|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2005-12-02 15:08:08
|
|
Bangarori dabam daban na kasar Amurka sun nuna rashin jin dadi ga manufar da fadar gwamnatin Amurka ta yi kan kasar Iraqi
cri
Wakiliyarmu ta ruwaito mana labari cewa, ran 30 ga watan jiya, kwamitin tsaron kasa da ke karkashin shugabancin fadar gwamnatin Amurka ya sanar da wata takarda mai suna "Muhimman tsare-tsaren samun nasara a kasar Iraqi". A wannan rana kuma, Mr. Bush, shugaban kasar Amurka ya yi wani jawabi, inda ya bayyana muhimman abubuwa na manufarsa kan kasar Iraqi, da yakin Iraqi. Manazarta suna ganin cewa, ba za a iya ganin sabun abubuwa a cikin takardar da fadar gwamnatin Amurka ta sanar, da jawabin da shugaba Bushi ya yi ba.
Wannan takarda mai suna "Muhimman tsare-tsaren samun nasara a kasar Iraqi" da aka sanar da itsa a tashar giza-gizan sadarwa ta fadar gwamnatin Amurka, tsawonsa ya kai shafuffuka 35. Ana ganin cewa, wannan ne karo na farko da gwamnatin Bush ta sanar da manufarta a dukan fannoni game da matsalar kasar Iraqi. Takardar nan ta sake nanata cewa, ba za a tsara shirin lokacin janye sojoji daga kasar Iraki ba, in aka yi haka za a ba da dama ne ga 'yan ta'ada. Takardar ta ce, babu wani yakin da ake iya samun nasara a cikinsa bisa shirin lokaci, haka ma yakin Iraqi." Takardar ta bayyana cewa, bayan shekaru 3 da suka wuce da aka tumbuke mulkin Saddam, ana sa idon ganin kasar Iraqi za ta samu karfi don kayar da 'yan ta'ada, ko wata gwamnati a Iraqi mai dimokuradiya, wannan ba mai yiyuwa ba ne. A sa'i daya kuma, kasar Syria da kasar Iran, wato kasashen da ke makwabtaka da kasar Iraqi suna nuna goyon baya ga 'yan ta'ada da ke kasar Iraqi, wannan kuma ya sa halin yakin Iraqi ya kara yamutsewa.
A wannan rana, a lokacin da shugaba Bush ya yi jawabi a jami'ar sojin ruwa da ke Annapolis na jihar Maryland, ya nuna cewa, yanzu muhimmin abu na manufar kasar Amurka a cikin yakin Iraqi shi ne horar da isassun sojojin kwanciyar hankali na Iraqi, har su samu karfi don yaki da 'yan ta'ada. Ya jaddada cewa, kafin sojojin Amurka su gama aikinsu, ba za su janye jiki daga kasar Iraqi ba. Shugaba Bush kuma ya ce, zai tsaida kuduri kan yawan sojojin Amurka da ke kasar Iraqi, da kuma lokacin da za a janye sojoji bisa hakikanin halin da kasar Iraqi ke ciki, da hukuncin da jami'an da ke jagorancin sojoji a Iraqi suka yanke, amma ba bisa ra'ayin wasu 'yan siyasa na Washington ba, wato tsara shirin lokacin janye jiki.
An bayar da takardar fadar gwamnatin Amurka, da jawabin shugaba Bush a lokacin da sojojin Amurka suke gamuwa da matsaloli a Iraqi, kuma a dai dai lokacin da jama'ar kasar amurka suke kara kira kan janye jiki daga Iraqi.
Yanzu, yawan sojojin kasar Amurka da ke Iraqi ya kai dubu 159. Tun bayan da aka tayar da yakin Iraqi, akwai sojojin Amurka sama da 2100 da suka rasa rayukansu. Jama'a da mutanen bangarori dabam daban na kasar Amurka suna la'antar gwamnatin Bush sabo da ta rasa muhimman tsare-tsare kan yakin Iraqi, kuma sun bukaci gwamnatin bi da bi da ta janye sojojinta daga kasar Iraqi tun da wuri. Jama'a da yawa sun bayyana cewa, ba za su amince da shugaba Bush ba. Kuma yawan mutanen da suke goyon bayan Bush ya yi ta raguwa. Bisa sakamakon binciken ra'ayin jama'a da aka yi a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, ya nuna cewa, kashi 62 cikin dari bisa na dukan masu fadan ra'ayoyinsu ba su yarda da manufar da shugaba Bush ya dauka kan kasar Iraqi ba, kuma yawan mutanen da suke goyon bayan Bush ya riga ya ragu zuwa kashi 37 cikin dari.
'Yan jam'iyyar dimokuradiya, da jama'a da yawa na kasar Amurka suna ganin cewa, ba za a iya ganin sababbin abubuwa ba a cikin takardar fadar gwamnatin Amurka, da jawabin shugaban kasar. Wannan ya nuna cewa, ko takardar da fadar gwamnatin Amurka ta fitar, ko jawabin da Bush ya yi, dukansu babu wani sassauci na nuna rashin jin dadi na bangarori dabam daban na kasar Amurka ta yi, da kyar gwamnatin bush za ta janye jikinta daga matsalar Iraqi. (Bilkisu)
|
|
|