Ran 10 ga wata, kasar Iran ta fara aiki da tashar binciken makamashin nukiliya gadan gadan wadda ta daina aiki da ita har cikin sama da shekaru biyu da suka wuce, wannan ya jawo hankulan gamayyar kasa da kasa kwarai, bantun nukiliyar Iran wanda ya dan lafa kwanakin baya ba da dadewa ba ta hanyar maido da shawarwari ya kara zafi da sauri.
Mr Mohammad Saidi, mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran ya shelanta a ran 10 ga wata cewa, kasarsa ta riga ta bude tashar nukiliyarta da sanyin safiyar wannan rana, sa'an nan kuma ta sake fara aiki da ita gadan gadan don binciken makamashin nukiliya. Madam Melissa Fleming, kakakin hukumar makamashin nukiliyar duniya ta tabbatar a wannan rana cewa, kasar Iran ta bude tashar nukiliya ta Natanz ne yayin da sifetoci masu bincike na hukumar suke wurin. Haka zalika Mr Mohamed El Baradei, babban direktan hukumar nan shi ma ya bayyana cewa, bangaren Iran ya nuna masa cewa, yana son fara wani karamin aikin sarrafa sinadarin Uranium.
Bayan da kasar Iran ta sake fara yin aikin binciken makamashin nukiliya, sai hukumar makamashin nukiliya ta duniya da kasar Amurka da Britaniya da Rasha da Jamus da kuma sauran kasashe da kungiyoyi suka nuna damuwa da kulawa ga wannan, kuma sun bayyana cewa za su daidaita matsayinsu don magance lahani da za a samu daga wajen wannan al'amarin.
Manazarta suna ganin cewa, aikin nan na kasar Iran ya kalubalanci shawarwari na sabon zagaye da za a yi tsakanin kasar Iran da Kungiyar Hadin Kan Turai wato EU a ran 18 ga wannan wata. Tun bayan da aka fara yin shawariwarin tsakanin Iran da kasashe uku wato Britaniya da Faransa da Jamus da ke wakiltar kungiyar EU a watan Oktoba na shekarar 2003, an sha gamuwa da fadi tashi. A watan Agusta na shekarar bara, Kungiyar EU ta gabatar wa kasar Iran shawarwari da dama a kan bai wa kasar Iran hadin kai a fannin tattalin arziki da kimiyya da fasaha da shigar da ita cikin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO da sauran irinsu don neman ta da ta soke sarrafa sinadarin nukiliya cikin cin gashin kanta. Amma kasar Iran ta yi watsi da wadannan shawarwari, ta fara yin shirye-shirye don sarrafa sinadarin Uranium a ran 8 ga watan Agusta na shekarar bara. Ta haka an dakatar da yin shawarwari a tsakaninsu cikin watanni hudu ko fiye da suka wuce, ba a maido da shawarwarin nan ba sai a ran 21 ga watan Disamba da ya wuce.
Kasar Amurka tana goyon bayan kungiyar EU bisa shawarwari da take yi a tsakaninta da kasar Iran, idan an sami sakamako mai kyau a gun shawarwari, to, za su nuna farin cikinsu, amma in ba haka ba, to, kungiyar EU da Amurka za su yi kokari tare wajen gabatar da batun nukiliyar kasar Iran ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.
Kafofin watsa labaru sun bayyana cewa, bisa goyon baya da jama'a ke nunawa, kasar Iran tana ganin cewa, bisa matsayinta na wadda ta rattaba hannu kan "yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya", kasar tana da halalen iko sosai wajen yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. Babu yadda za ta yi kasar Iran ta kare matsayinta na babbar kasa a gabas ta tsakiya, sai ta mallaki fasahar nukiliya da kanta. Yanzu, kasar Iran tana neman cim ma makasudinta kan batun nukiliya bisa shirin da ta tsara.
Yawancin kafofin watsa labaru na Turai sun nuna bacin rai ga shawarwari da ake yi tsakanin kungiyar Eu da kasar Iran. A ganinsu, idan kasar Iran ta sake fara yin aikin sarrafa sinadarin Uranium a wannan gami, to, mai yiwuwa ce, shawarwarin za su bi ruwa. Kungiyar Eu ta riga ta fara shirin gabatar da shawara a kan yin taron gaggawa na majalisar hukumar makamashin nukiliya ta duniya don yin tattauna a kan matakai da kila za a dauka. Amma wasu kafofin watsa labaru na Turai sun nuna ra'ayinsu cewa, da yake kasar Rasha ta sanar da cewa za ta sake yin shawarwari a tsakaninta da kasar Irana a watan gobe kan shirin sulhu da ta gabatar, haka nan kuma kasashen Turai ta yamma ma za su sake jira cikin wani gajeren lokacin ta yadda kasar Rasha za ta taka rawarta sosai. (Halilu)
|