Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-02 16:56:54    
Ana farin ciki da damuwa wajen yin rigakafin cutar sida da shawo kanta a kasashen da ke kudancin Afrika

cri
Bisa rahoton da hukumar tsara shirin yaki da cutar sida ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya suka bayar a kwanan baya a kan halin da ake ciki na kamuwa da  cutar sida a duk duniya a shekarar 2005, shiyyoyin Afrika da ke kudancin Sahara har wa yau dai suke zama shiyyar da ke samun wadanda suka kamu da cutar sida mafi yawa a duk duniya, dole ne a ci gaba da inganta manufar yin rigakafin cutar da shawo kanta. Ra'ayoyin bainal jama'a suna ganin cewa, kodayeke halin da kasashen Afrika suke ciki na yin rigakafi da shawo kan cutar sida yana da tsanani sosai, amma fasahohin samun nasara da wasu kasashe suka samu sun bayyana cewa, idan rukunoni daban daban za su iya hada kansu, to za a iya sa ran alheri ga samun nasarar yaki da cutar.

Rahoton ya bayyana cewa, yawan mutanen shiyyoyin Afrika da ke kudancin Sahara ya kai kashi goma cikin dari kawai bisa yawan mutanen duk duniya , amma a wadannan shiyyoyin, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai kashi 60 cikin dari bisa na duk duniya, daga cikinsu da akwai mutane miliyan 25.8 suka kamu da ciwon sida. A shekarar 2005, yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 3.2, daga cikinsu da akwai mutane miliyan 2.4 da suka mutu bisa sanadiyar kamuwa da cutar sida, yawan mutanen da suka mutu ya fi na sauran wurare.

Shiyyar kudancin Afrika cibiyar shiyya ce da take yin fama da matsalar  yaduwar cutar sida, ban da kasar Zimbabuwei, a cikin shiyyar, kasashe daban daban sun kara samun sabbin wadanda suka kamu da cutar , musamman ma a kasar Mozambigue da Swaziland, yawan wadanda suka kamu da cutar ya kara karuwa.

Yin rigakafi da kuma samar da magungunan kawar da cutar muhimmin aiki ne da za a yi don yaki da cutar. Rahoton hukumar tsara shirin yaki da cutar ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya suka bayar ya bayyana cewa, a Afrika da ke kudancin Saraha, in a aiwatar da shirin yin rigakafi da yaki da cutar daga dukan fannoni, za a iya hana kashi 55 cikin dari na yawan sabbin wadanda za su kamu da cutar su kamu da cutar, in ba haka ba, to yawan wadanda za su kamu da cutar zai kara karuwa. Rahoton ya bayyana cewa, shiyyar wurin mai muhimmanci kuma wurin da ke da wuyar yin rigakafi da shawo kan cutar sida. A kasar Afrika ta kudu, a kalla wadanda suka kamu da cutar da yawansu ya kai dubu 900 suna bukatar magungunan sha cikin gaggawa, amma ya zuwa tsakiyar shekarar 2005, a kalla kashi 85 cikin dari na yawan wadanda suka kamu da cutar na kasar Afrika ta kudu ba su sami magungunan sha ba. A kasar Lesotho da Mozambique da sauran kasashe , ana kuma fuskantar halin fama da wahaloli, har ma kashi 90 cikin dari daga cikinsu ba su iya samun damar samun magungunan sha ba.

Mun sami labari cewa, dalilin da ya sa aka haifar da halin nan da ake ciki shi ne saboda farashin magungunan sha da ke kara hauhawa. Ministan kiwon lafiya na kasar Zimbabuwei ya bayyana cewa, kodayake yaduwar cutar sida tana kara tsanani har ta kai matsayin da dole ne a daidaita ta da kuma ana bukatar magungunan sha da warkar da cutar cikin gaggawa ,amma abin bakin ciki shi ne, farashin magungunan sha na yaki da cutar yana ta kara karuwa har  wasu ba su iya samun damar yin amfani da su ba .

Kodayake halin da kasashen Afrika ke ciki na yin rigakafi da shawo kan cutar sida na da tsanani sosai, amma ana sa ran alheri ga shawo kan cutar. A kasar Malawi da ke kudancin Afrika, kamfannoni 15 na wurin da na ketare suna nan suna hada kansu don samar wa ma'aikatansu magungunan sha a fayu don shawo kan cutar.

Ban da shawo kan cutar ta hanyar yin amfani da magungunan sha, kasashen Afrika su ma sun kara karfin yin farfaganda don yin rigakafi da shawo kan cutar.

Kwamitin duk kasar zimbabuwwei na yaki da cutar sida ya bayyana cewa, a bayyane ne yawan wadanda suka kamu da cutar sida ya ragu, inda dukan mutane za su iya cika alkawarinsu, to za a iya kara samun ci gaba wajen yin rigakafi da shawo kan cutar.(Halima)