Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-29 18:21:49    
Kasar Sin za ta horar da jami'an ba da ilmi 3000 na Afrika a cikin shekaru uku masu zuwa

cri

Ran 27 ga wata, Madam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta horar da jami'ai masu kula da aikin ba da ilmi da yawansu zai kai 3000 domin kasashen Afrika. Sa'an nan kuma kasar Sin za ta kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakaninta da kasashen Afrika a fannin aikin ba da ilmi ta hanyar daukar dalibansu da aikawa da kwararru masu aikin ba da ilmi na Sin zuwa kasashen Afrika da dai sauransu.

Madam Chen Zhili ta yi wannan kalami ne a gun taron dandalin ministocin ilmi na Sin da Afrika da aka shirya a birnin Beijing ran 27 ga wata. Ministocin ilmi na kasashen Afrika 17 da jakadunsu da ke wakilci a kasar Sin sun halarci taron nan.

Wani batu mai muhimmanci da aka tattauna a gun taron nan shi ne, hanyar da za a bi nan gaba wajen yin hadin guiwa da ma'amala tsakanin Sin da Afrika a fannin aikin ba da ilmi. A gun taron nan, Madam Chen Zhili ta bayyana wa jami'an ilmi na kasashen Afrika cewa, "kamar yadda take yi a kullum, gwamnatin kasar Sin za ta kara kokari sosai wajen yin hadin guiwa da ma'amala a tsakaninta da kasashen Afrika a fannin aikin ba da ilmi. Bisa bukatun da kasashen Afrika ke yi don neman bunkasa harkokin zamantakewar al'umma, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa ayyukanta wajen bai wa kasashen Afrika gudummowar gabatar da ilmi ta hanyar daukar dalibansu da aika musu masanan ilmi da dai sauransu."

A cikin shekaru da yawa da suka gabata, kasar Sin ta yi ma'amala da hadin guiwa a tsakaninta da kasashen Afrika a fannin aikin ba da ilmi kuma ta hanyoyi daban daban. Tun daga shekarun 1950, kasar Sin ta ba da sukolashif din gwamnati ga dalibai dubu 17 da suka fito daga kasashen Afrika 50. Yanzu, yawan daliban kasashen Afrika da ke iya samun sukolashif daga gwamnatin kasar Sin ma ya kan kai 1200 a ko wace shekara, yawan nan kuma zai karu da ninki daya nan da shekaru 5 masu zuwa. Haka zalika kasar Sin ta aika da malaman koyarwa da yawansu ya wuce 500 zuwa Afrika don ba da taimako wajen horar da 'yan kimiyya da fasaha da bunkasa harkokin ba da ilmi a makarantar sakandare da kolijoji da kuma jami'o'i.

Jami'an ilmi na kasashen Afrika wadanda suka halarci taron nan sun nuna yabo da goyon baya ga kara karfin hadin guiwar da za a yi a tsakanin Sin da kasashen Afrika a fannin aikin ba da ilmi. Sa'an nan kuma suna fatan nan gaba kasashen Afrika za su kara samun gudummowar ba da ilmi daga wajen kasar Sin. Malam Aires Ali, ministan ilmi da al'adu na kasar Mozambique ya bayyana cewa, "yana fatan nan gaba za a aika da jami'ai da shugabannin makarantu na kasarsa zuwa kasar Sin don koyon sakamako da kasar Sin ta samu, sa'an nan kuma yana fatan bangaren Sin zai aika da kwararru da malaman koyarwa zuwa kasarsa don yi musu jagoranci. "

Jami'in nan ya kara da cewa, kasar Sin ta kware wajen horar da malaman koyarwa.

Madam M. Y. Katagum, jami'ar ba da ilmi ta kasar Nijeriya ta bayyana cewa, tana fatan masu aikin ilmi na kasar Sin za su kai ziyara a Afrika don kara dankon aminci ta hanyar koyi da juna. Ta ce,

"Sin da Nijeriya suna da dimbin abubuwa bai daya, mutanensu suna da yawan gaske, kuma yawan mutane da ke neman ilmi ma suna da yawa. Haka nan kuma suna da mutane da yawa da ke zama a kauyuka, a cikin irin wannan hali , suna bukatar yin ayyuka masu yawa wajen ba da ilmi a kauyuka. Haka nan kuma suna fuskantar matsaloli da wahalhalu iri daya wajen bunkasa aikin ba da ilmi a nan gaba. Don haka, wajibi ne, mu taimaki juna, mu sami hanyar da za mu bi don daidaita matsalolin nan."

Malam Zhou Ji, ministan ilmi na kasar Sin shi ma ya bayyana a gun taron cewa, Sin da yawancin kasashen Afrika suna hadin guiwa da ma'amala a tsakaninsu a fanning ba da ilmi, ta haka Afrika ta kara fahimtar kasar Sin, sa'an nan kuma kasar Sin ma tana kara fahimtar Afrika, wannan ya samar da sharadi ga kara karfin hadin guiwa tsakanin Sin da Afrika a fannin aikin ba da ilmi. (Halilu)