Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-30 09:29:15    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(24/11-30/11)

cri
A ran 25 ga wata, a nan birnin Beijing, an fara gina kauyen manema labarai na wasannin Olympic na shekara ta 2008 wanda ke zauna a arewa maso gabashin mihimmin fili na wasannin Olympic na Beijing da kuma wurin yawon shakatawa na daji na Olympic. Kauyen nan yana da nisan kilomita 5 tsakaninta da muhimmin fili na wasannin Olympic na Beijing da kuma cibiyar watsa labarai ta wasannin Olympic, in an tuka mota, to za a kashe mintoci 5 zuwa 10. Murabba'in gine-gine gaba daya ya kai kusan mita dubu 630. Kauyen zai samar da sharudda masu kyau wajen zaman manema labarai daga wurare daban daban. Kuma an yi kiyasta cewa, za a kammala aikin nan a farkon shekara ta 2008.

A ran 23 ga wata, bi da bi ne kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan shawo kan magani mai sa kuzari a cikin wasannin Olympic na shekara ta 2008 tsakaninsa da kwamitin yaki da magani mai sa kuzari na kwamitin wasannin Olympic na Beijing da kuma cibiyar yin nazarin ilmin likita kan motsa jiki ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin. wani jami'in kula da harkokin lafiyar jiki da ke cikin kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, daddale yarjejeniyar ya alamta cewa, aikin shara fage wajen shawo kan magani mai kuzari a cikin wasannin Olympic na Beijing ya riga ya shiga wani sabon mataki, haka kuma a lokacin wasannin Olympic na shekara ta 2008, kwamtin shirya wasannin Olympic na Beijing zai dukufa kan yin ayyukan shawo kan magani mai kuzari cikin adalci.

A ran 27 ga wata, a birnin Melbourne na kasar Australia, an rufe gasar fid da gwani ta wasannin kungunbala da lankwashe-lankwashe ta duniya ta shekara ta 2005 wadda aka shafe kwanaki 7 ana yinta. 'yan wasa na kasar Sin sun samu lambobin zinariya 2 a cikin gasar, wato Cheng Fei ta zama zakara a cikin gasar vaulting horse tsakanin mace da mace , kuma Xiao Qin ya samu lambar zinariya a cikin gasar pommelled horse. Kungiyar kasar Amurka kuwa ta samu lambobin zinariya hudu bisa rinjayenta wajen wasannin mata, shi ya sa ta zama ta farko a cikin jadawalin samun lambobin zinariya.

A ran 27 ga wata, a cikin gasar wasan kankara ta cin kofin duniya da ake yi a birnin West Allis na jihar Wisconsin ta kasar Amurka, 'yan wasa na kasar Sin Wang Manli da kuma Wang Beixing sun samu lambar zinariya da ta azurfa bi da bi a cikin gasar wasan kankara na mita 500 tsakanin mace da mace.

An rufe budaddiyar gasar wasan judo ta duniya ta karo na biyar da aka yi a cikin dakin motsa jiki na jami'ar Qingdao da ke birnin Qingdao na kasar Sin a ran 27 ga wata da dare. A cikin gasar ta kwanaki biyu, 'yan wasa na kasar Sin sun samu lambobin zinariya hudu da ke cikin 16, kuma kungiyar kasar Japan ta samu lambobin zinariya biyar, haka kuma kungiyar kasar Korea ta Kudu ta samu shida, kungiyar kasar Jamus ta samu guda. Budaddiyar gasar wasan judo na duniya na birnin Qingdao da ke cikin kasar Sin gasa ce ta duniya wadda Hadaddiyar kungiyar wasan judo ta duniya ta amincewa, ya zuwa yanzu an riga an yi wannan gasa a birnin Qingdao har shekaru biyar.

A ran 26 ga wata, an yi gasar gudun dogon zango wato Marathon ta duniya ta shekara ta 2005 a birnin Shanghai na kasar Sin, dan wasan kasar Sin Han Gang ya zama zakara a cikin gasa tsakanin namiji da namiji bisa makinsa na awa 2 da minti 13 da dakika 22, haka kuma 'yar wasa ta kasar Sin Zhang Shujing ya samu lambar zinariya a cikin gasa tsakanin mace da mace bisa makinta na awa 2 da minti 34 da dakika 25.(Kande Gao)