Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-30 15:44:03    
Karfin injunan wuta ya wuce kilowatt miliyan 500 a kasar Sin

cri
Ran 29 ga wata, an bayyana a nan birnin Beijing cewa, karfin injunan wuta ya zarce kilowatt miliyan 500 a kasar Sin a halin yanzu. Ta haka a zahiri dai aka sassauta karancin wutar lantarki da ake fama da shi a cikin shekarun nan biyu da suka wuce.

Bisa saurin karuwar wutar lantarki da ake samu a yanzu, za a kawar da karancin wutar lantarki daga kasar Sin kwata-kwata a shekarar 2007. Malam Zhang Guobao, mataimakin shugaban hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin ya bayyana cewa, a sakamakon ci gaba da ake samu wajen kara samar da wutar lantarki mai tarin yawa, nan gaba za a fi yin kokari wajen kara kyautata tsarin ba da wutar lantarki, yayin da ake bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki a kasar Sin. Ya ce, "kasar Sin za ta dora matukar muhimmanci ga kyautata tsarin ba da wutar lantarki a kasar Sin. Yayin da ake mai da hankali sosai ga saurin bunkasuwar masana'antun ba da wutar lantarki, ya kamata, a bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki ta hanyar samun babbar fa'ida da tsimin makamashi da rashin gurbacewar muhalli da sauransu. Wato a yi kokari sosai wajen gina tashoshin ba da wutar lantarki wadanda ke aiki da karfin ruwa da makamashin nukiliya da kwal mai tsabta da hasken rana da karfin iska da kuma makamantansu."

A cikin shekarun nan biyu da suka wuce, kasar Sin ta gaggauta bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki don sassauta karancin wutar lantarki da ake fama da shi. Karfin sabbin injunan wuta da aka samu ya wuce kilowatt miliyan 60 a shekarar 2005 kawai.

Nan gaba kasar Sin za ta gaggauta kyautata tsarin ba da wutar lantarki don ba da tabbaci ga samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki. Yanzu, bisa shirin da ta yi, kasar Sin ta riga ta fara daina aiki da kananan sassan injunan wuta wadanda ke bukatar kwal mai yawa, kuma wadanda ke gurbacewar muhalli, sa'an nan kuma ta fara aiki da sassan injunan wuta masu aiki da kwal wadanda karfin ko wanensu ya wuce kilowatt dubu 300. Haka zalika an sami ci gaba da sauri wajen gina tashoshin ba da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa. Karfin injunan wuta masu aiki da karfin ruwa ya riga ya zarce kilowatt miliyan 100 a watan Satumba na shekarar 2004, wato ke nan ya kai matsayi na farko a duniya. Ta haka an yi amfani da albarkatun ruwaye na Kogin Yangtse da Rawayen Kogi da kuma sauran manyan koguna na kasar Sin sosai. Bugu da kari kuma an mai da hankali sosai ga yin amfani da hasken rana da karfin iska da makamatansu don ba da wutar lantarki. Karfin injunan wuta masu aiki da kwal ya ragu zuwa kashi 73.7 cikin dari bisa duk karfin injunan wuta na kasar Sin a karshen shekarar 2004.

Don kyautata tsarin ba da wutar lantarki, kasar Sin ta kara sanya ido ga ayyukan ba da wutar lantarki, ta kayyadde yawan sabbin masana'antun ba da wutar lantarki masu aiki da kwal da ake ginawa, sa'an nan kuma ya kara amincewa da kafa sabbin masana'antun ba da wutar lantarki masu aiki da karfin iska da makamashin nukiliya. Kamfanin zuba jari ga aikin ba da wutar lantarki na kasar Sin yana daya daga cikin manyan kamfanonin ba da wutar lantarki. Malam Wang Binghua, babban manajan wannan kamfanin ya bayyana cewa, "a karkashin babban sharadin kare muhalli, muna kokari sosai wajen bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa, mu kara yin amfani da sabon makamashi wajen ba da wutar lantarki, ta yadda za mu kara daga matsayin kamfaninsu na ba da wutar lantarki."

Bisa manufar da gwamnatin Sin ta tsara dangane da bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki, nan gaba kasar Sin za ta bunkasa masana'antun ba da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa da makamashin nukiliya da karfin iska da makamantasu bisa shiri da aka tsara. (Halilu)