
Jama'a masu karatu, a sabuwar shekara ta 2006, a madadin dukkan ma'aikatan rediyonmu, shugaban rediyonmu Mr.Wang Gengnian ya nuna kyakkyawar gaisuwa da fatan alheri ga dukkan masu sauraronmu. Yanzu za mu gabatar muku wannan jawabin nuna fatan alheri filla filla:
Jama'a masu karatunmu: a gabanin kusantowar sabuwar shekara ta 2006, a madadin dukkan ma'aikatan rediyonmu,kuma bisa sunana ni kai, daga nan birnin Beijing ne na yi muku babbar gaisuwa da nuna fatan alheri.
A shekara ta 2005 da ta shige, akwai babban sakamakon da muka samu, kuma mu yi hange nesa, a shekara ta 2006, ba shakka za mu iya kara samu babban sakamako.
A shekara ta 2005, kasar Sin ta sami bunkasuwar tattalin arziki, kuma zaman al'umma namu mai dorewa sosai, dukkan jama'ar kasar Sin sun yi kokarin aiki bisa dabarar kimiyya, har an sa jimlar kudin da kasar Sin ta samu daga aikin kawo albarka sun karu da kashi 9.4 cikin dari. Kuma akwai wani babban albishiri mai jawo hankulan mutanen duniya shi ne kasar Sin ta sami nasara wajen harba kumbo mai tafiye tafiye a sararin sama mai dauka mutane mai lamba" Shenzhou" shida. A wancan lokaci akwai masu sauraronmu da yawa da suka taya mana murna ga wannan nasarar da muka samu.
A shekara ta 2005, sha'anin aiki na rediyonmu ya sami babban ci gaba daga sassa daban daban. Kuma yawan masu sauraronmu suna nan suna kara yawa sosai, ta haka ne rediyonmu ya kara lokatan watsa labarunmu da kyautata fasalin shirye shiryenmu. Yanzu yawan lokatan da rediyonmu ke watsa labaru kai tsaye zuwa kasashen duniya sun kai sa'o'I l87, Bugu da kari kuma ire iren yarenmu sun kara yawa sosai. A shekara ta 2005 da ta shige, rediyonmu ya kafa giza-gizan sadarwa na internet don bayar da labarai. A da, rediyonmu ya watsa labaru ta hanyar rediyonmu kawai, amma yanzu ta hanyoyi daban daban , ban da rediyo kuma akwai rediyo mai hoto da giza ?gizan sadarwa na internet da jarida da mujalla har da sauransu.
Yanzu, kokarin da muka yi ya sami yabo daga dukkan masu sauraronmu wadanda suka nuna mana ban kula da goyon baya har cikin dogon lokaci. A shekara ta 2005, yawan wasikun da masu sauraronmu suka aiko mana sun kai wajen fiye da miliyan 2, wannan adadi ya kai matsayin koli na rediyonmu.
Robert Smith . mai sauraro na kasar Amurka ya himmantar da mu cewa , CRI wato Rediyon kasar Sin na yau , yana watsa labaru a ko'ina na duniya . Ko youshe ka iya saurara shirye-shiryensa . Muna sanin cewa , kowane ci gaban da CRI ya samu ba ya rabuwa da goyon bayanku da kularku , saboda masu sauraro harsashi ne na rayuwar sha'aninmu . Yau a madadin dukannin ma'aikatan CRI , na bayyana sahihiyar godiya ga dimbin masu sauraro na kasashe daban daban na duk duniya .
A nan kasar Sin akwai wata thohuwar waka wadda ake cewa , idan mun zama abokai , to, wurin dake nisa ya zama makwabta . Muna zaune a duniya daya tare kuma muna shan hasken rana daya . Ya kamata mu zama abokai kuma ya kamata mu yi zaman rayuwa cikin lumana . Kullum muna hakake cewa , zaman lafiya da yalwatuwa sun kai matsayin muhimmanci a duniyar yau . Evgeniy Fradkin , mai sauraro na kasar Rasha ya aiko mana wasika tare da wani hoto . A bayan hoton , Babansa ya rubuta cewa , yara , domin zaman lafiya . Haka ne , bari mu yi addu'a don zaman lafiya da jituwa . Muna fatan sabuwar shekara za ta kawo mana zaman lafiya da yalwatuwa da kuma ci gaba. (Ado da Hadiza)
|