Yau ran 26 ga watan nan a nan birnin Beijing an yi babban taron murnar cikakkiyar nasarar da aka samu a wajen harba kumbon sama janati mai daukar mutane na lamba 6 na Shenzhou na kasar Sin. A gun wannan taro Fei Junlong da Ni Haisheng wadanda suka tuka wannan kumbo sun samu lambar Jarumin kumbon sama janati. Hu Jintao, babban sakatare na kwamiatin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin ya mika musu Lambar yabo na sama janati. Yanzu sai ku saurari labarin da aka ruwaito mana.
A gun wannan taron murna, da farko Wen Jiabao, firayim ministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya karanta kuduri na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa da kwamitin soja na tsakiya game da mika wa Fei Junlong da Ni Haisheng lambar jarumin sama janati da lambar yabo na sama janati. Cikakkiyar nasarar da aka samu a wajen harba kumbo sama janati mai lamba 6 na Shengzhou tana hade da hikima da kokarin da dukkan 'yan kimiya da da kwararru suka yi. Fei Junlong da Ni Haisheng sun nuna jan hali, kuma sun fi da tsoron hatsari sun tuka wannan kumbo janati, kuma sun kamala dawainiya mai tsarki da jam'iyya da jama'a suka mika musu. Domin yaba fifitaccen taimakon da suka yi wa sha'anin kasarmu na tafiya cikin sararin sama, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa da kwamitin soja na tsakiya sun tsai da kudurin mika wa abokai Fei Junlong da Ni Haisheng lambar kwarjini na jarumin sama janati, da lambar yabo na tafiyar sararin sama.
A gun wannan babban taro, Fei Junlong wanda ya tuka kumbon sama janati ya yi jawabi don bayyana yadda suka tuka kumbon sama janati. Ya ce, A wannan gami mu biyu mun yi tafiya a sararin sama har kwanaki 5, mun yi gwajegwajen kimiya kai tsaye, a cikin aikinmu mun yi taimakon juna da kyau, mun yi wannan tafiya tare da nasara.
A gun wannan babban taron murna, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi, inda ya ce, cikakkiyar nasarar da kumbo sama janati mai lamba 6 na Shengzhou ya samu wani muhimmin taimako ne ga 'yan Adam a wajen yin amfani da sararin sama sabo da zaman lafiya. Ya ce, A cikin shekaru 2 kawai mun harba kumbon sama janati mai lamba 5 da ya dauki mutum daya da kumbon sama janati mai lamba 6 da ya dauki mutane biyu, wannan ya alamanta cewa, kasar Sin ta kara samun babbar nasara. Dukkan Sinawa sun yi alfahari da wannan nasarar da muka samu.
(Dogonyaro)
|