Ran 12 ga wata, 'yan sanda masu kwantar da tarzoma na kasar Sin sun tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasar Haiti don kare zaman lafiya a wurare da majalisar dinkin duniya ke kare zaman lafiya a kasar Haiti. Wannan karo na uku ne da gwamnatin kasar Sin ta aika da 'yan sanda masu kwantar da tarzoma zuwa kasar Haiti tun bayan watan Oktoba na shekarar 2004. Kasar Sin ta aika da 'yan sanda masu kare zaman lafiya zuwa wurare da majalisar dinkin duniya ke tabbatar da zaman lafiya, wannan wani babban matakin diplomasiya ne da gwamnatin Sin ta dauka, kuma ya nuna wa duniya yadda gwamnatin kasar Sin ke kokari sosai wajen kare zaman lafiya.
A gun bikin da aka shirya a babban filin jirgin sama na birnin Beijing a ran 12 ga wata don yin ban kwana da wadannan 'yan sanda masu kwantar tarzoma, Malama Nan Fujuan wadda take daya daga cikin mata 'yan sandar 8 da kasar Sin za ta aika zuwa kasar Haiti, ta bayyana cewa, "aikin kare zaman lafiya da za mu yi aiki ne mai girma, don haka ina takama da shi. Babu wani abu da ke dame mu, domin muna samun tsayayyen goyon baya daga wajen kasa mahaifiyata."
Kasar Haiti tsibirori ne da ke a arewacin tekun Caribbean, fadinta bai kai muraba'in kilomita dubu 28 ba, yawan mutanenta kuma ya kai miliyan 8 da 'yan doriya kawai, haka nan kuma tana daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya. A watan Febrairu na shekarar 2004, dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Haiti sun tada bore, sun mamaye Port Au Prince, babban birnin kasar da sauran birane, kuma sun yi musayar wuta da magoyan bayan Jean Bertrand Aristide, shugaban kasar na wancan lokaci. Bayan haka bisa matsin da jam'iyyar adawa da Amurka da sauran kasashe suka yi masa ne, Aristide ya ga tilas ne ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kasa, ya yi gudun hijira a kasashen waje. A cikin irin wannan hali ne, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartas da kuduri a an 30 ga watan Afrilu na wancan shekara a kan aika da kungiyar musamman ta kare zaman karko ta majalisar zuwa kasar Haiti don kwantar da zarzoma. Bisa tambayar da majalisar dinkin duniya ta yi mata ne, kasar Sin ta fara aika da 'yan sanda masu kwantar da tarzoma zuwa kasar Haiti a watan Oktoba na wancan shekara.
Ya zuwa yanzu, ba a kwantar da halin yamutsi a kasar Haiti ba. Da Mr Shi Xuepeng, kwamishinan siyasa na rundunar 'yan sanda masu kwantar da tarzoma na kasar Sin da za a aika zuwa kasar Haiti ya tabo magana a kan wannan, ya ce, " Ko da yake halin da ake ciki a kasar Haiti ya kasance mai sarkakiya kuma ya kai intaha, amma duk da haka dukkanmu mun nuna cikakken imani ga kammala aikinmu kwarai. Mun riga mun shirya sosai wajen magance halin da ake ciki a kasar Haiti. Kafin wannan lokaci, an horar da mu a fannoni daban daban a cikin watanni biyu zuwa uku. Yanzu, duk 'yan sandanmu masu kwantar da tarzoma da yawansu ya kai 125 sun kware sosai, sabo da haka ko shakka babu, za mu kamala aikinmu na kare zaman lafiya da kyau a kasar Haiti."
Tun bayan da kasar Sin ta fara shiga aikin kare zaman lafiya da majalisar dinkin duniya ke yi a shekarar 1999, ta riga ta aika da 'yan sanda masu kare zaman lafiya da yawansu ya kai misalin 400 zuwa East Timor da Bosnia Herzegovina da Liberiya da Afghanistan da Kosovo da kuma Haiti. Mr Sun Yongbo, mataimakin ministan kare zaman lafiyar jama'a na kasar Sin ya bayyana cewa, "kasar Sin ta aika da 'yan sanda masu kare zaman lafiya zuwa wurare da majalisar dinkin duniya ke kare zaman lafiya, wannan wani babban matakin diplomasiya ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka, don nuna muhimmiyar rawa da kasar Sin ke takawa bisa matsayinta na zaunanniyar wakiliyar kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, da kokarin da gwamnatin Sin ke yi wajen kare zaman lafiya a duniya. " (Halilu)
|