Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-12 16:02:05    
Yanzu makiyayya ba sa samun matsala wajen samun magani a jihar Tibet

cri

Da akwai makiyayya sama da miliyan daya dake zama a jihar kabilar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta wadda fadinta ya kai muraba'in kilomita miliyan daya da dubu metan a kasar Sin.Da ya ke da akwai ruwa da ciyayi masu yawan gaske a can,makiyayya su kan yi yawo da garakan shannu da tumaki,babu hanyoyi masu sauki shi ya sa makiyayya su kan sha wahala wajen samun magani.Ga shi a yau kome ya canja.Ta yaya aka kawo sauyi a cikin wannan halin kaka-nika-yin da makiyayya suka sami kansu a ciki,to a cikin shirinmu na yau na "kimiyya da ilimi da kuma kiwon lafiya" za mu karanta wani bayanin da wakilin gidan rediyonm ya rubuta mana bayan da ya ziyarci gundumar Zhongba dake kudu maso yammacin jihar Tibet.

Mista Bstan a'dzin mai shekaru 41 da haihuwa,wani makiyayi ne da ke zama a kauyen Budo na gundumar Zhongba.Kwanan baya matarsa na fama da ciwon zuciya,ya kai ta asibitin gunduma wadda take da nisan kilomita dari shida daga kauyen.Da ya shiga asibitin ke da wuya,sai ya ga dansa da ke karatu a garin gunduma ma na ciki asibitin da mallaminsa.Likitan asibitin ya gaya masa dansa na fama da mura,sai ya sha magani babu matsala,amma matarsa na bukatar zama a asibiti domin samun magani.

Bayan da aka kwantar da matarsa a asibitin,mallam Bstan a'dzin ya ji sauki.Ya gaya wa wakilinmu cewa  idan muna fama da kananan matsaloli kamar mura da ciwon kai da kuma gushewar ciki,sai mu sami magani daga likitan kauye.Idan muna fama da babbar matsala,kuma likitan kauye ya gaza kulawa,sai mu je asibitin gunduma domin samun magani."

Gundumar Zhongba mai fadin muraba'in kilomita fiye da dubu arba'in tana shimfidu kan tudu mai tsayin mita dubu biyar daga leburin teku,makiyayya sama da dubu ashirin ke zama a ciki,kiwon dabobi muhimmiyar sana'a a gundumar nan,zaman a nan ba mai sauki ba ne.Har zuwa shekarun 1960 aka sami asibitin jama'a na gundumar Zhongba,wato asibiti na kwarai a wannan wuri.A cikin shekaru da dama da suka gabata,asibitin nan ya dauki nauyin kula da lafiyar makiyayya a wannan wuri.Domin kyautata sharudan kiwon lafiya na asibitin,a shekarar bara,bisa daurin gindin hukumar kiwon lafiya ta wurin aka gina wani sabon ginin asibiti mai benaye biyar masu launin fari da ya iya daukar marasa lafiya sama da dari ke zama a ciki domin samun magani,ginin nan ya fi daukar hankulan mutanen wurin.

Mallam Nyima Dondrup,likita ne dake aiki a cikin asibiti na tsawon shekarun kimanin talatin,shekarunsa ya kai wajen sittin.Makiyayya da yawa sun san shi sosai.Duk lokacin da dan Bstan a'dzin da matarsa ke da matsala,su kan neman likitan Nyima Dondrup.A ganin likitan Nyima Dondrup.sharudan asibitin yana kara kyautatuwa.Ya ce a cikin asibitinmu na yanzu akwai sassan kula da ciwon jiki da na ciki da yara da kuma mata.A da ba haka yake ba.likitocin ba su da kayan aiki sai abin auna bugun jinni da abin kunne na sauraron bugun zuciya.Ga shi a yau muna da na'urori na daukar hoton bugun zuciya da na duba abubuwan dake cikin jikin mutum."

A halin yanzu gundumar Zhongba ta kawo karshen rashin magani.Shugaban hukumar kiwon lafiya ta gundumar nan Mista Zhao Huijun yana mai ra'ayin cewa har wa yau dai da akwai wasu matsalolin da ke bukatar neman samun bakin zare a fannin kiwon lafiya ta gundumar nan.hukumarsa za ta dauki matakan warware su a nan gaba.Ya ce "ana bukatar kyautatuwa cikin gaggawa a fannin kiwon lafiya a gundumar,na farko a kara kwarewar likitoci,na biyu a samu isassun likitoci,na uku a kafa wani tsarin yin gwanzaro domin samar da magani ga makiyayyan dake zama wawware."

Ga shi a yanzu sharudan kiwon lafiya na kara kyautatuwa.dimbin makiyayya sun samu tabbacin samun magani cikin lokaci.Gwamnatin Sin ta tsara wata manufar musamman wajen samar da magani ga mutanen Tibet,wato gwamnatin ta baiwa kowane makiyayi kudin alwas na kiwon lafiya a kowace shekara.lalle makiyayya sun fara jin sauki wajen samun magani.ba su sake samun matsala a wannan fannin ba. (Ali)