Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-04 08:51:18    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(29/12-04/01)

cri

A ran 1 ga wata na shekara ta 2006, 'yan wasa nakasassu fiye da 60 da suka zo daga kasashen Norway da Sweden da Mongolia da kuma Sin sun shiga gasar gudun kankara ta nakasassu ta shekara ta 2006 da birnin Changchun da ke jihar Jilin ta kasar Sin ya shirya. An fara yin gasar gudun kankara ta nakasassu a cikin shekara ta 1964 a kasar Norway, an shigar da ita zuwa kasar Sin a cikin shekara ta 2005, kuma ta zama wani kashi na sallar gudun kankara ta duniya ta birnin Changchun, gasar da aka yi a cikin shekarar da muke ciki gasa ta biyu ce da aka yi a kasar Sin. Haka kuma a cikin gasa ta wancan rana, jakadan Norway da ke kasar Sin Mr. Tor Christian Hildan ya je filin gasar don karfafa zuciyar 'yan wasa, kuma ya jagoranci dan wasa makaho na karshe da ya kammala yin gasar.

Har zuwa ran 31 ga watan Disamba ta shekara ta 2005, an riga an fara gina filaye da dakuna na wasannin Olympic na shekara ta 2008 guda 18 da ke cikin 31, wato an gina sabbin filaye da dakuna guda 11, kuma an gyara da kuma habaka filaye da dakuna guda 2, haka kuma an gina filaye da dakuna na wucin gadi guda 5. Ban da wannan kuma, an riga an fara gina dukkan gine-gine 5 da ke dangane da wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008. Kwamintin shirya wasanin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, an iya tabbatar da lafiya da ingani na dukkan ayyukan da aka fara gina su. Bisa shirin da aka tsara, za a kammala gina dukkan sabbin filaye da dakuna kafin karshen shekara ta 2007.

A ran 29 ga watan Disamba na shekara ta 2005, an rufe gasar nagartattun 'yan wasa ta badminton ta Copenhagen wadda gasa ce ta karshe ta hadaddiyar kungiyar badminton ta duniya a cikin shekara ta 2005. Dan wasa na kasar Sin Bao Chunlai ya lashe shahararren dan wasa na kasar Denmark Peter Gade bisa maki na biyu ba ko daya a cikin karon karshe na gasar da ke tsakanin namiji da namiji, kuma wannan karo ne na farko da ya zama zakara a cikin gasar. Haka kuma a cikin karon karshe na gasa a tsakanin maza biyu biyu, 'yan wasan kasar Sin Cai Yun da Fu Haifeng ba su ci 'yan wasan Amurka Tony Gunawan da Howard Bach ba bisa maki daya da biyu, shi ya sa sun samu lambar azurfa.

Bisa kididigar da babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin ta bayar, an ce, 'yan wasan kasasr Sin sun samu lambobin zinariya na duniya 106 gaba daya a cikin wasannin iri na 22 da ke cikin gasar fid da gwani ta duniya da kuma gasar cin kofin duniya da aka yi a shekara ta 2005, ciki har da wasanni iri na 10 da ke cikin wasannin Olympic na lokacin zafi. Ban da wannan kuma, 'yan wasan kasar Sin sun samu lambobin zinariya na duniya 63 a cikin wasannin katare iri na kasar Sin da kwale-kwale da darar chess ta kasar Sin da kuma bowling da dai sauran wasannin da ba na wasannin Olympic ba. Daga shekara ta 1949 zuwa watan Disamba na shekara ta 2005, 'yan wasan kasar Sin sun samu lambobin zinariya 1901 gaba daya a duk duniya.

Za a yi gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta 18 ta hadaddiyar kungiyar kwallon kafa ta duniya wato FIFA a cikin kasar Jamus daga watan Yuni zuwa Yuli na shekara ta 2006. a ran 31 ga watan Disamba, wato rana ta karshen shekara ta 2005, an shirya biki wanda aka mayar da kofin duniya a matsayin babban take domin taya murnar sabuwar shekara a kofar Brandenburg da ke cikin birnin Berlin, babban birnin kasar Jamus, 'yan birnin Berlin da kuma jakadun kasashe daban daban da ke cikin Jamus sun shiga bikin.(Kande Gao)