 Ran 29 ga wata, wakilan gwamnatin kasar Sudan da na manyan kungiyoyin dakaru biyu na yankin Darfur wadanda ke adawa da gwamnatin sun fara yin shawarwarin sulhu a tsakaninsu a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, don neman samun hanyar da za a bi wajen neman bakin zaren warware rikicin Darfur kwata-kwata cikin kawancen kasashen Afrika.
Jami'an kawancen kasashen Afrika wadanda suka halarci shawarwarin, sun bayyana cewa, ana yin shawarwarin sulhu na wannan karo ne musamman domin yin tattaunawa a kan hanyar daidaita hargitsin Darfur a siyasance da batun raba mukamai da albarkatun kasa na yankin Darfur da zaman lafiyar yankin da kuma warware rikicin jin kai da sauransu. Jami'an nan sun kara da cewa, za su sa kaimi ga bangarori daban daban da su kulla yarjejeniyar zaman lafiya game da wadannan batutuwa a gun shawarwarin sulhun nan, amma kawancen kasashen Afrika ba za su tsara jadawalin shawarwarin sulhun ba.

Kafin wannan , an taba samun dan sakamako ne kawai a gun shawarwarin sulhu da aka yi har sau 6 a kan neman warware rikicin Darfur. Sakamakon nan shi ne aka girke masu lura da tsagaita bude wuta da sojojin tsaro na kawancen kasashen Afrika a yankin Darfur, hakan nan kuma gwamnatin kasar Sudan da manyan kungiyoyin dakaru masu adawa da gwamnatin biyu na yankin Darfur sun kai ga daddale wata sanarwa kan ka'idojin raba mukamai da albarkatun kasa da halin zaman lafiya da daidaita matsalar rashin jin kai a yankin Darfur.
Manazarta suna ganin cewa, ko da yake masu lura da harkokin tsagaita bude wuta da sojojin tsaro na kawancen kasasahen Afrika da ke girke a yankin Darfur suna taka 'yar muhimmiyar rawa ce kawai wajen tabbatar da zaman karko a yankin, dalilin da ya sa haka shi ne domin yawansu ya yi kadan, kayayyakin aikinsu na baya-baya, kuma suna shan wahalhalu wajen samun guzuri. A cikin watannin nan biyu da suka gabata, an sha saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankin Darfur, al'amuran hargitsi da aka yi a tsakanin wasu dakaru sun yi ta aukuwa, duk wadannan sun shaida cewa, kawancen kasashen Afrika ya gamu da wahala a yankin.
Ban da wannan kuma, ko da yake bangarori mahalarta shawarwarin sulhu na kasar Sudan sun kai ga daddale sanarwa a kan ka'idojinsu, amma ya zuwa yanzu ba su sami ra'ayi daya a kan yadda za a aiwatar da wadannan ka'idoji filla-filla ba, sabo da haka ba su iya daddale wata yarjejeniyar zaman alfiya a tsakaninsu daga duk fannoni ba a cikin wani tsawon lokaci da ya wuce.
A kwanakin nan, kungiyar neman kwatar 'yancin kasar Sudan ta sami sabane-sabane sosai a kan batun shugabancin aikin soja da na siyasa, kana an sami shugabannin kungiyar nan biyu. Ko da yake yanzu manyan rukunoni biyu na kungiyar sun taba bayyana cewa, za su shiga shawarwarin sulhu na karo na 7 bisa matsayinsu daya cikin daidaituwa, amma mai yiwuwa ne, za a sake tsunduma cikin mawuyancin hali saboda manyan sabane-sabane da ke kasancewa a cikin kungiyar.
Haka zalika a ranar da aka fara yin shawarwarin sulhu a wannan gami, kungiyar kwaskwarima da bunkasuwa ta kasar wadda ta kafu ba da dadewa ba don yin adawa da gwamnati a yankin Darfur ta yi hargitsin zubar da jini a yankin, sakamakon haka sojoji da 'yan sanda sama da 30 na kasar Sudan sun rasa rayukansu. Makadudin kungiyar nan shi ne domin mayar da martani ga hana ta shiga cikin shawarwarin sulhun nan. Kungiyar ta bayyana cewa, idan ba a shigar da ita cikin shawarwarin sulhu ba, to, za ta ci gaba da kai hare-hare a yankinsu.
Dangane da batun Darfur mai sarkakiya a yanzu, kafofin watsa labaru suna ganin cewa, babu yadda za a yi a sami babban ci gaba wajen yin shawarwarin sulhu a wannan gami, sai duk bangarori mahalartan shawarwarin su nuna sahihanci sosai kuma su yi babban kokari. (Halilu)
|