Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-02 09:35:11    
Yaran fatan alheri na wasannin Olimpic na Beijing sun sami maraba daga dukkan fannoni

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,kayayyakin fatan alheri na wasannin Olimpic na Beijing wato yaran fatan alheri biyar sun fito a gabanmu,kuma sun sami maraba da yarda daga dukkan fannoni a duk fadin duniya,wadannan yara suna da siffofi daban daban alal misali kifi da panda da gwankin Tibet da tsatsewa da kuma wuta mai tsarki ta wasannin Olimpic.

Kafin wata guda da ya wuce,ba a san mene ne siffarsu ba,amma da kyar a saye su,kusan dukkan jama`ar kasar Sin suna kaunarsu,kayayyakin tunawa dake shafar yaran fatan alheri suna yaduwa sosai a wurare daban daban na kasar Sin,a wasu wurare kuwa,irin wadannan kayayyaki su kan kare a cikin kantanin lokaci.A ran 30 ga watan jiya,madam Tang wadda ta zo birnin Beijing daga Hongkong,yankin musamman na kasar Sin ta je kantin musamman na wasannin Olimpic dake cikin babban ginin sayar da kayayyaki na titin Wangfujing na birnin Beijing tana fatan za ta sayi kayayyakin wasa masu siffar yaran fatan alheri,amma mai sayar da su a kantin ta gaya mata cewa,`Allah ya gafarta,sun kare`.Madam Tang ta yi bakin ciki kwarai da gaske ta ce,`Mun zo birnin Beijing ne daga Hongkong musamman domin sayen kayayyakin yaran fatan alheri,amma amma sun kare,ba mu samu ba.`Mr.Zhen Yudong,wanda ke kula da aikin kantin wasannin Olimpic na babban ginin sayar da kayayyaki na titin Wangfujing na birnin Beijing ya gaya wa manema labarai cewa,`Kowace rana,kantinmu ya kan shigo da kayayyakin yaran fatan alheri da yawansu ya kai akwatuna fiye da 60,amma cikin awa daya da rabi,sai sun kare cikin sauri.`A sauran kantunan sayar da kayayyakin wasannin Olimpic na Beijing,kayayyakin yaran fatan alheri su ma su kan kare,bi da bi ne mutane da yawa suna ta tambayen su yaushe za su sayi kayayyakin yaran.

Ba ma kawai a birnin Beijing ba,har ma a birnin Shanghai da birnin Guangzhou da birnin Chengdu da sauran birane,yaran fatan alheri sun sami maraba sosai daga dukkan fannoni.

Sunayen yaran su ne Beibei da Jingjing da huanhuan da Yingying da Nini,siffofinsu suna da nasaba da teku da kungurmin daji da wuta da kasa da kuma sararin sama,wannan ya nuna mana zaman jituwa dake tsakanin dan adam da halittu,wato ya dace da tunanin `tsabtatacen wasannin Olimpic` na wasannin Olimpic na Beijing.

Ban da wannan kuma,siffofinsu sun hada da al`adun gargajiya na kasar Sin,ana iya cewa,siffofinsu suna da farin jini kwarai da gaske.

Kazalika,siffofinsu sun yi kyau sosai,game da wannan,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogge ya ce,`Da zarar na ga wadannan kayayyakin yara,ina jin farin ciki kwarai da gaske,kamata ya yi mu nuna biyayya ga `yan fasaha wadanda suka kago su,na amince da cewa,yaran fatan alhari na wasannin Olimpic za su sami zuciyar duniya.`

Kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing ya taba yi bincike kan wannan,sakamakon da aka samu ya nuna mana cewa,yaran da yawansu ya kai kashi 98 cikin dari suna ganin cewa,kayayyakin yaran fatan alhari suna da kyan gani sosai.

Abu mai ban sha`awa shi ne idan an hada sunayensu,to,ma`anar kalmar nan ita ce `Beijing yana yin maka maraba`.Ana iya cewa,kayayyakin fatan alhari na wasannin Olimpic sun fi tambari da kirarin wasannin Olimpic wajen kawo tasiri da jawo hankali.Yaran fatan alheri biyar suna bazawa wayin kan kasar Sin da amincin kasar Sin a ko ina na duk fadin duniya.(Jamila zhou)