 A ran 1 ga wata, an bude gizagizan internet na gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gaske, da bude wannan tashar internet waddda adireshinta shi ne www. gov. cn, sai nan da nan ta jawo hankulan sassa daban-daban na zaman al'umma sosai.
Mr. Duan Guohua, jami'in cibiyar harkokin kayayyakin lantarki ta ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, muhimmin dalilin da ya sa wannan tashar internet ta gwamnatin kasar Sin ta jawo hankulan mutane shi ne sabo da tashar ta zama dandalin gwamnatin kasar Sin domin bayar da labaru masu kwarjini kuma daga duk fannoni, ya ce, "Bisa matsayinta na wata tashar internet ta kofar gwamnatin kasar Sin, wannan tashar ta zama wata hanya ce da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke bi wajen ba da labaru kan harkokinta na siyasa nata, kuma wani dandali ne na sassa daban-daban na gwamnatin kasar ciki har da kananan hukumomin gwamnati na wurare daban- daban don su aiwatar da harkokin siyasa a fili da yin hidima ga jama'a da zaman al'umma ta hanyar gizagizan internet na kasashen duniya."
Mr. Duan ya ce, a da akan samun labaru game da harkokin siyasa na gwamnatin kasar Sin ta hanyar tashoshin internet na ma'aikatu daban-daban na gwamnatin kasar, ko kuma na kananan hukumomin kasar, sabo da tashoshin internet suna da yawan gaske, shi ya sa da kyar ake iya samun wadannan labaru. Amma yanzu an bude hadaddiyar tashar internet ta gwamnatin kasar, sai a kawo sauki ga jama'a da su samu labarun kasar Sin.

A yayin da Mr. Stepen Belter wanda ya zo daga Amurka ya amsa tambayar da wakilinmu ya yi masa ya ce, "Wannan tashar internet ta gabatar da labarun gwamnatin kasar Sin. Hanyoyin da ake bi wajen daidaita matsaloli daban-daban, dukansu ana iya samun su a kan wannan tashar. Har ma abubuwa game da yadda za a share wuri a zauna, yaya za a yi don yin aure da Sinawa."
Bisa labarin da aka bayar an ce, nan gaba idan baki suna son zuwan kasar Sin don yin ciniki ko yawon shakatawa, wadanne irin abubuwan za su yi, dukkansu ana iya samun labarun da abin ya shafa cikin shafuffukan Turanci na wannan tashar internet.
Wani dalili daban da ya sa wannan tashar internet ta gwamnatin kasar Sin ta jawo hankulan mutane shi ne sabo da tashar za ta sa kaimi ga raya harkokin siyasa na gwamnatin kasar Sin ta hanyar internet, wannan yana da amfani ga kafa wata gwamnati wadda take gudanar da harkokin kasa masu amfani kuma cikin da'a kuma a fali kuma bisa gaskiya.
Yayin da Mr. Wang Yukai, farfesa na kolejin koyon harkokin siyasa na kasar Sin yake amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa ya ce, "Bayan da aka bude wannan tashar internet ta gwamnatin kasar Sin, mai yiwuwa ne za ta iya kafa wata gwamnati wadda ke tafiyar da harkokinta a fili, jama'a za su iya samun tarin labaru ta hanyar wannan tashar, bayan haka kuma za su iya yin mu'amala a tsakaninsu da gwamnatin kasar, sabo da haka an bude wata muhimmiyar hanya ga jama'a don su shiga harkokin gwamnati, da da ba da ra'ayoyinsu domin tsai da manufofin kasar."
Ban da wannan kuma, bude hadaddiyar tashar internet ta gwamnatin kasar Sin ta kawo amfani daga fannoni da yawa ga ayyuka da zaman rayuwar jama'a na kasar. (Umaru)
|