Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-20 17:06:28    
Birnin Guiyang mai bishiyoyi na kasar Sin

cri

Birnin Guiyang mai bishiyoyi yana kan tudu mai suna Yunnan da Guizhou da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. A nan wuri ne mararrabar Kogin Yangtze, kogi mafi tsawo na farko a kasar Sin da Kogin Zhujiang, kofi mafi tsawo na uku na kasar, a nan kuma akwai tuddai da kwarurruka da kuma makamatansu masu dimbin yawa, sabo da haka bishiyoyi da ciyayi suna ci ainun.

Lambun bishiyoyi da ake kira Guiyang cikin Sinanci yana da nisan kimanin kilomita 2 daga kudancin birnin Guiyang, fadinsa ya wuce kadada 530. Lambun nan lambun bishiyoyi ne mafi girma da ke daura da birni a kasar Sin a halin yanzu.

Da aka sa kafa cikin lambun bishiyoyin nan, to, za a tarar da bishiyoyi iri daban daban masu dimbin yawa har ba ji ba gani, sai a ce, kai, lalle, a nan wata kasar bishiyoyi ce. Bisa kidayar da aka yi, an ce, yawan irin bishiyoyi masu daraja da gwamnatin kasar Sin ke kokarin kare su ya tashi misalin 1,000.

Madam Liu Yun, 'yar yawon shakatawa mutumiyar birnin Shanghai na kasar Sin ta bayyana wa wakilin gidan rediyonmu cewa, "ina sha'awar lambun bishiyoyi na Guiyang ainun. Da ma na yi shirin yin yawon shakatawa a birnin Guiyang cikin makonni biyu kawai, amma ya zuwa yanzu dai, na yi makonni uku ina yawon shaktawa a nan, har ba na so na bar wurin, abin da ya fi kyau shi ne tsawon lokacin hutuna ya kai watanni biyu, amma ina. "

Daidai kamar Madam Liu Yun, masu yawon shakatawa da yawa wadanda suka yi yawon shakatawa a birnin Guiyang, su ma su kan yi sha'awar birnin Guiyang ainun.

Ban da 'yan kabilar Han mafi yawa da ke zama a birnin Guiyang, kuma akwai kananan kabilu daban daban wadanda yawansu ya kai 38 su ma suna zaune a birnin nan. Kidar da kuka ji dazu, kida ce da wakilin gidan Rediyonmu ya dauka a kan titunan birnin Guiyang, yayin da 'yan karamar kabilar Miao ke raye-raye cikin tashin kide-kide da wake-wake don muryar ranar bikinsu na gargajiya.

A duk ranar bukukuwa na kananan kabilu, jama'a su kan runtuma zuwa filin kagaggen marmaro da ke a cibiyar birnin Guiyang daga unguwoyi daban daban, su sanye da sabbin tufafi masu kyaun gani iri na kananan kabilu, su yi raye-raye da wake-wake cikin annashuwa don taya wa juna murnar ranar bikinsu. Masu yawon shakatawa ma su kan more idanunsu da wadannan bukukuwa, su ji dadi ainun.

Ya kasance da kauyukan kananan kabilu da yawa a karkarar birnin Guiyang, ya zuwa yanzu dai 'yan kananan kabilu da ke zaune a wadannan kauyuka suna bin al'adar gargajiyarsu, tufafi da suke sanyawa ma irin nasu ne. Idan wani ya sami damar zuwa wadannan kauyuka, to, zai more idonsa da wadannan abubuwan musamman na kananan kabilu.

Yayin da Madam Wang Shengsheng, jami'ar hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta birnin Guiyang ta tabo magana a kan abubuwan nan, sai ta bayyana cewa, "a galibi dai, ba mu san abubuwa da yawa dangane da kananan kabilu kamar su kabilar Buyi da ta Miao da kuma ta Dong ba. Me nene kimaninsu, wadanne irin tufafi suke sanyawa? Kuma me za mu gani a kauyukan nan? To, abubuwa da ya kamata mu gani su ne dabi'un zaman rayuwarsu da al'adunsu da kuma zaman yau da kullum da kakanni-kakkanin wadannan kananan kabilu suka yi, da yadda su iya kiyaye su har zuwa yanzu, haka zalika da rubutunsu da kuma harshensu."

Ban da wadannan abubuwa, abinci iri daban daban masu dadin ci su ma su kan jawo hankulan masu yawon shakatawa sosai. Da dare ya yi, fitilu na haskaka cikin dakunan cin abinci manya da kananan da ke a gefunan filin kagaggen marmako da tituna daban daban na birnin Guiyang, masu yawon shakatawa su iya shiga cikinsu, su dandana abinci mai dadi iri daban daban wadanda ba a iya same su ba a sauran wurare, su sha daularsu kwarai. (Halilu)