 A ran 18 ga wata an jefa kuri'ar raba gardama game da sabon tsarin mulkin kasar Kongo Kinshasha. Wannan ne karo na farko ke nan da aka jefa kuri'ar raba gardama a kasar a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce. Wannan yana da alamar cewa wani mihimmin taki ne da aka yi kan yadda za a iya cimma burin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar har abada.
Wannan rana, masu jefa kuri'a kusan miliyan 25 wadanda suka yi rajista sun jefa kuri'a a tasoshin kuri'u dubu 36 da suke wurare daban-dabam a duk fadin kasar. Jama'ar kasar Kongo Kinshasha wadanda suka sha wahalolin yakin basasa sosai sun shiga cikin wannan aiki kwarai da gaske.
Mutane masu dimbin yawa wadanda suka gudu yakin basasa na kasar Kongo Kinshasha a sauran kasashe makwabta sun koma kasarku cikin lokaci domin shiga wannan muhimmin ayyukan shimfida dimokuradiyya. A ranar da aka jefa kuri'ar raba gardama, ko da yake an jinkirtar da lokacin bude wasu tasoshin kuri'a domin dalilai iri iri, amma masu jefa kuri'a sun fara jirawa kafin gari ya waye. Wasu masu jefa kuri'a sun bayyana cewa, ko da yake ba a bayar da labarai game da wannan aikin jefa kuri'ar raba gardama sosai ba, mutane da yawa ba su san sabon tsarin mulkin kasar kwarai ba, amma ko shakka babu za su halarci wannan aikin jefa kuri'ar raba gardama domin ciyar da ayyukan shimfida zaman lafiya gaba.

A ran 18 ga wata da dare, Mr. Malu, shugaban kwamitin kula da harkokin zabe cikin 'yanci na kasar Kongo Kinshasha ya shelanta cewa, za a bayar da sakamakon wannan kuri'ar raba gardama a ran 26 ga watan.
Bisa sabon tsarin mulkin kasar, masu jefa kuri'a za su iya zaben shugaban kasar kai tsaye. Wa'adin aikin shugaban kasar zai kai shekaru 5. Bugu da kari kuma sabon shugaban kasar zai iya ci gaba da zaune a kan mukamin shugaban kasar har sau 1 kadai idan an sake zabe shi. Haka nan kuma zai iya nada firayin ministan gwamnatin kasar bayan ya yi shawarwari da rukunin jam'iyyun siyasa na majalisar da yake kunshe da 'yan majalisar dokokin kasar mafi yawa. Sannan kuma, za a raba larduna 10 da wani birnin da ke karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye na yanzu da su zama larduna 25 da wani birnin da ke karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye. Wasu larduna inda ke da wadatattun albarkatun hallita za su iya cin gashin kansu.
An fara yakin basasa ne a kasar Kongo Kinshasha daga watan Agusta na shekarar 1998. A watan Disamba na shekara ta 2002, bangarori daban-dabam da suke adawa da juna sun sa hannu a kan Yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a tsakaninsu daga duk fannoni". Hakazalika, a ran 30 ga watan Yuni na shekara ta 2003, aka kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Kongo Kinshasha. Bisa sabon tsarin mulkin kasar Kongo Kinshasha, a ran 30 ga watan Yuni na shekara ta 2006 ne za a yi babban zaben kasar Kongo Kinshasha, amma wannan sabon tsarin mulkin kasar zai fara aiki ne bayan ya samu amincewa daga yawancin masu jefa kuri'ar kasar wadanda suka jefa kuri'ar raba gardama. Kasar Kongo Kinshasha ta taba tsolma baki a cikin yake-yaken basasa da yawa da suka auku a wasu kasashen da ke makwabtaka da ita. Sabo da haka, ta taba zama wani dalilin da ya yi tashe-tashen hankali a yankin babban tafkin, inda aka yi sanadiyyar mutuwar mutane wajen miliyan 4. Idan za a iya amincewa da tsarin mulkin kasar Kongo Kinshasha, ba ma kawai za a iya kafa tushen doka domin kawo karshen halin tarzoma da lokacin wucin gadi na siyasa da ake ciki a kasar ba, har ma za a iya shimfida hanyar yin zaben majalisar dokokin kasar da shugaban kasar yadda ya kamata. Sabo da haka, an bayyana cewa, ko sabon tsarin mulkin kasar zai iya samun amincewa a cikin wannan kuri'ar raba gardama, wannan wani muhimmin taki ne ga yunkurin kawo karshen kwarya-kwaryar gwamnatin kasar kuma da kafa wata gwamnatin dimokuradiyya a kasar. (Sanusi Chen)
|