Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-05 18:42:47    
Yadda za a magance matsalolin ido wajen amfani da inji mai kwakwalwa

cri
Inji mai kwakwalawa wani muhimmin abu ne da aka kago a karni da ya shige.Da bullowarsa ya kawo babban sauyi ga zamanin da mu ke ciki ko waje aiki ko wajen zama ko ma a cikin karatu.Tare da bazuwar hanyoyin sadarwa na internet a duniya,mutane sun kara dogara kan inji mai kwakwalawa,kullum su kan aiki tare da shi cikin ofishi,wasu kuwa su kan shiga yanar giza gizan sadarwa na internet dare da rana.lalle inji mai kwakwalwa ya kawo sauki ga mutane duk da haka ya kan kawo lahani ga lafiyar jiki na mutane.

Matsalar da ake fi fama da ita wajen amfani da inji mai kwakwalwa ita ce ido.idan ka yi yawan amfani da inji mai kwakwalwa,ka kan gaji a ido ko ka jin kamar wani abu ya cika idonka,har ma karfin gani ya ragu.Mista Cao Zhuo,wani dalibi ne dake karatun digiri na farko a jami'ar Beijing,inji mai kwakwalwa ya zama abokinsa cikin karatu,amma karfin ganin idonsa ya ragu a cikin 'yan shekarun da suka gabata,saboda hanyar da yake bi wajen amfani da inji mai kwakwalwa ba daidai ba ne.Mista Cao ya ce:"lahanin da injin ya kawo mini ya bayyanu a ido.Da na shiga jami'ar,karfin gani na idon nawa dukkansu biyu sun wuce digiri daya da digo biyu.ga shi a yanzu daya digo da uku dayan kuwa digo da takwas.Yawan amfani da inji mai kwakwalwa cikin dogon lokaci a jami'ar ya haddasa wannan matsala."

Yayin da mutum ke amfani inji mai kwakwalwa,ya kan sa idonsa kan fuskar inji,tsakanin idonsa da injin ba nisa.idan ya dade yana cikin wannan hali,sai idonsa ya gaji saboda yawan amfani da shi.wani dalili kuwa shi ne kalmomi da hotuna da alamun dake jikin injin su kan fito tare da walkiya,mutum dake amfani da injin ba damar kifta idonsa yadda ya kamata,shi ya sa ya kan ji wani abu ya cika idonsa.

Duk da haka injin mai kwakwalwa ya kan kawo lahani da dama ga ido,za a iya magance shi ta hanyar daukar matakan da ya wajaba.Mista Zhen Hexin,masani ne a fanning yaki da cututtukan da aka fi gani a cikin ayyuka a cibiyar rigakafin cututtuka ta birnin Beijing ya ce:"hanyoyin rigakafi saukake ne.idan ka kan yi amfani da inji mai kwakwalwa cikin dogon lokaci,sai ka dan huta da idonka.kamar a ce idan ka yi aiki na sa'o'I daya ko biyu,sai ka huta minti 10 ko 15.za ka iya huta ta hanyoyi da dama,rufe idonka tare da kwantar da hankalinka,hange itatuwa da shuke shuke masu launin kore da ke nesa." Ya kuma ce yayin da ake amfani da inji mai kwakwalwa,kamata ya yi ya bi hanyoyin daidai da ake bukata,kamar hasken rana ya ninka hasken fuskar injin sau uku,nisan dake tsakanin idonka da injin ya kasance centimeter sama da sittin,za ka iya amfani da ruwan maganin ido domin rage zafin da ka kan ji a idon.

Ba matsalar ido kawai inji mai kwakwalwa ke kawowa mutane masu aiki da su ba,da akwai sauran matsalolin da injin ya kawo musu.Wasu mutane da su kan yi amfani da inji mai kwakwalwa cikin dogon lokaci su kan ji zafi a jikinsu.Mista Chen Cheng,shi ne akawun gwamnatin dake aiki a ofishi a nan birnin Beijing ya taba jin wannan abu.Ya ce:"na kan yi amfani da inji mai kwakwalwa a cikin ofishi wajen rubuta takardu ko neman bayanai.da na gama aikina a rana sai na ji zafi a jikina,musamman a sashen kafada."

Muhimmin dalilin da ya samu wannan matsala shi ne yayin da yake amfani da injin,ba ya motsawa,yana cikin wannan hali mai dogon lokaci wannan ya jawo gjiyar jiki,daga nan ka ji zafi a jiki.a kan samu wadannan alamu a wuyan hannu da damtse da kafada da kuma wuya.Masanin ya ce domin gudun wannan matsala,ya kamata a yi amfani da injin cikin matsayin yadda ya kamata ta yadda hannaye da kafafuwa da jiki suna cikin matsayin daidai,a kowadanne mintuna gomai sai ka dan canja matsayin da jikinka ke ciki.(Ali)