Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-16 20:29:10    
Kawancen kasashen Afrika yana jagorar kasashen Afrika zuwa ga tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa

cri
Shekarar nan shekara ce da kasashen Afrika suka fi yin kokari wajen tabbatar da zaman lafiya, kuma sun sami kyakkyawan sakamako a zahiri.

Alal misali, a karo ne na farko, an yi nasarar zaben shugaban kasar Liberiya da majalisar dokoki ta kasar tun bayan da aka kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru 14 ana yinsa a kasar, kuma a karo na farko ne aka zabi wata mace don ta zama shugabar kasar a cikin tarihin Afrika. A kan wannan, Malam Salimu, kwararren Nijeriya kan batuttuwan Afrika ya bayyana wa wakilin gidan rediyonmu da ke a Lagos cewa, "kafa sabuwar gwamnatin kasar Liberiya bayan yakin basasa yana da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a kasar daga duk fannoni, da sake raya kasar bayan yakin basasa, da kuma tabbatar da zaman karko a duk yammacin Afrika. Ko da yake ya zuwa yanzu dai, sabuwar gwamnatin kasar tana fuskantar kalubale mai yawa, amma duk da haka ina sa ran alheri ga sabuwar shugabar kasar Liberiya."

Ban da kasar Liberiya, gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Sudan da gwamnatin mai ikon kai ta kudancin kasar su ma sun kafu a watan Satumba da watan Oktoba na shekarar nan tun bayan da aka shafe shekaru 21 ana yin yakin basasa a kasar. Wannan ma yana da matukar muhimmanci ga samar da zaman lafiya a duk kasar Sudan da kuma tabbatar da zaman jituwar al'ummar kasar. Haka zalika gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya wadda ta kafu a karshen shekarar bara, an koma da ita gida daga Kenya, kasar makwabciyar Somaliya, ta haka gwamnatin nan za ta iya shugabantar jama'ar kasar wajen sake raya kasa. Bugu da kari kuma an kara kwantar da hali mai yamutsi da ake ciki a kasar Ruwanda da Kongo Kinshasa da Burundi da Cote D'ivoire da sauran kasashe.

Da Malam Salimu ya tabo magana a kan kyakkyawan sakamako da kawancen kasashen Afrika ya samu wajen tabbatar da zaman lafiya a Afrika, sai ya ce, "ko da yake ya kasance da kalubale mai yawa da yake fuskanta, amma duk da haka kawancen kasashen Afrika zai kara yunkurawa gaba wajen daidaita su. Na hakake, bisa taimako da gamayyar kasa da kasa ke bayar, kawancen kasashen Afrika zai kara taka muhimmiyar rawarta a nan gaba."

Manazarta suna ganin cewa, kawancen kasashen Afrika shi ma ya sami sakamako mai kyau wajen neman bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen Afrika. Malam Dai Yan wanda ya taba zama jami'in dolimasiya na kasar Sin da ke wakilci a kasashen Afrika da dama ya bayyana cewa, ci gaba da aka samu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin Afrika yana da nasaba da kokarin da kawancen kasashen Afrika ya yi sosai. Ya ce, "yayin da ake bunkasa harkokin tattalin arzikin Afrika, an dora muhimmanci sosai ga yin manyan ayyuka da bunkasa aikin gona da na zirga-zirgar abubuwan hawa da yada labaru ta hanyar zamani. Idan ana son samun bunkasuwa, to, wajibi ne, a hada guiwa a tsakanin bangarori biyu ko bangarori da dama, a jawo kudaden jari daga kasashen waje, kuma a tabbatar da gamayyar tattalin arziki bai daya a babban yankin Afrika."

Manazarta sun nuna cewa, idan nan gaba kawancen kasashen Afrika ya gaggauta samar da zaman karko a shiyya-shiyya, ya yi kokari wajen tabbatar da gamayyar tattalin arzikin Afrika bai daya, ta daidaita matsayin kasashen Afrika daban daban, ta yadda duk nahiyar Afrika ta bayyana ra'ayinta irin daya a kan al'amuran duniya, to, kasashen Afrika daban daban za su kubutar da kansu daga talauci da yamutsi, su yunkura gaba a kan hanyar zaman lafiya da samun bunkasuwa. (Halilu)