Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-21 16:30:50    
Kasar Sin ta gyara adadin GDP na shekara ta 2004

cri

A ran 20 ga wata hukumar yin kididdiga ta kasar Sin ta shelanta cewa ta riga ta gyara adadin GDP na shekara ta 2004. Bayan an yi wannan gyara, jimlar GDP ta kasar Sin ta shekara ta 2004 ta samu karuwa, wato ya karu da kashi 16.8 cikin kashi dari. A sa'i daya, ta gyara adadin karuwar kudaden da aka yi a masana'antu da sana'o'in ba da hidima a cikin jimlar GDP ta shekara ta 2004. Sabon adadin da aka yi ya bayyana cewa, ba ma kawai duk yawan tattalin arzikin kasar Sin ya samu karuwa ba, har ma ana ganin cewa tsarin tattalin arzikinta yana cikin hali mai kyau. Yanzu ga wani bayanin musamman a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari.

Dalilin da ya sa kasar Sin ta gyara jimlar GDP ta shekara ta 2004 shi ne a 'yan kwanakin nan da suka wuce ta kammala aikin binciken tattalin arzikinta. Sabuwar kididdiga ta bayyana cewa, a shekara ta 2004, jimlar GDP ta kasar Sin ta kai kudin Renminbi yuan biliyan dubu 15 da dari 9 da tamanin da 7 da wani abu, wato ya karu da kudin Renminbi yuan biliyan 2300 bisa adadin da aka kidaya a karshen shekarar bara. Sakamakon haka, yanzu jimlar GDP ta kasar Sin ta riga ta haura ta kasar Italiya, kuma ta kai matsayi na 6 daga cikin kasashe wadanda jimlolin GDP nasu suna gaba a duk duniya duniya. Amma sabuwar kididdiga ta kuma bayyana cewa, har yanzu matsakaicin yawan GDP na kowane Basine yana baya, bai kai matsayi na 100 a duk duniya ba.

Mr. Li Deshui, shugaban hukumar yin kididdiga ta kasar Sin ya ce, sana'o'in da aka shafi lokacin da aka yi aikin binciken tattalin arzikin kasar Sin sun kunshi wasu sabbin sana'o'in ba da hidima. Sabo da haka, sabuwar kididdiga ta fi dacewa da halin da kasar Sin ke ciki. Tana kuma bayyana cewa, tsarin karuwar tattalin arzikin kasar Sin yana cikin hali mai kyau kuma tana da lafiya.

"A 'yan kwanakin nan da suka wuce, wasu mutane sun ce, kasar Sin tana dogara a kan masana'antun sarrafawa kawai domin neman cigaban tattalin arziki. Wasu mutane sun kuma fadi cewa, kasar Sin tana samun cigaban tattalin arziki ne domin fitar da kayayyakinta masu dimbin yawa. Yanzu, na ga ba za a iya yanke irin wannan shawara ba. Sakamakon aikin binciken tattalin arzikin kasar Sin ya bayyana cewa, sana'o'in ba da hidima suna bayar da gudummawa kwarai wajen ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba. Ya kuma bayyana cewa, tsarin tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya samun kyautatuwa."

Amma, Mr. Li ya ce, sabuwar kididdiga ba ta iya sauya ainihin halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki ba. Lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, har yanzu maganar karancin makamashin halittu da maganar kazamtar da muhalli sun fi tsanani. Bugu da kari kuma, ko da yake jimlar GDP ta kasar Sin ta yi yawa sosai, amma har yanzu matsakaicin kudin shiga na kowane Basine ya yi kadan. Sinawan da suka kai kashi 1 cikin kashi 10 suna fama da talauci. Sabo da haka, kasar Sin ba za ta sauya manufar bunkasa tattalin arzikinta da ta riga ta tsara ba.

"A ganina, kididdigar da aka yi a da game da tattalin arziki ba ta yi mummunar tasiri ga manufofin bunkasa tattalin arziki daga duk fannoni ba, haka nan kuma ba za a sauya manufofin bunkasa tattalin arziki daga duk fannoni da ake bi yanzu ba."

Sannan kuma an bayyana cewa, bisa sabon tsarin neman bunkasuwa na tsawon shekaru 5 masu zuwa da aka tsara, kasar Sin ta riga ta tabbatar da cewa, za ta kara kyautata hanyar yin amfani da makamashin halittu da ingancin karuwar tattalin arzikinta. Bugu da kari kuma, kasar Sin ba za ta canja manufar saya ko sayar da kudin musanye da take bi yanzu ba domin tabbatar da neman bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin hali mai dorewa.

Mr. Li Deshui ya ce, kasar Sin za ta kara bunkasa sana'o'in ba da hidima a nan gaba domin ciyar da tattalin arzikinta gaba yadda ya kamata.

Mr. Yuan Gangming, wani masani ne da ya kware kan ilmin tattalin arziki ya nuna goyon baya ga ra'ayin Mr. Li. Mr. Yuan ya nuna cewa, kara bunkasa sana'ar ba da hidima a nan kasar Sin za ta rage dogarar da tattalin arzikin kasar Sin ke yi kan masana'antu da makamashin halittu. A bayyane ne wannan abu ne da ya wajaba ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin hali mai dorewa lami lafiya. (Sanusi Chen)