Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-25 18:07:07    
Zababbiyar shugabar kasa ta farko ta Afrika tana da babbar dawainiya a gabanta

cri
A ran 23 ga watan nan Madam Johnson Morris, shugabar kwamitin zabe na duk kasar Liberia ta sanar da cewa, Madam Johnson Sirleaf, tsohuwar ministan kudi mai shekaru 67 da haifuwa ta ci zaben zama shugabar kasa a cikin babban zaben da aka yi bayan yakin basasa a kasar Liberia. Wannan kakkarfar mace ta kasar Liberia ta zama shugabar kasa ta farko da za ta hau karagar mulki ta hanyar zaben jama'a a cikin tarihin Afrika.

A gun taron manema labarum da aka shirya a ran nan a Monrovia. Madam Johnson Morris ta ce, bisa sakamakon zabe na zagaye na biyu, Madam Johnson Sirleaf da ta shiga zabe a madadin Jam'iyyar hadin kai ta samu kuri'u na kashi 59.4 cikin kashi 100. amma shahararren dan wasan kwallon kafa Weah ya samu kuri'u na kashi 40.6 cikin kashi 100 kawai. Bisa yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da rukunoni suka sa hannu a shekara ta 2003, gwamnatin wucin gadi na bayan yakin basasa za ta gama aikinta a watan Janairu na shekara mai zuwa, kuma za ta mika iko ga sabuwar gwamnatin da ke karkashin shugabancin Madam Johnson Sirleaf.

An bayyana cewa, sabuwar gwamnatin da za a kafa a bayan yakin basasa na Liberia tana da muhimmancin gaske ga zaman lafiyar duk kasa da aikin sake raya kasa da zama mai dorewa har ma ga halin da a ke ciki a yammacin Afrika. Kuma an nuna cewa, zabar sabuwar shugabar kasa da aka yi a bayan yakin basasa muhimmin taki ne na farko kawai, akwai kalubale da yawa a gaban aikin shimfida zaman lafiya. Sabuwar shugabar kasa tana da babbar dawainiya a gabanta.

Da farko ko da ye ke kwamitin zabe na Liberia ya sanar da cewa. Johnson Sirleaf ta ci zaben zama shugabar kasa, amma har yanzu ana bincike magudin da aka yi a cikin zabe. Idan ba a iya daidaita hargitsin zabe ba, to, zai zama mahani ga aikin shimfida zaman lafiya.

Sa'an nan aikin sake raya kasa zai zama wani kalubale daban a gaban sabuwar gwamnatin da Johnson Sirleaf za ta shugbanta. Yakin basasa da aka yi cikin dogon lokaci ya barnata tattalin arziki na kasar Liberia gaba daya, kusan an bata dukkan ayyuka na ba da ruwa da wutar lantarki da sufuri, masu rasa aikin yi sun kai fiye da kashi 85 cikin kashi 100. idan kasashen duniya ba za su kai gudummuwa ga Liberia a daidai lokaci ba, to, ba za a iya tabbatar da zama mai dorewa ba. A sa'I daya kuma har yanzu MDD ba ta soke kwalelen dutse da katako da ta ke yi wa Liberia ba. Sabuwar gwamnati kuma za ta yi kokarin kau da cin hanci da rashawa don MDD ta soke kwalelen nan tun da wuri.

A karshe yaya za a warware maganar tsohon shugaba Chaarles Taylor da ke yin gudun hijira ta zama magana mai wuya ga sabuwar gwamnatin kasar Liberia. Sabo da haka mutane suna sa ido ga aikin da sabuwar gwamnati za ta yi a wajen daidaita wannan matsala. (Dogonyaro)