Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-27 16:41:02    
Firayim ministan Lebanon ya yi maraba da yarjejeniyar da MDD da Syria suka daddale

cri
A ran 26 ga wata a babban birnin Beruit,Firayim ministan kasar Lebanon Fouad Siniora ya bayyana cewa Lebanon ta yi maraba da yarjejeniya da majalisar dinkin duniya da Syria suka daddale kwanan baya na tuhumar jami'an tsaro biyar na kasar Syria da ake tsammanin suke da hannu a cikin kisan gilla da aka yi tsohon firayim ministan Lebanon Rafik Al-hariri a ofishin majalisar dikin duniya dake a Vienna.

Mista Fouad Siniora ya bayyana cewa gwamnatin Lebanon ta amince da kwamitin bincike na kasa da kasa da jami'ansa kan kisan gilla da aka yi wa Hariri,ya kuma bayyana cewa majalisar dinkin duniya da kwamitin bincike na kasa da kasa da su nuna idon basira da ra'ayin yan ba ruwanmu da kuma kwarewa wajen daddale wannan yarjejeniyar da kasar Syiria.(Ali)