A ran 7 ga wata, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fara tattara shirin tsare-tsare na wutar yula ta wasannin Olympic da za a yi a shekara ta 2008 a birnin Beijing ga duk duniya. Wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, za a sanar da hanyar da wadanda ke bai wa juna wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing za su bi a farkon shekara ta 2007.
A cikin kwanakin nan, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta tsai da kuduri cewa, tun daga wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008, 'yan wasan kwallon kafa da shekarunsu da haihuwa ba su dace da ka'idar da aka tsara ba ba za su shiga gasar kwallon kafa ta Olympic tsakanin maza da maza ba, wato dukkan 'yan wasan kwallon kafa da za su shiga gasar dole ne shekarunsu da haihuwa ba su wuce 23 ba. Kafin wannan, a cikin gasar kwallon kafa ta wasannin Olympic, an yarda da kasancewar 'yan kwallon kafa 3 da shekarunsu da haihuwa suka zarce 23 a cikin ko wace kungiya.
A cikin kwanakin nan, wani jami'in kwamitin shirya wasannin kasashen Asiya na lokacin hunturu na shekara ta 2007 ya bayyana cewa, an gudanar da ayyukan shafa fage ga wasannin kasashen Asiya na lokacin hunturu iri daban daban lami lafiya, kuma za a kammala gina da gyara dukkan filaye da dakuna na wasanni a karshen shekara ta 2006. za a yi taron wasannin kasashen Asiya na lokacin hunturu na shekara ta 2007 a birnin Changchun da ke arewacin kasar Sin daga ran 28 ga watan Janairu zuwa ran 4 ga watan Fabrairu na shekara ta 2007.
A ran 8 ga wata, kwamitin wasannin Olympic na kasar Sin ya bayar da sanarwa a nan birnin Beijing, cewa Liu Xiang, dan wasan kasar Sin wanda ya zama zakara a cikin gasar gudun tsallake shinge na mita 110 ta wasannin Olympic na Athens, da Yang Yang, shahararriyar 'yar wasan kasar Sin ta wasan gudun kankara na gajeren zango za su bai wa juna wutar yula ta wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino a ran 15 ga wata a madadin kasar Sin. Za a yi wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino daga ran 10 zuwa ran 26 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa. An riga an fara harkar bai wa juna wutar yula ta wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino a cikin kasar Italiya a ran 8 ga wata, kuma za a ci gaba da yin harkar har ranar bude wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino.
Hadaddiyar kungiyar wasan karate ta kasa da kasa ta shirya babban taro na karo na 8 na wakilanta a birnin Hanoi, hedkwatar kasar Vietnam a ran 9 ga wata. a gun wannan taro kuma, ta karbi kungiyoyin wasan karate na kasashen Sudan da Syria da Palasdinu da su zama sababbin mambobinta, sa'an nan kuma, ta yarda da kungiyoyin wasan karate na kasashen Jordan da Benin da Slovenia da Afghanistan da Chile da su zama mambobinta a hukunce, a maimakon na wucin gadi. Ta haka yawan mambobin hadaddiyar kungiyar wasan karate ta kasa da kasa ya kai 106 gaba daya.
An yi bikin jefa kuri'a na kungiya kungiya na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006 a birnin Leipzig na kasasr Jamus a ran 9 ga wata, an ware kungiyoyi 32 da za su yi takara da juna zuwa manyan kungiyoyi 8. An mayar da kungiyoyin kasashen Brazil da Jamus da Argentina da Ingila da sauran kungiyoyi 4 kamar gogaggun kungiyoyi a wannan gami. Kungiya ta C tana kunshe da kungiyoyin Argentina da Holland da Cote d'Ivoire da kuma Yugoslavia, an kiyasta cewa, za su yi takara mai tsanani da juna.(Kande Gao)
|