Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-29 18:28:26    
Sha'anin yawon shakatawa na Xinjiang ya samar wa jama'arsa alheri

cri

Jihar Xinjiang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da kabilar Weiwu'er ke cunkushe tana arewa maso yammacin kasar Sin, shi ne wuri mai ni'ima a fannin yawon shakatawa. A cikin shekaru gomai da aka bunkasa sha'anin yawon shakatawa a jihar, sha'anin ya zama daya da ke cikin manyan masana'antun jihar Xinjiang. A sa'i daya kuma, jama'a ta kabilu daban daban a jihar suna kara samun moriya mai tsoka daga sha'anin yawon shakatawa.

Tabkin Kanasi da ke arewacin jihar Xinjiang wurin yawon shakatawa ne da ya yi suna a kasar Sin da kasashen waje. Wani tsohon 'dan kabilar Mongoliya mai suna Ye'erdexi yana zama a bakin tabkin Kanasi, tun daga shekarunsa ya kai 13 da haihuwa, ya fara rera wani irin kayan kida na kabilarsa wato Chu'er. Abu na mamaki ga Tsohon Ye'erdexi shi ne rera kayan kida mai suna Chu'er ya canza zaman rayuwarsa sosai bayan shekaru fiye da 50.

Tare da bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a wurin Kanasi, 'yan yawon shakatawa masu kara yawa suna zuwa wurin, wannan ya samar wa iyalan Ye'erdexi damar yin ciniki. Kafin shekaru da dama, sun canza gidagensu da su zama wuraren karbar 'yan yawon shakatawa, haka kuma rera kayan kida Chu'er da tsohon Ye'erdexi ya yi ya fi jawo hankulansu.

'Yar tsohon Ye'erdexi malama Meihua ta gaya wa wakilinmu cewa, a da dukkan iyalanta mafarauta ne, amma wannan zaman rayuwa ya canja a sakamakon bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a wurin. Ta ce, bayan da iyalanta sun fara gudanar da sha'anin yawon shakatawa, sun sayi na'urori na zamani da yawa kamar TV da taliho da firiji da dai sauransu, a shekarar da muke ciki, suna shirin sayen wani mota.

Ganin kyakkyawan zaman rayuwa, tsohon Ye'erdexi yana da wani sabon shiri. Ya gaya wa wakilinmu cewa, ' 'Dana na biyu yana koyon rerar kayan kida Chu'er a halin yanzu, kuma ya riga ya koyi wannan har shekaru uku ko hudu. A shekara mai zuwa, zai gama karatunsa, zai iya rera Chu'er tare da ni.'

Da sauran mazaunan kauyen suka ga canjawar zaman rayuwar tsohon Ye'erdexi, sai sun fara gina dakunan cin abinci ko sayar kayayyakin da aka yi da madara ko sayar da tsarabobi ga 'yan yawon shakatawa, a halin yanzu dai, kashi 70 da ke cikin dari na mazaunan kauyen suna gudanar da sha'anin yawon shakatawa.

Ban da wuraren da ke bakin tabkin Kanasi, a sauran wuraren yawon shakatawa na Xinjiang, mazaunansu suna gudanar da sha'anin yawon shakatawa suna canza zaman rayuwarsu sosai. Wani tsohon 'dan kabilar Weiwu'er mai suna Abulizi da ke zama a Tulufan, shahararren wuri wajen samar wa inabi, shi ne daya da ke cikin mazaunan.

Tsohon Abulizi ya gaya wa wakilinmu cewa, a da ya kan dasa inabi, a ko wace shekara kudin shigarsa ya kai dubu da dama kawai. Amma tun daga shekaru fiye da goma da suka gabata, wato lokacin da yake gudanarwa da sha'anin yawon shakatawa, ya kyatatta zaman rayuwarsa sosai. Ya ce,

(Murya Ta Hudu)

'A ko wace shekara, na kan karbi 'yan yawon shakatawa da yawansu ya zarce dubu daya. A bana, baki sun yi yawa, ya zuwa yanzu, na riga na karbi baki 1200, kudin shiga da na samu ya zarce kudin Sin Yuan dubu 12.'

Domin kara sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a Xinjiang, a shekaru 5 da suka gabata, gwamnatin jihar Xinjiang ta zuba jari da yawansu ya zarce biliyan 4 domin gina da kiyaye wurare masu ban sha'awa a jihar. Ban da wannan kuma, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gwamnatin jihar Xinjiang sun zuba jari da yawansu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 10 domin gina manyan ayyuka da filayen jirgin sama dangane da sha'anin yawon shakatawa. Danladi).