Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 15:52:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(22/12-28/12)

cri
Mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr. Liu Jingmin ya fayyace a ran 22 ga wata cewa, za a fara sayar da tikitoci na wasannin Olympic na Beijing tun daga farkon watanni 6 na shekarar 2007.

Wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayyana a nan birnin Beijing a ran 20 ga wata cewa, yanzu ana gudanar da ayyukan gina filayen wasa da manyan dakunan motsa jikin da za a yi amfani da su a cikin wasannin Olympic na Beijing lami lafiya. A cikin dukan wadannan filayen wasa da manyan dakunan motsa jiki guda 31 da ake ginawa a nan da kuma sauran gine-gine 5 da abin ya shafa, an riga an fara gina wasu 18 a yanzu. Ya kara da cewa, ana sa ido kan ingancin dukan filayen wasan da ake ginawa. Bisa shirye-shiryen da aka tsara, za a kammala gina dukan filayen wasa da dakunan motsa jiki kafin karshen shekarar 2007.

An bude gasar cin kofin Toyota ta karo ta 3 ta wasan kwallon tebur ta duniya a dakin motsa jiki na Aichi-ken da ke birnin Nagoya na kasar Japan a ran 25 ga wata, wadda gasar duniya ce ta karshe da aka yi a cikin shekarar da muke ciki. Bayan da aka yi takara mai tsanani da juna, 'yar wasan kasar Sin Zhang Yining ta lashe dukan yan wasa masu shiga gasar ta zama zakara cikin kungiyar mata, dan wasan kasar Korea ta Kudu Rye Seung-min kuma ya zama zakara na maza.

Sabuwar kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin da aka kafa ba da dadewa ba ta fara horo da aka shafi wata daya a birnin Guangzhou na kasar Sin a ran 20 ga wata. Makasudin horon kungiyar kasar Sin a wannan gami shi ne don share fage ga gasar da za a shirya bisa gayyata ta wasan kwallon kafa tsakanin mata na kasashe 4 a Guangzhou daga ran 18 zuwa ran 22 ga wata Janairu na shekara mai zuwa. Kungiyoyin kasashen Amurka da Norway da Faransa za su kuma shiga wannan gasa.

Ran 19 ga wata, dan wasan kwallon kafa na kungiyar kasar Brazil Ronaldinhoal ya zama nagartaccen dan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar 2005 na Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA. Manyan malaman wasa da shugabannin kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen duniya sun zabe shi ta hanyar kada kuri'a, a cikin shekarar da muke ciki Ronaldinhoal ya gwada gwanintarsa sosai, ya taimaki kulob na Barcelona da ya zama zakara cikin lokacin gasa tsakanin shekarar 2004 da ta 2005, sa'an nan kuma ya taimaki kungiyar kasar Brazil da ta ci kofin Confederations na kungiyar FIFA na shekarar 2005. Ya samu yawancin kuri'un da aka jefa a wannan gami saboda ayyukan da ya yi a wannan shekara.

An bude gasar tseren keke ta kewayen tekun kasar Sin ta kudu ta karo ta 10 a Hong Kong a ran 26 ga wata, wadda gasa ce da Hadaddiyar Kungiyar Keke ta Duniya ta amince da ita. Ana gudanar da wannan gasa a Hong Kong da Guangdong de kuma Macao a wannan shekara, tsawonta ya kai kusan kilomita 760 gaba daya. 'Yan wasa fiye da 140 na kungiyoyin tseren keke guda 14 daga nahiyoyi daban daban sun shiga wannan gasa. Za a kammala gasar nan a Macao a ran 2 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.(Tasallah)