Bisa umurnin da shugaban kasar Nigeriya Olusegun Obasanjo ya bayar a ran 13 ga wannan wata, kasar Nigeriya ta soma babban aikin duddubawa a cikin mako guda kan lafiyar zirga-zirgar jiragen sama don kawar da cikas da za a samu wajen yin zirga-zirgar jiragen sama. Ra'ayoyin bainal jama'a suna ganin cewa, a cikin lokacin da bai cika watanni biyu ba, a kasar Nigeriya, an gamu da hadarurruka masu tsamani sosai guda biyu wajen zirga-zirgar jiragen sama, mutane da yawa sun mutu ko ji rauni bisa sanadiyar, saboda haka gwamnatin Nigeriya ta yi niyyar daidaita ayyukan zirga-zirgar jiragen sama.
A gun taron gaggawa da shugaban kasar Obasanjo ya kira a wannan rana kuma manyan jami'an sassan zirga-zirgan jiragen sama na kasar da shugabannin kamfannoni daban daban na zirga-zirgar jiragen sama na kasar suke halarta, an nemi dabarun daidaita matsalolin rashin lafiyar zirga-zirgar jiragen sama da ke kasancewa a kasar, Taron yana ganin cewa, hadarurrukan da aka samu a jere wajen zirga-zirgar jiragen sama sun riga sun kawo tasiri maras kyau sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da sha'anin yawon shakatawa a kasar. Taron ya tsai da kuduri cewa, za a dakatar da zirga-zirgar dukan jiragen saman da aka gano cikas da suke samu a gun duddubawar da aka yi a wannan gami. Mun sami labari cewa, kwararru guda biyu na zirga-zirgar jiragen sama wadanda kungiyar zirga-zirgar jiragen saman farar hula ta kasashen duniya ta tura su za su yi jagorancin aikin duddubawar. Taron ya kuma tsai da kudurin dakatar da harkokin zirga-zirgan jiragen sama na kamfanoni guda biyu masu zaman kansu na kasar wadanda suke da cikas wajen yin zirga-zirgan jiragen sama. An bayyana cewa, wadannan kamfannonin biyu su ne, kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Sosoliso wanda ya gamu da hadarin zirga-zirgar jiragen sama a ran 10 ga wannan wata da wani kamfanin daban .
A ran 12 ga wannan wata, Mr Obasanjo shi ma ya rattaba hannu a kan wani umurnin soke mukaman manyan jami'ai guda biyu na sashen kula da harkokin zirga-zirgan jiragen sama na kasar don yanke musu hunkuci bisa sanadiyar rashin kokarinsu na ba da tabbaci ga kiyaye lafiyar zirga-zirgan jiragen sama.
A ran 10 ga wannan wata, Wani jirgin sama mai lamba DC-10 na kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Sosoliso na kasar Nigeriya ya fadi bisa sanadiyar kaucewar hanyarsa a filin jirgin sama na Port Harcourt, mutane 106, ciki har da 'yan makarantun middle 71 da ke cikin jirgin sun mutu. A watan Oktoba na shekarar da muke ciki, wani kamfanin zirga-zirgan jiragen sama daban na kasar Nigeriya shi ma ya fadi a wurin dab da birnin Lagos , mutane 117 sun mutu bisa sanadiyar, kuma har wa yau dai ba a san dalilin da ya sa hadarin ya auku ba.
Tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, gwamnatin Nigeriya ta soma mayar da sha'anin zirga-zirgan jiragen sama cikin hannun mutane masu zaman kansu, shi ya sa a kasar, an kafa kamfannoni masu zaman kansu fiye da goma na yin zirga-zirgan jiragen sama, dayake ana karancin kudadde da kuma yin takara mai tsanani sosai, shi ya sa wasu kamfannonin Nigeriya sun sayi jiragen saman da kamfanonin zirga-zirgan jiragen sama na wasu kasashen Turai da Amurka suka daina aikinsu , wadannan jiagen sama sun riga sun yi aiki cikin shekaru fiye da 20, daga cikinsu, wanda ya gamu da hadari a ran 10 ga wannan wata ya riga ya yi zirga-zirga cikin shekaru fiye da 32, amma wani daban da ya gamu da hadari shi ma ya yi zirga-zirga cikin shekaru fiye da 22, kuma ba a gyara su a daidai lokaci ba, hanyarsu a filin jirgin sama ma ta lalace sosai, shi ya sa an sami hadarin da ba a gano su ba wajen zirga-zirgan jiragen sama a kasar. A watan Afril na shekarar 2002, gwamnatin Nigeriya ta bayar da matakan kayyade lokaci ga jiragen sama cewa, dole ne su dakatar da zirga-zirgarsu a lokacin da suka cika shekaru 22 wajen zirga-zirgasu, amma dukan kamfannonin jiragen sama sun nuna kiyewarsu sosai, a karshe dai ba a aiwatar da matakin nan ba. Kuma kamfanonnin jiragen sama suna kasancewa cikin halin cin hanci da rashawa, shi ya sa dole ne a daidaita babbar matsalar.(Halima)
|