 Shekarar 2005 da ta wuce ba da dadewa ba, shekara ce da ba a taba ganinta tamkar yadda sauran shekarun da suka wuce wajen huldar da ke tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan. Tun daga farkon shekarar 2005, kusan a kowane wata, an iya samun manyan al'amaran ciyar da huldar da ke tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan gaba, daga cikinsu, da akwai al'amarin zartas da dokar hana kawo baraka ga kasa da ziyarar da tsohon shugaban jam'iyyar Kuomintang Lien Chan ya yi a babban yankin kasar Sin da dai sauran al'amuran da ke da zurfafiyar mana'a a tarihi, ciki har da 'yan kasuwa na Taiwan sun komawa gidajensu ta hanyar yin kwangilar jiragen sama a bikin gargajiyar kasar Sin na yanayin bazara, da soke harajin kwasatan ga shigar da 'ya'yan itatuwa na Taiwan cikin babban yankin kasar Sin da sauran manyan al'amuran musayar zaman rayuwar alaka ta jini a tsakanin jama'ar bangarorin biyu.
An soma shekarar 2005 da ba a taba ganin irinta ba wajen huldar da ke tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan daga somawar zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan ta hanyar yin kwangilar jiragen sama a bikin yanayin bazara. A farkon shekarar 2005, cikin himma da kwazo ne babban yankin kasar Sin ta sa kaimi ga 'yan kasuwa na Taiwan da su yi kwangilar zirga-zirgar jiragen sama, bisa sanadiyar nan ne, karo na farko ne jiragen sama masu daukar fashinjoji na bangarorin biyu sun yi wa juna zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye wanda aka riga aka dakatar da zirgar nan har cikin shekaru 56 ba tare da yin zango a wuri na uku ba.

Amma a gaskiya dai, huldar da ke tsakanin bangarorin biyu ta taba shiga cikin hali mai zafi sosai, Mr Xu Shiquan, mataimakin shugaban kungiyar yin nazari kan Taiwan ta kasar Sin yana ganin cewa, sauyawar nan da aka samu musamman domin babban yankin kasar Sin ya bayar da wata manufa mai yakini kuma mai sassauci ta hanyar hakikanin abubuwan da aka yi, ya bayyana cewa, a kan batun sa kaimi ga babban sha'anin dinkuwar mahaifar kasar Sin, muna yin hakuri sosai, manufar nan ta bayyana cewa, ko shakka babu ba za mu yi kome a fannoni hudu wanda shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar, wannan shi ne babban dalilin da ya sa aka samu sabon hali wajen huldar da ke tsakanin bangarorin biyu.
Game da batun da aka cewar "Ko shakka babu ba za mu yi kome a fannoni hudu" shi ne babban abin da ke cikin ra'ayoyi hudu da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar a watan Maris na shekarar 2005 dangane da yadda za a raya huldar da ke tsakanin bangarorin biyu a karkashin sabon halin da ake ciki . Wannan ya bayyana tsayayyen matayi da sahihanci sosai da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatinta suka yi ga daidaita batun Taiwan, kuma ya bayyana halin nuna alakar jini a tsakanin bangarorin biyu da kaunar da juna, ya ba da babban tasiri ga yalwata huldar da ke tsakanin bangarorin biyu. Bayan da Mr Hu Jintao ya bayar da ra'ayoyi hudu ba da dadewa ba, hukumar koli ta kasar Sin ta zartas da dokar hana kawo baraka ga kasa bisa kuri'u masu rinjaye , dokar ta bayyana ra'ayin kullum da babban yankin kasar Sin ya dauka na yin matukar kokari don neman samun dinkuwar kasar Sin cikin lumana da kuma cikin sahihanci sosai , sa'anan kuma ya bayyana niyyar da jama'ar duk kasar Sin suka yi don nuna kiyewarsu ga kawo baraka ga kasa da kiyaye dinkuwar kasa, har da kawo tabbaci ga hana kawo baraka ga kasa wanda rukunin 'yan aware yake yi da dai sauransu. Ba hakan aka yi kawai ba, Mr Hu Jintao shi ma ya gayyaci jam'iyyun Taiwan da ke yin adawa da kawo baraka ga kasa da kuma daukar ra'ayin raya huldar da ke tsakanin bangarorin biyu da su kawo ziyara a babban yankin kasar Sin bisa sunan babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Ziyarce-ziyarce da aka yi sun sami sakamako sosai, jam'iyyu uku na Taiwan da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun sami ra'ayi daya a kan batun dinkuwar kasar Sin .
Jama'ar bangarorin biyu suna fatan huldar da ke tsakanin bangarorin biyu za ta sami sabuwar mafita a cikin sabuwar shekara.(Halima)
|