Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-23 16:22:40    
Kasar Sin ta bayar da takardar bayanin gwamnati game da hanyar neman bunkasuwa cikin lumana da take bi

cri

Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 22 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da wata takardar bayanin gwmnati game da "Hanyar da kasar Sin ke bi wajen Neman Bunkasuwa cikin Lumana". A cikin takardar, an waiwayi hanyar neman bunkasuwa cikin lumana da kasar Sin ke bi bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin daga karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata domin wannan hanya tana dacewa da halin da kasar Sin ke ciki da halin zamani da ake ciki a duk duniya da gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen neman cigaban zaman al'ummar duk duniya. Wannan takarda ta nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsaya tsayin daka kan hanyar neman bunkasuwa cikin lumana domin yunkurin cimma burin neman bunkasuwa irin ta hadin guiwa cikin lumana da jituwa tare da kara bude kofa ga kasashen waje. Yanzu ga bayanin da wakilinmu ya rubuto mana filla filla.

Ma'anar hanyar neman bunkasuwa cikin lumana da kasar Sin ke bi ta bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a duk fadin duniya domin raya kanta, kuma tana fatan za ta iya ba da gudummawarta wajen tabbatar da zaman lafiya a duk duniya bayan ta samu bunkasuwa. Haka nan kuma, lokacin da take dogara da kanta wajen yunkurin yin gyare-gyare da kirkiro sabbin fasahohin zamani domin cimma burin samun bunkasuwa, za ta ci gaba da bin manufar bude kofa ga kasashen waje. Sannan kuma, za ta yi kokari wajen raya tattalin arzikin duniya bai daya. Sabo da haka, za ta iya cimma burin neman bunkasuwa da moriya tare da sauran kasashen duniya gaba daya. Bugu da kari kuma, za ta ci gaba da bin manufar yin hadin guiwa da sauran kasashen duniya domin neman bunkasuwa cikin lumana. A sakamakon haka, za ta iya yin kokari tare da sauran kasashen duniya wajen kafa wata duniyar da ke cike da jituwa da bunkasuwa tare har abada.

Da farko, wannan takarda ta yi nazari kan halin da ake ciki a nan kasar Sin da al'adu da tarihin kasar Sin kuma da makomar da kasashen duniya suke nuna, ta nuna cewa, hanyar neman bunkasuwa cikin lumana hanya ce da ta wajaba da kasar Sin ta zaba wajen gina zaman al'ummarta ta zamani. Ita kuma muhimmin zabe da alkawari ne da gwamnati da jama'ar kasar Sin suka yi. Bunkasuwar kasar Sin ba za ta yi wa sauran kasashen duniya da mutane kowace irin barazana ba, amma za ta bai wa sauran kasashen duniya damar kara neman bunkasuwa da babbar kasuwa.

A cikin wannan takarda, an nuna cewa, a cikin 'yan shekarun nan, bunkasar kasar Sin ta ciyar da zaman lafiya da bunkasuwar duk duniya gaba daya. Kasar Sin za ta raya sabbin masana'antu inda ke cike da kimiyya da fasahohin zamani, amma za su rage yin amfani da makamashin halittu kuma ba za su kazamtar da muhalli ba. Kasar Sin ta ci nasara sosai domin ta dinga bin manufar yin haihuwa bisa shiri. A karkashin kokarinta, an kuma cimma burin rage saurin karuwar yawan mutanen duk duniya. A sa'i daya, wannan takarda ta nuna cewa, ko da yake kasar Sin ta samu cigaban da ke jawo hankulan duniya sosai, amma har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma, kuma tana fuskantar babban nauyin neman bunkasuwa da aka dora mata.

Sannan kuma, wannan takarda ta jadadda cewa, kasar Sin za ta nemi bunkasuwa kan karfinta da bin manufofin yin gyare-gyare da kirkiro sabbin fasahohin zamani. Kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin neman bunkasuwa bisa ilmin kimiyya lokacin da take neman bunkasuwa da bude kofa ga sauran kasashen waje.

Daga karshe dai, wannan takarda ta jadadda cewa, ba ma kawai kasar Sin za ta bi hanyar neman bunkasuwa cikin lumana a yau ba, har ma za ta ci gaba da bin wannan hanya a nan gaba bayan ta zama wata babbar kasa mai karfi. Gwamnati da jama'ar kasar Sin ba za ta sauya niyyar bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana kwata kwata ba. Ko da kasar Sin kasa ce mai tasowa kuma mafi girma a duniya, jama'ar kasar Sin miliyan dubu 1 da dari 3 suna bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, ko shakka babu wannan za ta bayar da gudummawa sosai ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar dan Adam. (Sanusi Chen)