Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-09 17:18:25    
Shugabannin kasashen Musulmai sun yi taro a birnin Makka don kiyaye musulunci

cri
A ranar 7 ga wannan wata, an kira taron musamman na shugabannin kasashen kungiyar taron Musulmi a birni mai tsarki na Makka da ke kasar Saudiyya, don tattauna yadda za a fuskanci kalubalen da ke gaban kasashen Musulmi.

Za a shafe kwanaki biyu ana yin wannan taro, inda shugabanni da ministocin harkokin waje mahalartan taron daga kasashe 57 na kungiyar taron Musulmi za su tattauna yaki da ta'addanci da shirin gyaran kungiyar taron Musulmi bisa babban batun wannan taron, wato 'kiyaye musulunci'. Ban da wannan, za a tattauna halin da kasashen Iraki da Palasdinu da Afghanistan ke ciki. Manazarta suna ganin cewa, a gun wannan taro, za a jaddada matsayin kasashen Musulmi daga bangarori biyu.

Da farko, a lokacin taron, kasashe mahalartan taron za su yi kokarin neman samun daidaituwar baki a kan maganar yaki da ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayi, ta yadda za a kawar da abubuwan da za su kawo barazana kan kwanciyar hankali da tsaron zaman al'umma da kuma gyaran sunansu a duniya.

Sarkin kasar Saudiyya Abdullah Bin Abdul Aziz ya yi jawabi a gun bikin bude taron, inda ya yi kira ga kasashen Musulmi da su hada kai da kuma yi hakuri don fuskantar tsattsauran ra'ayi. Ya kuma jaddada cewa, dole ne a yi adawa da tsattsauran ra'ayin da mai yiwuwa ne zai haddasa ta'addanci, kuma a yi kira da a watsa ra'ayoyi na nuna adalci da yi hakuri na musulunci. Sarki Abudullah ya kuma nuna cewa, don neman farfado da kasashen Musulmi, tilas ne a kawar da ra'ayoyi da kuma ayyuka na nuna karfin tuwo da kin jinin zaman al'umma, kuma a aiwatar da gyare-gyare a fannin ba da ilmi. Ya jaddada cewa, wannan taron da ake yi ya bayyana cewa, kasashen Musulmi suna matukar son samun sauye-sauye, don kawo karshen halin da suke ciki na rashin ci gaba.

Babban sakataren kungiyar taron Musulmi Ekmeleddin Ihsanoglu ya jaddada cewa, kamata ya yi a bi asalin ta'addanci don yaki da shi, duk wanda ya aiwatar da aikin ta'addanci, ko shi mutum ne ko kungiya ko kasa ce, ya kamata a yanke masa hukunci. Ya nuna cewa, ya kamata ko wane Musulmi ya yi yaki da ta'addanci.

Na biyu kuwa, kasashen Musulmi suna son ganin wannan taron koli da ake yi zai sa kaimi ga yin gyare-gyaren kungiyar taron masulmi, ta yadda kungiyar za ta kara taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya.

A gun bikin bude taron ministocin harkokin waje da aka shirya a ran 6 ga wata don share fage ga wannan taron koli da ake yi, ministan harkokin waje na kasar Saudiyya Saud al-Faisal ya bayar da jawabi cewa, kasar Saudiyya tana fatan taron koli na kungiyar taron Musulmi wanda za a yi a Makka zai zamanto wnai muhimmin al'amari a tarihin Musulmai. Ya kuma fayyace cewa, shugabanni mahalartan taron za su bincike shirin gyaran kungiyar taron Musulmi a gun wannan taron koli. Wannan shiri kuwa ya dukufa kan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi da ba da taimako ga kasashen kungiyar wajen daidaita matsaloli, da kuma gyaran sunan musulunci a duk duniya, ta yadda za a mayar da martani a yayin da ake nuna wa musulunci kiyayya.

Ra'ayoyin bainal jama'a suna ganin cewa, ko da yake kasashen kungiyar taron Musulmi suna bin musulunci baki daya, amma duk da haka, suna da bambanci a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma tsarin zaman al'umma, sabo da haka, suna daukar ra'ayoyi daban daban a wajen yaki da ta'addanci da kuma gyare-gyare.

Ko da yake kasashe mahalartan taron ba su samu daidaituwar baki a kan wasu batutuwa ba, amma wannan taron koli ya jawo hankulan gamayyar kasa da kasa sosai. Ana yin imani da cewa, taron zai cimma burinsa na 'kiyaye musulunci'.(Lubabatu Lei)