Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-07 19:03:40    
Kasar Sin tana tsaya tsayin daka kan nuna goyon baya ga zagayen tattaunawa na Doha

cri
A ran 5 ga wata, wani jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana tsaya tsayin daka kan zagayen tattaunawa na Doha na kungiyar WTO. Tana kuma fatan za a sami ci gaba irin na ainihi a gun taron ministoci na 6 da kungiyar WTO za ta kira a Hong Kong na kasar Sin, kuma za a kawo karshen zagayen tattaunawa na Doha da ake yi a tsakanin bangarori daban-dabam na kungiyar WTO a shekara ta 2006.

Tun daga ran 13 zuwa ran 18 ga watan Disamba na wannan shekara ne za a yi taron ministoci na kungiyar WTO na 6 a Hong Kong. Wannan wani muhimmin taro ne a cikin zagayen tattaunawa na Doha na kungiyar WTO. A ran 5 ga wata, Mr. Zhang Xiangcheng, direkta mai kula da harkokin kungiyar WTO a ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, kasar Sin za ta yi kokari kan yadda za a sami ci gaba irin na ainihi a gun taron Hong Kong.

"A ganinmu, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su yi kokarinsu domin ciyar da zagayen tattaunawa na Doha gaba. Sakamakon karshen da za a samu a gun shawarwarin zai iya ba da gudumawa ga yunkurin yin ciniki cikin 'yanci a duk fadin duniya. Kuma za a iya daidaita wasu maganganun da ke jawo hankulan kasashe masu tasowa kamar yadda ake fata."

Zagayen tattaunawa na Doha shawarwari mai girma na farko ne da ake yi a kan harkokin cinikayya bayan da kafuwar kungiyar WTO a shekarar 1995. A watan Nuwamba na shekara ta 2001 kungiyar WTO ta fara zagayen tattaunawa na Doha a gun taron ministocin kungiyar WTO da aka yi a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar. Muhimman batuttukan da aka amince da su kuma da ake yi shawarwari sun shafi fannoni 8 ciki har da aikin gona da shigar da kayayyakin da ba na amfanin gona ba a kasuwanni da cinikin sana'ar yin hidima da dai sauransu. Sakamakon da za a samu a gun shawarwari za su bayar da muhimmiyar gudummawa ga yunkurin karfafa amfanin tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban-dabam da ciyar da tattalin arzikin duk duniya gaba.

Maganar aikin gona da ke jawo hankulan mutane sosai ainihin batu ne da ake yi cacar baki a gun zagayen tattaunawa na Doha. Mr. Zhang Xiangcheng ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana fatan wasu kasashe masu sukuni, musamman wadanda suke neman harajin kwastam da yawa, amma suke samar wa aikin gona nasu kudin rangwame da yawa za su iya daukar matakan soke kudin rangwame lokacin da suke fitar da amfanin gona nasu. Kuma ana fatan za su iya rage kudin rangwame da suke bai wa aikin gona."

Kasar Sin tana kokari sosai wajen halartar zagayen tattaunawa na Doha na kungiyar WTO. Bayan da shigowarta a cikin kungiyar WTO a shekara ta 2001, kasar Sin ta fara halartar zagayen tattaunawa na Doha daga duk fannoni, kuma tana daidaita matsayin da membobin kungiyar suke dauka. Ya kamata a ce kasar Sin ta bayar da gudummawarta sosai kan yadda za a yi zagayen tattaunawa na Doha. Mr. Zhang Xiangcheng ya kara da cewa, "Zagayen tattaunawa na Doha shawarwari ne na farko da kasar Sin ta shiga bayan shigowarta a cikin kungiyar WTO. Wannan ne kuma karo na farko da kasar Sin ta shiga ayyukan yin kwaskwarima kan ka'idojin yin cinikin waje a babban mataki. Ko da kasar Sin take sabuwar memba ce a cikin kungiyar, muna kuma mai da hankali kan moriyarmu. Alal misali, wasu sana'o'inmu ba su da karfin yin takarar harkokin kasuwanci, tabbas ne za mu kiyaye su. Sabo da haka, za mu bayyana matsayin da muke dauka filla filla ga sauran membobin kungiyar. Muna fatan za mu iya samun fahimta da goyon bayansu."

Bugu da kari kuma, wannan jami'i ya bayyana cewa, ko da take kasar Sin sabuwar memba ce a cikin kungiyar, kasar Sin za ta yi kokari wajen yin kwaskwarima kan ka'idojin yin cinikin waje a gun zagayen tattaunawa na Doha. Lokacin da take kiyaye moriyarta, za ta gama kan sauran membobin kungiyar domin kafa wani yanayin yin ciniki cikin adalci. (Sanusi Chen)