A ran 8 ga wannan wata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da shirin ko ta kwana na kasar don magance al'amuran jama'a da za su faru ba zato ba tsammani cikin gaggawa a dukan fannoni, wanann ya sa tsarin shirin ko ta kwana da kasar Sin ta tsara a kai a kai a lokacin da ta daidaita al'amuran jama'ar da suka faru ba zato ba tsammani a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce ya sami wata takardar da ke da ma'anar babbar manufa. Kwararun da abin ya shafa sun bayyana cewa, bayar da shirin ko ta kwana a dukan fannoni zai ci gaba da karfafa karfin gwamnati wajen ba da tabbacin tsaron kai ga jama'a da daidaita al'amuran da za su faru ba zato ba tsamamni, a sa'I daya kuma, matakin nan shi ne aiki mai muhimmanci da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen kara inganta aikin kula da harkokin zamantakewar al'umma da aikin samar da hidima ga jama'a.
Kafin ballowar annobar cutar SARS a shekarar 2003, kasar Sin ta tsaya kan matakan yin binciken a'amuran da za su faru ba zato ba tsammani kawai, amma a cikin lokacin da bai cika shekaru uku ba, a kai a kai ne aka bayar da shirin ko ta kwana na bangarori fiye da 100 da na yawancin larduna da jihohi. Shirin ko ta kwana da aka bayar a dukan fannoni a wannan gami ya kasa al'amuran da za su faru ba zato ba tsammani bisa matakai daban daban da iri iri daban daban, ya kuma tsara tsarin shirya ga gwamnati wajen magance al'amuran da za su faru ba zato ba tsammani, sa'anan kuma ya tsara ajandojin magance al'amuran da suka faru ba zato ba tsammani daga wajen bayar da labarai da nuna martani a kai da yadda aka daidaita su da yin bincike a kansu da kimantawarsu, a karshe dai zuwa matakin sake farfado da su. Direktan sashen koyar da ilmin kula da harkokin gwamnati na jami'ar jama'ar Sin Mao Shoulong ya bayyana cewa, wajen daidaita labarai, ya kamata a gabatar da al'amarin da ya faru ga majalisar gudanarwa ta kasar Sin cikin sa'o'I hudu, sa'anann kuma ya kamata a bayar da takaitaccen labari ga jama'a kafin sauran labarun da aka bayar, ciki har da matakin gwamnati na magance al'amarin da yadda jama'ar farar hula za su yi. musamman ma ya mai da hankali ga ba da tabbaci ga samar da kudadde da kayayyaki da kula da zaman rayuwar jama'a, a karshe dai ya kamata a bi tsarin daukar hakki da nuna yabo har da yanke hukunci ga wadanda ke da nauyin bisa wuyansu.
Shirin ko ta kwana ya kasa al'amuran da suka faru bisa matakai hudu, wato bala'in halitta da masifar hadari da annobar cuta mai yaduwa da abinci mai inganci da al'amuran tsaron kai a zamantakewar al'umma ciki har da farmakin ta'adanci.
Mr Mao Shoulong ya bayyana cewa, bayar da shirin ko ta kwana a dukan fannoni na da ma'anar musamman ga zamantakewar al'ummar kasar Sin,ana sa ran alheri ga gwamnatocin matakai daban daban da za su kara kyautata ayyukansu, kuma jama'a za su iya samun tabbaci wajen aiwatar da aikace-aikacensu da kwance zuciyarsu. Ya ce, wannan shirin ko ta kwana yana da ma'anar aiwatar da dokokin shari'a sosai . Idan al'amuran da ke faruwa cikin gaggawa, to gwamnati za ta iya daukar matakai kai tsaye cikin sauri sosai , sa'anan kuma, jama'a za su iya kwance zuciyarsu a lokacin faruwar al'amuran cikin gaggawa.
Mr Mao Shoulong ya kuma ci gaba da bayyana cewa, bayan da aka bayar da shirin ko ta kwana a duk fannoni, gwamnatin kasar Sin ta ba da tabbaci ga sassan da ke karkashinta wajen aiwatar da shirin, sa'anan kuma ya kamata jama'ar kasar Sin su kara karfinsu na magance al'amuran da suke faru ba zato ba tsammani. Ya bayyana cewa, majalisar gudanarwar kasar Sin da gwamnatocin wuri wuri ne kawai za su aiwatar da shirin nan, amma ba a tsari da kuduri ga jama'a da rukunonin zamantakewar al'umma da masu masana'antu da cewar wai ko za su yi wane irin abu ko bai kamata su yi ba.(Halima)
|