Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 20:06:15    
Kasar Sin tana yin ayyukan sake farfadowa tare da jama'ar wuraren da ke fama da bala'in tsunami

cri

A ran 26 ga watan Disamba na shekarar 2004, an yi girgizar kasa da tsunami a tekun Indiya, bisa sanadiyar nan ne, mutane da yawansu ya kai dubu 200 ko fiye suka mutu , kuma mutanen da yawansu ya kai miliyan 2 sun shiga jerin wadanda suke fama da bala'in. A wancan lokaci, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun ba da taimako ga jama'ar wuraren da ke fama da bala'in don kawar da wahalolin da suke sha. Sa'anan kuma, kasar Sin ta yi alkawarin ba da taimako gare su wajen sake farfado da kasashensu. A cikin shekara daya da ta wuce har zuwa yanzu, kullum kasar Sin tana aiwatar da alkawarinta, tana yin ayyukan sake farfado da wadannan kasashe tare da jama'arsu.

A kasar Srilanka , tsunami ta rushe gidaje da yawansu ya kai dubu goma kwata kwata ko wasu sassansu. Yanzu, mutane kusan miliyan sun rasa gidajensu. Gina gidajen kwana domin jama'ar da ke fama da bala'in a kasar Srilanka shi ne aiki mai muhimmanci wajen sake farfado da kasar bayan bala'in. Yanzu, daya daga cikin ayyukan gina gidajen kwana domin jama'ar da ke fama da bala'in ta hanyar yin amfani da kudadden da jama'ar kasar Sin suka samar  kyauta wato kauyen farko na sada zumuncin da ke tsakanin kasar Sin da kasar Srilanka an  riga an  kammala matakin farko na aikin, jami'in farko na zartaswa na hukumar kula da aikin sake gina gidajen da tsunami ya rushe Gemunu Alawattegama ya tabbatar da aikin da bangaren kasar Sin ya yi . Ya bayyana cewa, wadanda ke samar da kyaututuka na kasar Sin sun soma shirin gina kauyukan sada zumunci ta hanyar hakikanin kokarinsu, sun yi aikin da saurin gaske. Gidajen da suka gina na da kyaun gani sosai, ana jin dadin kwana a ciki, mun riga mun mayar da kauyen farko na sada zumunci da ke birnin Galle don ya zama misalin aikin, kuma mun nemi sauran wurare da dole ne za su gina gidajen kwana masu dorewa kamar yadda kauyen nan ya ke, wannan ya ba da himma da kwazo ga ayyukan da za a yi.

Kauyen farko na sada zumunci tsakanin kasar Sin da Srilanka yana gabashin birnin Galle da ke nesa da birnin Klumpuer da kilomita 120 ko fiye. A gaban babbar kofar bakin kauyen, an rubuta kalmomin da harshen Sinanci da na Ingilish da na Senggaro da cewa, "Kauyen farko na sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Srilanka", a bayanta kuma, an rubuta cewa, "ba da taimakon juna da zuciya daya, kuma a sada zumunci daga zuri'a zuwa zuri'a.

Aikin su yana daya daga cikin manyan ayyukan kasar Srilanka, yawancin tashoshin kamun kifaye sun rushe sosai bisa sanadiyar tsunami. Yanzu, aikin da kasar Sin ta yi don ba da taimakon sake gina tashar ruwa ta kamun kifaye wadda ta lalace sosai yana tafiya da saurin gaske. Wani direba na kasar Srilanka ya gaya wa manema labaru cewa, aikin sake gina tashar, aiki ne da gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako ga gwamnatin kasar Srilanka, mutanen kasar Sin sun yi aikin da gaske sosai, a karshe dai, masunta na kasar Srilanka za su sami fa'ida a tashar, saboda haka masunta sun yi farin ciki sosai.

A cikin ayyukan da kasar Sin ta yi don ba da taimako ga kasar Thailand, bangaren Thailand ya nuna yabo sosai a kansu, don ba da taimako ga kasar Thailand wajen sake farfado da aikin yawon shakatawa, kasar Sin ta shirya mutanen da yawansu ya kai dubu 7 don zuwa yawon shakatawa a kasar Thailand, a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da shirya mutane da yawansu zai kai dubu goma don yin yawon shakatawa a kasar. Mataimakin firayim ministan kasar Suwat Liptapanlop ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Thailand da jama'arta sun nuna godiya sosai ga taimakon da bangaren kasar Sin ya samar musu ba tare da kowane sharadi ba. Ya bayyana cewa, har wa yau dai ina tunawa da cewa, mun sami taimakon agaji a fannoni da yawa daga wajen kasar Sin , tamkar kungiyoyin masu yin aiki bisa son kai da kayayyakin sadarwa da saukakkun gidajen kwana da sauran kayayyakin gine-gine.(Halima)