Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. Kasar Sin ta riga ta tabbatar da cewa rage yin amfani da makamashin halittu da kiyaye muhalli za su zama muhimman ma'aunonin kyautata tsarin sana'o'inta a nan gaba. A ran 21 ga wata, a gun wani taron manema labaru da aka yi a nan birnin Beijing, wani jami'i mai kula da harkokin tattalin arziki na kasar Sin ya bayyana cewa, lokacin da ake kyautata tsarin sana'o'in tattalin arziki a nan gaba, za a kawar da dukkan ayyukan da suke yi amfani da makamashin halittu da yawa kuma suke kazamtar da muhalli a kai a kai. Haka nan kuma za a nuna goyon baya ga sana'o'in da ba za su yi amfani da makamashin halittu da yawa ba, kuma ba za su kazamtar da muhalli ba. Burin da ake son cimma lokacin da ake kyautata sana'o'i iri iri shi ne neman bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin hali mai dorewa. Yanzu ga wani bayanin musamman filla filla.
Bisa fasalin sassa daban-dabam na sabon tsarin sana'o'i iri iri da kasar Sin ta bayar, an raba dukkan sana'o'i kashi-kashi uku, wato sana'o'in da za a sa kaimin neman bunkasuwa da sana'o'in da za a kayyade bunkasa su da sana'o'in da za a hana raya su. Mr. Liu Zhi, direktan hukumar tsara manufofin raya sana'o'i daban-dabam a kwamitin yin gyare-gyare da neman bunkasuwar kasar Sin ya ce, "Dukkan sana'o'in da za su ci makamashin halittu masu dimbin yawa kuma za su kazamtar da muhalli ba za su samun izinin kafuwa ba a nan gaba. Dukkan irin wadannan masana'antun da suke aiki yanzu, ba za a kara zuba jari a kansu ba, kuma za a dauki matakan kawar da su a cikin kayaddaden lokaci. Idan ba za a kawar da irin wadannan masana'antu cikin lokacin da aka tsara ba, za a rufe su kwata kwata."
Bisa ma'aunonin rage yin amfani da makamashin halittu da kiyaye muhallin da ake ciki, kasar Sin za ta kyautata sana'ar sarrafa bakin karfe da sana'ar kera aluminium a Turanceda sana'ar kera motoci domin suna kazamtar da muhalli kuma yawan wadannan kayayyakin da ake samarwa ya wuce bukatun da ake nema kasuwa. Mr. Liu ya kara da cewa, "Za a kayyade a kara yawan kayayyakin da suke kera amma ba bisa bukatun da ake nema a kasuwa ba. Burin da ya fi muhimmanci kuma za a cimma shi ne kawar da injunan ja da baya. Sannan kuma, za a kara yin gyare-gyare kan fasahohin masana'antu da kara saurin yin kwaskwarima kan wasu sana'o'i."
Hakazalika, an bayyana cewa, lokacin da ake kawar da sana'o'i masu yin amfani da makamashin halittu da yawa kuma masu kazamtar da muhalli, za a sa kaimi wajen kafa masana'antun da za su yi amfani da fasahohin zamanin yanzu kuma ba za su kazamtar da muhalli ba domin tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri. Alal misali, za a sa kaimi wajen yin amfani da tsinken amfanin gona da kafa masana'antun yin amfani da karfin iska domin samar da wutar lantarki kuma da kara sarrafawa kashin makera da masana'antu su kan bata a banza gaba daya.
Kamfanin zuba jari a kan ayyukan da ba za a yi amfani da makamashin halittu da yawa ba na kasar Sin kamfanin kasa kadai ne a nan kasar Sin da ke zuba jari a kan sana'o'in kiyaye muhalli da rage yawan makamashin halittu da za a yi amfani da su. Mr. Zou Guijin, wanda ke kula da harkokin zuba jari a cikin kamfanin nan ya ce,
"Kan yadda za mu yi amfani da karfin iska domin samar da wutar lantarki, yanzu muna gina wata masana'antar yin amfani da karfin iska da ke da wani injin samar da wutar lantarki mai kilowatts dubu 30 a jihar Xingjiang mai cin gashin kanta. A sa'i daya, muna gina wata masana'anta daban da ke da inji mai kilowatts dubu 45 a lardin Hebei. Bisa shirin da muka tsara, ya zuwa shekara ta 2007, yawan kilowatts na injunan samar da wutar lantarki ta karfin iska zai kai kilowatts daga dubu dari 5 zuwa dubu dari 8. Sannan kuma, muna kafa ayyukan yin amfani da tsinken amfanin gona domin samar da wutar lantarki. Idan an yi amfani da wannan hanya, ba ma kawai za a iya kara wa manoma yawan kudin shiga ba, har ma za a iya kiyaye muhalli domin manoma ba za su kone tsinken amfanin gona a cikin gonaki ba."
Amma, lokacin da ake kawar da sana'o'i masu kazamtar da muhalli kuma masu yin amfani da fasahohin ja da baya, mutane da yawa za su rasa aikin yi. Sabo da haka, tun daga yanzu, an fara koyar da ilmi ga mutane wadanda suke aiki a cikin irin wadannan sana'o'i iri iri domin za su iya samun aikin yi a nan gaba. (Sanusi Chen)
|