Ran 9 ga wata, a karo na farko ne kasar Sin ta shirya taron kasar kan kimiyya da fasaha a nan birnin Beijing tun bayan da aka shiga sabon karni. Bisa labarin da wakilin gidan Rediyo kasar Sin ya samu daga wajen taron nan, an ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta dora muhimmanci wajen gudanar da aikin nazarin kimiyya don neman bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, kuma ta sami manyan sakamako masu yawa. Nan gaba kuma kasar Sin za ta kara daga matsayin zaman rayuwar jama'a ta hanyar sabunta fasaha da kimiyya.
Bayan da aka shiga lokacin kaka na shekarar bara, annobar murar tsuntsaye ta taba bullawa a larduna da jihohi guda 9 na kasar Sin, amma ba ta bulla a Qianshan, wani babban wurin kiwon tsuntsayen gida da ke a karkarar birnin Anshan na lardin Liaoning a arewa maso gabashin kasar Sin. Malam Huang Mingxin wanda ke aiki a cibiyar shawo kan cututtukan dabbobi ta wurin ya bayyana cewa, "yawan kaji da ake kiwo a wurinmu mai suna Qianshan ya kai kimanin miliyan 6, amma mun ci gajiyar allurar rigakafi sosai wajen shawo kan cutar murar tsuntsaye, don haka cutar nan ba ta taba bullawa a wurinmu ba har cikin shekarun nan uku da suka wuce."
Ya zuwa yanzu, an riga an yi amfani da irin wannan allurar rigakafin murar tsuntsaye da yawansu ya kai biliyan 1 a kasar Sin. Sa'an nan kuma duk tsuntsayen gida da aka yi musu irin wannan allurar rigakafi ko daya ma bai taba kamu da cutar murar tsuntsaye ba. Sabo da haka an ba da lambar kasa mafiya girma ta ci gaban kimiyya da fasaha ga wadanda suka gano irin wannan allurar rigakafi. Yanzu, an riga an fitar da irin wannan allurar rigakafi mai inganci zuwa kasar Vietnam da Malasiya da kuma sauran kasashe. Alal misali, yawan irin wannan allurar rigakafi da aka yi amfani da su ya wuce miliyan 300 a kasar Veitnam, haka nan kuma kasar Vietnam ta yi odar allurar rigakafin nan da yawansu ya kai miliyan 500 daga kasar Sin a wannan shekarar.
A gun wannan taron duk kasar Sin kan kimiyya da fasaha da aka yi a yau, wata sabuwar hanya da ake bi wajen ban ruwa ta jawo hankulan mutane sosai. Matsakaicin ruwa da ko wane mutum na kasar Sin ke da shi bai kai rubu'i na duniya ba. Kasar Sin tana bukatar ruwa mai tarin yawa wajen shayad da gonaki, a cikin irin wannan hali ne kasar Sin ta yi ta yin kokari sosai wajen neman samun sabuwar hanya da za a bi wajen shayad da gonaki domin tsimin ruwa. Shehun malami Lu Bingheng na Jami'ar koyon aikin zirga-zirga ta birnin Xi'an ya gano sabuwar hanya da ake iya bi wajen shayar da gonaki domin tsimin ruwa sosai. Don haka ya sami lambar kasa ta kirkire-kirkire.
Malam Zhao Li xin, mataimakin shugaban cibiyar nazarin labarun kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya nuna cewa, "jama'a suna cin gajiyar kimiyya da fasaha wajen zaman rayuwarsu. Daga zaman rayuwar jama'a na kasar Sin a fannin sutura da abinci da gidajen kwana da kuma tafiye-tafiye, musamman ma daga aikin gona da na kare muhalli ma, za a iya gano sakamako da aka samu a fannin kimiyya da fasaha."
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi a gun taron duk kasar kan kimiyya da fasaha da aka yi a yau cewa, "ya kamata, a nace ga bin manufar nazarin kimiyya da fasaha domin neman bunkasuwar tattalin arzikin da zamantakewar al'umma da kuma bauta wa jama'a. A gudanar aikin sabunta kimiyya da fasaha domin daga matsayin zaman rayuwar jama'a, sa'an nan kuma a kara koshin lafiyar jikunan jama'a yayin da ake neman daga matsayin ilmin jama'a a fannin kimiyya da al'adu, ta yadda jama'a su ci gajiyar sakamako da ake samu wajen sabunta kimiyya da fasaha." (Halilu)
|