Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-03 19:27:22    
An yi yawon shakatawa a dutsen Mengding na kasar Sin

cri

Sinawa na da dogon tarihin sha ti, lardin Sichuan daya ne da ke cikin wuraren da suka dasa itatuwan ti a kasar Sin. Ti da aka yi a dutsen Meng ya fi samun suna daga cikinsu. An ce, a da da can, a kan bayar da tin dutsen kamar kyakkyawar kyauta ga iyalan sarautu daga zuriya zuwa zuriya har shekaru fiye da dubu daya.

Dutsen Mengding yana cikin gunduma ta Mingshan ta garin Ya'an na lardin Sichuan na kasar Sin. Mun tashi cikin mota daga garin Ya'an, bayan muka tafi kilomita 15, sai mun ga wani dutse mai launin kore, wannan shi ne dutsen Mengding, wanda ya yi suna sosai domin dasa itatuwan ti cikin shekaru fiye da dubu daya.

A cikin lambunan ti da ke kan dutsen, mun ga wasu manoma suna kokari suna aiki game da ti, suna rare wakar da ta zo daga zuriya zuwa zuriya.

A da, ana kiran dutsen Mengding da ya zama dutsen Meng, tun daga daular Tang mai wadata a karni 8 zuwa karshen daular mulkin gargajiya ta kasar Sin---daular Qing, a kan mayar da ti da aka dasa a dutsen Meng da ya zama kyakkyawar kyauta da aka bayar wa iyalan sarautu. Farar hula su kan ce haka, 'idan kana son shan ti, ya fi kyau ka sha ti na dutsen Meng tare da ruwan kogin Yangzi'. Wannan ya bayana cewa, mutanen zamanin da suna kaunar ti da aka dasa a dutsen Meng.

Amma ina dalilin da ya sa ti na dutsen Meng ya yi suna kamar haka? Yanayinsa ne ya yi haka. A kullum a kan yi karamin ruwan sama da tukukin hazo, wadannan sun kago wani muhali mai kyau ga itatuwan ti a kan dutsen. Game da asalin ti na dutsen Meng, wannan ya shafi sarkin ti na kasar Sin wato Wu Lizhen. Da aka tabo magna a kan haka, mazauniyar wurin Malama Feng Xia ta ji alfahari sosai, ta ce, 'Irin wannan ti yana da labari sosai. Kamar yadda muka sani cewa, a da can shinkafa ya zama kansa a duniya, ba a dasa shi ba, sai wani mutum mai suna Shennongshi ya fara dasa shi. Ti shi ma ya yi kamar haka. Shennongshi ya fara ganin ti da wuri wuri, amma sarkin ti na kasar Sin Wu Zhenli ya fara dasa itatuwan ti.'

Bisa bincike da aka yi, an ce, a shekaru 53 kafin bayyanuwar Annabi Isa(A.S), wani manomin da ke dasa magunguna da ake kiransa Wu Lizhen ya ga cewa, ti da ke zama kansa a kan dutsen Mengding ya iya zama magani, sai ya dasa itatuwan ti da yawansu ya kai 7 a kan dutsen Meng. Sai itatuwan suna ta girma cikin shekaru masu yawa har sun zama ti masu kyau.

Ya zuwa yau, ana kiyaye wani lambun ti, wanda aka bayar da labari cewa, wannan wuri ne da Wu Lizhen ya dasa itatuwan ti. A hagu na lambu, sai dakin da aka yi da duwatsu domin Wu Lizhen ya huta a ciki. Da duwatsu ne, an yi taga da rufi da kofar dakin, har ruwan sama ba su iya shiga cikin ba, amma hasken rana ke iya shigowa. Wannan ya bayana hikimar mutanen zamannin da na kasar Sin.

Bayan da muka tabo magana a kan ti cikin dogon lokaci, sai mu dandana shi. A dutsen Mengding, wurin shan ti da ya fi kyau shi ne gidan ibada na Tiangai. A ganin mutane, gidan idaba bayani ne na al'adun addinin Buddah, amma a cikin gidan ibada na Tiangai, an ajiye wasu shahararrun mutane game da al'adun ti na kasar Sin kamar sarkin ti Wu Lizhen da magajin garin Yazhou na daular Song ta arewa wato Lei Jianfu, wanda ya yi gyaran fasahar yin ti da Lu Yu, marubuci na farko a duniya da ya rubuta littattafai game da ti a daular Tang.

Malama Han Qiong da ke zama a wurin da ke dab da gundumar Mingshan ta kan hau dutsen Mengding, a lokacin, ta kan sha ti a dutsen, wannan abu mai dadi ne gare ta. Ta ce, 'Ti na dutsen Meng yana da dadin sha sosai, musamman irin na Huangya da Ganlu. Wurin yana da ti iri daban daban, wasu masu araha, wasu kuma masu tsada ne, ko tsofaffi da yara suna iya sha.'

Mutanen Sichuan suna san fasahar yadda ake kiyaye lafiyar jikinsu sosai, ti na dutsen Meng ya amfana wa lafiyar jiki sosai. Ban da wannan kuma, da kake sukuni, sai ka zo dutsen Meng ka sha ti, ka yi hira da manoman da ke dasa itatuwan ti, wannan shi ne zaba mai kyau da kake kashe Danladi)