Ran 1 ga wata, an rufe taron kasar Sin a kan ayyukan tattalin arziki da aka saba yi a shekara-shekara a nan birnin Beijing. Taron ya yanke shawara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga bin manufarta dangane da harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni cikin hali mai dorewa don kara bunkasa harkokin tattalin arziki sumul-sumul kuma da sauri a shekarar badi. Sa'an nan ya kamata, a kara daga matsayin yin amfani da makamashi, a kara kokari wajen kare muhalli da daidaita hakikanan matsaloli da ke jawo hankulan jama'a kwarai, kuma a sa kaimi ga tabbatar da zaman jituwa a tsakanin jama'a.
Kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwa ta kasar su ne suka shugabanci taron nan da aka yi tun dga ran 29 ga watan jiya har zuwa ran 1 ga wannan wata. Mr Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar da firayim minista Wen Jiabao ko wannensu ya yi jawabi a gun taron, inda suka gabatar da ka'idojinsu a fili kan tafarkin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin a shekarar badi.
Neman bunkasa harkokin tattalin arziki sumul-sumul kuma da sauri babbar manufa ce ga ayyukan raya tattalin arzikin kasar Sin a shekarar badi. Bisa tafarkin raya tattalin arziki da aka tsaida a gun taron, kasar Sin za ta nace ga yin taka tsantsan wajen aiwatar da manufar aikin kudin gwamnati da na kudi mai inganci, za ta kara kyautata tsarin tattalin arziki daga manyan fannoni, kuma za ta kara wa jama'a musamman manoma yawan kudin shiga da dai sauransu.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an yi ta bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin samul-sumul kuma da sauri, yawan saurin bunkasuwar tattalin arziki ya kan karu da kimanin kashi 9 cikin dari a ko wace shekara. Haka zalika an yi ta kara bunkasa harkokin tattalin arziki cikin daidaituwa da sauransu. Duk wadannan sun aza harsashi mai kyau ga kara bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba.
Dangane da matsalar karancin makamashi da gurbacewar muhalli da aka gamu da su wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin, taron ya nuna cewa, kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen tsimin makamashi a shekarar badi, za ta yi kwaskwarima kan masana'antun narke karfuna da ba da wutar lantarki da na fitar da kayayyakin gine-gine da makamantansu wadanda ke bukatar makamashi mai yawa ta hanyar zamani. Taron ya kuma gabatar da cewa, za a kokarta wajen kawar da gurbacewar muhalli da kare yanayin kasa da sauransu.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta yi ta gudanar da cinikin waje da kyau. Kasar Sin za ta kara aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa don neman samun moriya tare a shekarar badi, za ta yi kokari don daidaita matsalar rashin daidaituwa da aka samu wajen yin cinikin waje, za ta kara yin amfani da jarin waje mai yawa da kara daga matsayinta a wannan fanni.
Bisa tafarkin raya tattalin arzikin kasar Sin a shekarar badi, kasar Sin za ta yi kokari wajen daidaita batutuwa da suka shafi moriyar jama'a, za ta rage gibi da aka samu a tsakanin wurare daban daban kuma a tsakanin masu arziki da matalauta sannu a hankali. Taron ya nuna cewa, wurare masu ci gaba za su kara ba da gudummowa da goyon baya ga wurare marasa ci gaba. Kasar Sin za ta kara samar da guraben aikin yi ga jama'a yayin da take bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma. Za ta kafa cikakken tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a daidai da matsayin bunkasuwar tattalin arziki, ta kare halaliyar moriyar manoma da suke yin aiki a garuruwa da birane. Haka zalika kasar Sin za ta kara kokari wajen sanya ido ga kayan abinci da magungunan sha da ingancin abinci da magunguna masu hadari da zaman lafiyar zirga-zirgar abubuwan hawa da kuma tabbatar da zaman lafiyar jama'a yayin da suke aikin samar da kayayyaki da zaman rayuwarsu.
A shekarar badi, kasar Sin za ta ci gaba da mayar da aikin bunkasuwar tattalin arzikin kauyuka a matsayin babban aikin bunkasuwar tattalin
arzikin kasa, za ta kara wa manoma yawan kudin shiga da kara kyautata matsayin zaman rayuwarsu. (Halilu)
|