Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-29 17:34:21    
Gwamnatin kasar Sin za ta kara saurin yin gyare gyare kan tsarin makamashi don nuna tabbaci ga lafiyar makamashi

cri

Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na ci gaban kasar Sin; bunkasuwar aikin kawo albarka ta shafe matsalar makamashi sosai da sosai, sabo da haka matsalar makamashi ta zama muhimmiyar matsala mai ma'anar dabarun yaki dake kasancewa cikin hakikanin zaman al'umma, har ta iya kawo tasiri ga saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin. Yanzu a lokacin da kasar Sin ta sami saurin bunkasuwar tattalin arziki, amma wata babbar matsalar makamashi ta riga ta kawo tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki da ci gaban zaman al'uma nata.Sabo da haka ne yaya za a daidaita matsalar makamashi ta jawo hankulan zaman al'umma na duk kasar Sin. A ran 27 ga watan nan da muke ciki, Mr.Zen peiyan mataimakin firayin minista na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara dauki matakai don kara saurin yin gyare gyare ga tsarin makamashi don nuna tabbaci ga lafiyar makamashi. Yanzu za mu gabatar da abubuwan da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana kan matsalar nan.

Da farko dai wannan mataimakin firayin minista ya bayyana tsanantaccen halin da ake ciki kan matsalar makamashi a yanzu. Inda ya ce, yanzu da wani lokaci mai zuwa, bukatun makamashi yana nan yana kara sauri sosai har ya kawo karfin matsi mai tsanani ga aikin samar da makamashi, domin karancin albarkatai ya hana bunkasuwar aikin haka makamashi sosai, Bugu da kari kuma fasahar hakan makamashi tana baya baya har ta kawo tasiri ga karuwar aikin samar da makamashi sosai.

Mr.Zen peiyan yana gani cewa, fasalin yanzu na mai da kwal kaman wani muhimmin makamashi bai amfanawa aikin kiyaye muhalli ba.Bugu da kari kuma aikin samar da makamashi na kasar Sin ya gamu da babban tasiri daga sauye sauyen kasuwannin makamashi na duniya. A kan haka ne tabbas ne kasar Sin za ta dauki matakai don nuna tabbaci ga aikin samar da makamashi. A karshe dai wannan mataimakin firayin minista ya bayyana hakikanin matakan da kasar Sin za ta dauka. Ya ce, kiyaye da nuna tabbaci ga lafiyar makamashi ya kamata a yi tsimin makamashi daga sassa daban daban, kuma don yin kokari ga aikin neman kara yawan makamashi sosai, kuma cikin hakikanin hali ne da kara karfin kiyaye aikin kawo albarka da dinga daga matsayin fasahar hakan makamashi da kara habaka hadin guiwar hakan makamashi tsakanin kasar Sin da kasashen waje, da kuma ingiza aikin gyare gyare ga tsarin makamashi sosai, Kuma da kara karfin gine ginen dokokin shari'a na kiyaye lafiyar makamashi.

Ban da haka kuma yin gyare gyare ga farashin makamashi shi ne daya daga cikin muhimman matakan da za dauka cikin yin gyare gyare ga tsarin makamashi na kasar Sin.Har yanzu dai gwamnati ce ta tsara farashin man fetur, kuma kasashen duniya sun sa lura sosai ga aikin kimiyya na kula da farashin makamaki da tsara farashi mai dacewa na kasar Sin. Wadansu kwararru suna gani cewa, gyare gyaren farashin makamshi na kasar Sin yana shafewa bunkasuwar makamashi na kasar Sin. Mr.Zen peiyan ya ce, kasar Sin za ta nuna himma ga ingiza aikin tsara farashin makamashi cikin zama mai dorewa da neman daidaita dangantakar dake tsakanin kasuwanni da bukatun jama'a da kyautata aikin yin fama da lalataccen muhalli.

Wannan mataimakin firayin minista ya kuma bayyana cewa, zuwa shekara ta 2020, kasar Sin za ta yi kokarin neman kara yin amfani da abubuwan da an riga an yi amfani da su a da. Mr.Zen ya kuma bayyana cewa, za a yi kokarin hana aukuwar hadarin ma'adinan hakan kwal sosai.(Dije)