Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-11 15:36:50    
Sin da kasashen Afirka sun hada kansu don moriyar juna da samun bunkasuwa gaba daya

cri

A ran 10 ga wata, wani jami'in ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ke zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, har kullum hadin kan tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka ke bisa tushen moriyar juna da kuma samun bunkasuwa gaba daya. Kasar Sin ta kulla sabuwar dangantakar abonkantaka bisa manyan tsare-tsare domin raya tattalin arziki da gina kasa tare da jama'ar kasashen Afirka.

Kuma wani jami'in sashen kula da harkokin yammacin Asiya da arewacin Afirka na ma'aikatar cinikayya ta Sin ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afirka sun kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare ne bisa tushen daidai wa daida da fahimtar juna da hadin kai da moriyar juna, har kullum kasar Sin ta kan hada gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da kasashen Afirka bisa ka'idar daidai wa daida da moriyar juna da hada kai daga fannoni daban daban da mai da hankali kan amfani da kuma samun bunkasuwa gaba daya.

A cikin wannan mako, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing zai kai wa kasashen Afirka shida ziyara, ta haka za a ci gaba da bin al'adar ziyarar Afirka da ministocin harkokin waje na kasar Sin su kan yi a cikin ko wane farkon shekara.

He Wenping, shugabar sashen nazarin yammacin Asiya da Afirka na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin kwanakin nan, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun yi shela cewa, wai kasar Sin tana aiwatar da manufar sabuwar mulkin mallaka ga kasashen Afirka. Kuma ta ce, har kullum kasar Sin tana nanata samun bunkasuwa tare da kasashen Afirka, ba kamar kasashen yamma suke yi kan kwace albarkatun kasa na Afirka cikin dogon lokaci ba. Alal misali, sabo da kwacewar albarkatun kasa da kasashen yamma ke yi cikin shekaru da yawa a jere, ya zuwa yanzu kasar Nijeriya wadda babbar kasa ce wajen samar da man fetur ba ta da ko wane irin kayayyakin tace mai. Amma kasar Sin ta kafa manyan kamfanoni da yawa a kasashen Afirka domin samar da fasahohi da kudaden da kasashen Afirka ke bukata cikin gaggawa.

Bisa kididdigar da hukumar kwastan ta kasar Sin ta bayar, an ce, a cikin wadannan shekaru 5 da suka gabata, yawan kudin cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya kara daga dala biliyan 10 zuwa fiye da dala biliyan 37 a cikin ko wace shekara. Kuma a cikin shekarun nan da suka wuce, kasashen Afirka sun samu gibin ciniki tsakaninsu da kasar Sin, ta yadda kasashen Afirka suka samu kudade masu yawa daga kasashen waje.

Haka kuma domin shigo da kayayyakin Afirka cikin kasuwar kasar Sin da sauki, tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekara ta 2005, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar soke harajin kwastan kan kayayyaki na iri 190 da ake shigo da su daga kasashen Afrika 28 mafiya talauci. Kuma a cikin shekarar bara, jimlar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga wadannan kasashen Afirka da suka samu alheri ta ninka sau daya.

Ban da wannan kuma kamfanonin Sin sun kara zuba jari ga kasashen Afirka. Daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar bara kawai, yawan kudin da kamfanonin Sin suka zuba a kasashe daban daban na Afirka ya kai dala miliyan 175, wanda ya kai kashi 10 cikin kashi dari na jimlar kudin da Sin zuba a Afirka gaba daya.

Ya zuwa yanzu, mutanen Sin suna so su biya kudi da kansu don je kasashe 16 na Afirka yawon shakatawa, kuma yawan mutanen da suka je Afirka yana ta karuwa, ta haka an samar da zarafofi masu kyau kan tattalin arziki ga kasashen Afirka.

A cikin watan Satumba na shekarar da ta gabata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar da muhimman matakai 5 kan raya dagantakar da ke tsakanin Sin da kasashe masu tasowa, wadanda suka kunshe da soke bashin da kasashe mafi talauci ke ci, ta haka kasashen Afirka suka samu alheri sosai.(Kande Gao)