 Shekarar 2005 da ta wuce, shekara ce da ke cike da bala'un halitta ciki har da ambaliyar ruwa da guguwa da fari da girgizar kasa, yawan hasarar tattalin arzikin da aka haddasa sabo da bala'u a wannan shekara ya kai matsayin koli daga cikin shekaru 5 da suka gabata. Domin fuskantar wadannan bala'u, wadanne irin matakai ne gwamnatin kasar Sin ta dauka? Kuma yaya sassa daban-daban na zaman al'ummar kasar Sin suka taimaki jama'a masu shan bala'I domin farfado da zaman rayuwarsu? To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayani a kan wannan labari.
Cikin watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, an yi girgizar kasa mai tsanani a birnin Ruichang na lardin Jiangxi da ke kudancin kasar Sin. Da girgizar kasa ta auku sai nan da nan gwamnatin wurin ta buga wayar sulula don sanar da jama'ar birnin wannan labari. Mr. Lu Xuebing, dan birnin Ruichang ya gayawa wakilinmu cewa,
"Aukuwar girgizar kasar ke da wuya, sai na samu wani sakon salula cewa, kada a zauna cikin dakunan da suka lalace. Kuma mun dauki matakan yin rigakafi a daidai lokaci, sabo da haka ba mu sami babbar hasara ba. Mutane da yawa su ma sun sami sakonni irin haka. Wannan sako yana da kyau kuma an buga shi a daidai lokaci."
Kafa tsarin yin rigakafin bala'u da ba da labari tun kafin aukuwarsu ya zama wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka domin magance bala'un halitta. Sakamakon kafa wannan tsari ya sa wurare daban-daban na kasar Sin za su iya ba da labarun bala'I tun da wuri, ta yadda jama'a za su iya yin tsira daga bala'in, kuma gwamnati da zaman al'umma za su iya kama gaba wajen aikin ceto daga bala'i.
Ban da wannan kuma, domin fuskantar bala'un halitta, kasar Sin kuma ta dauki wasu matakai daban, a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 5 ga wata, Mr. Li Liguo, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a ya bayyana cewa,
"Kasar Sin ta kyautata tsarin ba da labaru da yin ceto tun kafin aukuwar bala'I, da zarar bala'I ya auku sai a iya yin aikin ceto daga bala'in bisa abubuwan da aka tanada cikin tsari kuma cikin gaggawa."
Bisa kididdigar da aka yi an ce, a shekarar 2005, yawan dakunan da suka rushe a kasar Sin sabo da bala'un halitta ya kai fiye da miliyan 2.2, yawan mutane masu shan bala'I da aka kaurar da su cikin gaggawa ya kai fiye da miliyan 15, yawan hasarar tattalin arziki da aka samu sabo da bala'u ya kai na darajar kudin Renminbi na kasar Sin wato fiye da Yuan biliyan 204. Domin taimaka wa jama'a masu shan bala'I, kasar Sin ta yi jigilar tantuna da yawansu ya kai kusan dubu 67 zuwa wuraren da suka gamu da bala'u, sai gwamnatin tsakiya kawai ma ta ware kudun Renminbi biliyan 8.7 domin yin ceto da kau da bala'u.
A lokacin da gwamnatin kasar Sin take yin aikin ceto daga bala'in, sassa daban-daban na zaman al'ummar kasar su ma sun yi ta ba da taimako ga jama'a masu shan bala'in. Kafin rabin wata da ya wuce a nan birnin Beijing, an yi wani babban tashe na ba da taimakon kudi da kayayyaki ga mutane masu shan bala'a da na masu shan wahala cikin zaman rayuwarsu. A wata tashar ba da gudummuwa ta ofishin unguwar Laoshan ta jihar Shijingshan ta birnin Beijing, wakilinmu ya samu labari daga wajen madam Zhang Jianjun wadda ta zo tashar don ba da gudunmmuwa, ta ce,
"Na ba da wani bargo da wasu tufaffi masu gashin tsuntsaye, wasunsu kuma sababbi ne, ban taba sawa ba, na yi haka ne domin ba da taimako ga jama'a da ke wurare masu talauci." (Umaru)
|