A ran 28 ga wannan wata a nan birnin Beijing, kungiyar Unesco ta yi bikin bude taro na biyar na ba da ilmi ga duk jama'a a karo na biyar. Shugabannin kasashe daban daban da ke kula da ayyukan ba da ilmi da suka zo daga wurare daban daban na duk duniya da wakilan kungiyoyin kasa da kasa sun mai da hankali ga yin ma'amala da bincike kan batun ba da ilmi ga duk jama'a, musamman ma ga kauyawa da kuma yaki da jahilci da sauran fannoni da yawa. A gun bikin budewar taron, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi jawabin fatan alheri, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da inganta aikinta na ba da agaji ga tarbiyyar kasashe masu tasowa.
A shekarar 1990, a bayyane ne kungiyar Unesco ta gabatar da ra'ayinta na ba da ilmi ga duk jama'a. A cikin nasa jawabin, a karo na farko ne Mr Wen Jiabao ya darajanta taimakon da kungiyar Unesco ta ba da wajen cim ma burin tarbiyya a duk duniya. Ya bayyana cewa, hakikanin abubuwa sun shaida cewa, kungiyar Unesco ta mayar da shirin ba da ilmi ga duk jama'a bisa matsayin babban aikin farko da take zaba , wannan ya dace da burin kasashe daban daban da gamayyar kasa da kasa , taron ya aiwatar da babbar manufarsa ta sa kaimi ga ba da ilmi ga duk jama'ar duniya da kuma mayar da aikin yaki da jahilci da ba da ilmi a kauyyuka bisa matsayin babban batunsa, wannan ya bayyana cewa, gamayyar kasa da kasa ta mai da hankali sosai ga ba da ilmi a kauyyuka da shiyyoyi marasa ci gaba.
Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara ba da gudumuwarta wajen ba da ilmi ga duk jama'a a duk duniya, kuma a gun taron, ya ba da alkawari cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara inganta aikinta na ba da agaji ga aikin ba da ilmi na kasashe masu tasowa. Ya bayyana cewa, na farko, kasar Sin za ta kara habaka matakan horar da shugabannin makarantu da malaman koyarwa na kasashe masu tasowa a kasar Sin, za ta kara yawansu daga mutane 500 zuwa mutane 1500 a kowace shekara. Na biyu, za ta samar wa cibiyar kara karfin kasashen Afrika da cibiyar ba da ilmi ga mata da yara na kungiyar Unesco agaji da yawansu ya kai kudin Amurka dolla miliyan daya, kuma cikin hadin guiwarsu ne za a yi aikin bincike da ba da horo ga wadanda suke bukata, na uku, bisa bukatun kasashe masu tasowa ne, a cikin shekaru uku masu zuwa, za ta ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen gina makarantun kayyuka da yawansu zai kai dari tare da cikakkun kayayyakin koyarwa.
Bisa bayanin da Mr Wen Jiabao ya yi, an ce, tun daga shekarar 2006, yawan daliban da za su sami shikolaship daga wajen gwamnatin kasar Sin zai karu zuwa mutane dubu 10 a kowace shekara, kuma za ta kara yawan kudadden taimako da za ta samar bisa halin da ake ciki. A sa'I daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin kara ba da taimako ga aikin ba da ilmi na kasashe masu tasowa wadanda suke fama da bala'in girgizar kasa da tsunami da babbar guguwr iska da sauran bali'o'in halitta masu tsanani .
Don sa kaimi ga aikin ba da ilmi ga jama'a a duk duniya, Mr Wen Jiabao ya gabatar da ra'ayin kasar Sin, ya bayyana cewa, hukumomin da abin ya shafa na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa ya kamata su kara ba da amfaninsu da kuma ci gaba da inganta hadin guiwar da ke tsakanin kasa da kasa da kuma girmama hanyoyi iri iri da ake bi don raya al'adu da tarbiyya.
Mr Wen Jiabao ya kuma bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu da ke da ma'anar tarihi wajen ba da ilmi ga duk jama'arta. Ya zuwa shekara 2004, yawan mutanen kasar Sin da suka sami ilmi ta hanyar shiga makarantu cikin shekaru 9 a fayu ya kai kashi 94 cikin dari, kuma yawan samari masu jahilci ya ragu zuwa kashi 4 cikin dari, yawan yara mata da suka sami damar shiga makaranta ya kai kashi 98.9 cikin dari. Ta hanyar kokarin da aka yi cikin shekaru 15 da suka wuce, kasar Sin ta sa mutane da yawansu ya kai miliyan 94 suka kawar da jahilci.
za a yi kwanaki biyar ana yin taron, taron zai bayar da "Sanarwar Beijing" da "Shirin yin aiki cikin hadin guiwa" da kuma yin kokarin fitar da matakan hakika don sa kaimi ga raya aikin ba da ilmi ga duk jama'a.(Halima)
|