Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-09 18:33:29    
Yawan kudaden da kasashen Sin da Afirka suka samu daga ciniki ya zarce dalar Amurka biliyan 30

cri
Bisa kididdigar da kwastan na kasar Sin ya bayar, an ce, yawan kudaden da kasashen Sin da Afirka suka samu daga ciniki tun da watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar 2005 ya kai dalar Amurka biliyan 32.17, wanda ya riga ya zarce jimlar kudaden da suka samu a cikin duk shekarar 2004.

Masana sun kiyasta cewa, jimlar kudaden da kasashen Sin da Afirka suka samu daga ciniki a cikin duk shekarar 2005 za ta zarce dalar Amurka biliyan 37, amma a cikin shekarar 2004 kuma wannan jimla ba ta kai biliyan 30 ba. Yawan kudaden da kasashen Sin da Afirka suka samu daga ciniki tun da watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar da ta gabata ya karu da kashi 39.1 bisa dari.

Wani jami'in kwastan na kasar Sin ya bayyana cewa, tun da aka yi taron dandalin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka a shekarar 2000 har zuwa yanzu, kasashen Sin da Afirka sun bude wani sabon shafi a fannin yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki cikin sauri kuma lami lafiya daga fannoni daban daban. Ba ma kawai yawan kudaden da suka samu daga ciniki ya ninka fiye da sau 2 a cikin shekaru 5 da suka gabata ba, har ma sun rika kyautata tsarin ciniki.

A cikin shekarun nan da suka wuce, kayayyakin da kasar Sin ta sayo daga kasashen Afirka sun fi wadanda ta sayar da su zuwa kasashen Afirka yawa, haka kuma karuwar yawan kayayyakin shigi ta fi ta yawan kayayyakin fici. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta rika kyautata tsarin sayar da kayayyaki zuwa kasashen Afirka, yawan injuna da kayayykin fasahar zamani ya kusan mamaye rabin jimlar dukan kayayyakin da kasar Sin ta sayar da su zuwa kasashen Afirka, wanda kuma yake ta karuwa cikin sauri.

Wannan jami'i ya kara da cewa, a cikin shekarar 2005 da ta gabata, kasashen Afirka sun tafiyar da harkokin siyasa lami lafiya, kuma sun gaggauta raya tattalin arzikinsu, sun kara mai da hankali kan yin mu'amala da kasar Sin wajen tattalin arziki da ciniki. Manyan jami'an kasashen Sin da Afirka sun ci gaba da yin mu'amala sosai, sun yi ta kai wa juna ziyara, wannan ya nuna cewa, shugabannin bangarorin nan 2 suna son kara karfin yin hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu, ta haka an ingiza bunkasuwar hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da ciniki.

Tun da ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2005, gwamnatin kasar Sin ta soke harajin kwastan na kayayyaki iri 190 da kasashen Afirka guda 28 mafi fama da talauci suka sayar da su zuwa kasar Sin, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, ta yadda yawan kayayyakin da kasashen Afirka suka sayar zuwa kasar Sin ya ninka har fiye da sau daya.

Sa'an nan kuma, gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi kan masana'antun kasar da su zuba jari da kuma kafa kamfannoninsu a kasashen Afirka. Kasashen Sin da Afirka sun rika habaka yin hadin gwiwar kasuwanci a fannoni daban daban. Fannonin da kasar Sin ta zuba jari a kai suna kunshe da ciniki da samar da albarkatun kasa da harkokin jigila da aikin noma da samar da amfanin gona da dai sauransu.

Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, tun da watan Janairu har zuwa watan Oktoba na shekarar 2005, masana'antun kasar Sin ta riga ta zuba jarin da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 175. Kuma ya zuwa waan Oktoba na shekarar 2005 yawan kudin da kasar Sin ta zuba cikin Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 75 gaba daya. Kasar Sin da kasashen Afirka 28 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar moriyar juna da ba da tabbaci wajen zuba jari, ta kuma sa hannu kan yarjejeniyar magance dora haraji sau biyu da wasu 8.

Taron dandalin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Aifirka ya zama wani muhimmin taro ne da bangarorin nan 2 suka kara yin tuntubar juna da hadin gwiwa. A cikin shekarar 2005 da ta gabata, bangarorin nan 2 sun ci gaba da aiwatar da matakai a jere don habaka hadin gwiwar moriyar juna, bisa tsare-tsaren taron dandalin nan.

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi bayani cewa, taimakon da kasar Sin ta ba kasashen Afirka muhimmin kashi ne da ke cikin hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin nan 2. Tare da karuwar karfin tattalin arziki na kasar Sin, za ta kara ba da taimako gare su. Ta kuma horar da ma'aikata na fasahohi iri daban daban. Kasashen Sin da Afirka za su kara bunkasa hadin gwiwar kasuwanci da ke tsakaninsu a cikin shekarar da muke ciki.(Tasallah)