyar kasa da kasa cewa, tana mai da hankali sosai ga aikinta kan kasashen Afrika da huldar diplomasiya da ke tsakaninta da kasashen Afrika, a sa'I daya kuma ta bayyana niyyarta sosai, wato ta yi fatan huldar da ke tsakaninta da kasashen Afrika za ta kara samun bunkasuwa sosai a karkashin sabon halin da ake ciki da sabon zamani.

Afrika, babbar nahiya ce da ke samun kasashe masu tasowa a cunkushe. A cikin shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya  tsakaninta da kasashe 47 da ke cikin kasashe 53 na Afrika. Amma ka'idar "Sin daya tak a duniya" ita ce tushen siyasa na kafa da kuma yalwata huldar da ke tsakaninta da kasashen Afrika. Takardar ta bayyana cewa, kasar Sin tana son kulla da kuma yalwata huldar kasa da kasa da ke tsakaninta da kasashen da ba su kulla huldar diplomasiya da ita ba bisa tushen nan .

A cikin shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin da kasashen Afrika sun sami sakamako da yawa wajen yin ma'amala da hadin guiwa a fannoni daban daban, musamman ma wajen tattalin arziki. Mr Lu Guozen ya bayyana cewa, bisa sabon halin da ake ciki, huldar gargajiya ta sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana fuskatar sabuwar dama mai kyau, shi ya sa kasar Sin ta bayar da takarda dangane da manufarta a kan kasashen Afrika. Ya bayyana cewa, musamman  takardar ta waiwayi gudanarwar da ake yi don sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma bayyana ra'ayin kasar Sin a kan matsayin kasashen Afrika da amfaninsu, kuma daga dukan fannoni ne aka tsara shirin yin hadin guiwar sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen siyasa da tattalin arziki da al'adu da zamantakewar al'umma da sauran fannoni.

Mr Lu Guozen ya takaita halayen musamman da kasar Sin take da su wajen ba da taimako ga raya tattalin arzikin kasashen Afrika. Ya ce, mun yi abubuwa cikin gaggawa domin biyan bukatun da kasashen Afrika suke yi , mun yi ayyukan ba da taimako bisa bukatun da kasashen Afrika suka yi, kuma mun yi ayyukan ba tare da kowane sharadi ba  kuma ba mu sa wa kasashen Afrika matsi ta hanyar ba da taimakon tattalin arziki.(Halima)