Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-13 20:42:18    
Yawon shakatawa a birnin Chengde na kasar Sin

cri

Birnin Chengde shahararren wuri ne da sarakunan daular Qing na kasar Sin suke yi hutawa a yanayin zafi. In an tashi daga birnin Beijing zuwa arewa, ana iya tafiya mai nisan kilomita sama da 200, kafin a isa birnin Chengde na lardin Hebei da ke a arewacin kasar Sin.

Birnin Chengde yana tsakiyar duwatsu. Wani sashen Babbar Ganuwa ya yi kamar wata mesa da ke kwance a kan dutse mai suna Jinshanling da ke a kudancin birnin Chengde. Ko da yake yau da shekaru dabbai ke nan da gina Babbar Ganuwar, amma duk da haka ya zuwa yanzu, wannan sashen Babbar Ganuwa yana sumul garau, kuma ba a canja shi ba. Da Malam Mai Zhandong, dan yawon shakatawa ya tabo magana a kan wannan sashen Babbar Ganuwa, sai ya bayyana cewa, "sashen Babbar Ganuwa a kan dutsen Jinshanling yana da girma kwarai. Idan ka hangi nesa daga kan babbar ganuwar nan, za ka ga kololuwan duwatsu layi-layi, da babbar ganuwa da ke kwance kwalmade-kwalmade, zannan zai sa ka jiku ka ce, lalle, babbar ganuwa mai girma ne."

Sarakunan daular Qing wadanda suka yi zamansu a birnin Beijing sun yi sha'awar yin farauta a filayen ciyayi da ke a arewacin Babbar Ganuwa, birnin Chengde kuma yana tsakiyar birnin Beijing da wadannan filayen ciyayi, haka zalika ba sanyi kuma ba zafi a birnin nan mai ni'ima. Da ganin haka, sai sarakunan daular Qing suka gina fada da lambun shan iska a birnin, ta haka ne birnin Chengde ya taba zama cibiyar siyasa da al'adu ta kasar Sin bayan birnin Beijing.

Wurin shakatawa mai suna Bishushanzhuang lambun shan iska ne da sarakunan daular Qing suka gina a karkarar arewacin birnin Chengde. Fadin lambun nan mai kayatarwa ya kai muraba'in mita miliyan 5.6. Madam Wei Li, jagorar yawan shakatawa ta ce, sarakunan daular Qing uku ne suka shafe shekaru 87 kafin su kammala aikin gina lambun nan. Yawan husumiya da haikali da gadoji da dakuna da kuma makamatansu da aka gina a cikin lambun shan iskar nan ya wuce 120. Madan Wei Li ta kara da cewa, "lambun nan ya kasu zuwa gida-gida kamar fada da duwatsu da tafkuna da sararin kasa. Fadar nan ta tashi daidai da karamin fadar sarakunan birnin Beijing, fadinta ya kai sulusin duk girman lambun shan iskar nan. Ban da wadannan ga kuma duwatsu da tafkuna masu kayatarwa."

Yau sama da shekaru 10 da suka wuce, hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta shigar da lambun shan iska da ake kira Bishushanzhuang cikin Sinanci cikin sunayen shahararrun tsofaffin kayayyakin al'adu na duniya. Haka zalika haikali 12 na gidan sarakunan kasar Sin da aka gina a kewayen lambun shan iskar nan su ma hukumar UNESCO ta shigar da su cikin sunayen tsofaffin kayayyakin al'adu na duniya.

Sigogin haikalin nan sun sha bamban da juna. Haikali da ake kira Puning haikali ne na farko na sarakunan kasar Sin da aka gina tun bayan gina lambun shan iskar nan. Haikali mai suna Putuozongchengzhi haikali ne mafi girma a cikin duk wadannan haikalai 12. Sigarsa ta tashi daidai da fadar Budala na birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin. A can zamanin da, yayin da sarkuna da sauran manyan masu mulki na jihar Tibet da lardin Qinghai suka kai ziyarar ban girma ga sarkin kasar Sin, sun kwana a lambun.

Malam Hu Zhanqi, jami'in kula da haikalai na birnin Chengde ya bayyana cewa, "an gina wadannan haikalai masu sigogi iri-iri ne domin kabilu daban daban da su gudanar da harkokin siyasa da na addini. Ban da wannan kuma haikalan nan wurin hutawa ne ga 'yan kabilu daban daban. Haka nan kuma an gina su ne don kara karfin hadin kan 'yan kananan kabilu."

Yau ko da yake daular Qing ta riga ta zama abin tarihi, amma duk da haka ya zuwa yanzu dai an kiyaye lambun shan iskar da haikalan da fada na birnin Chengde da kyau sosai, wadanda ke nuna kyawawan abubuwa masu haske na daular Qing, ta yadda jama'a za su iya tunawa da su. (Halilu)