A ran 22 ga wata kwamitin zabe na kasar Kenya ya sanar da cewa, kuri'ar raba gardama da aka gudanar a ran 21 ga wata ta yi watsi da shirin sabon kundin tsarin mulki. Manazarta sun bayyana cewa, wannan sakamako zai jawo wa gwamnatin Kenya wadda ke karkashin shugabancin shugaba Mwai Kibaki wasu wahaloli, amma har ila yau ba su kai ga girgiza matsayin mulkinsa ba tukuna.
A wannan rana Samuel Kivuitu, shugaban kwamitin zabe na kasar Kenya ya sanar da cewa, bisa kididdigar da aka yi an ce, har yanzu yawan mutane masu yin adawa da wannan kundi ya kai kashi 58 bisa 100, a yayin da masu shelar amincewa da shi da yawansu ya kai kashi 42 bisa 100. Ko da yake har yanzu ba a samu sakamakon kuri'a na karshe ba, amma babu tababa an yi watsi da shirin sabon kundin tsarin mulki ta hanyar raba gardama. Cikin jawabin da shugaba Kibaki ya yi ta rediyo mai hoto ya amince cewa shirin sabon kundin ya sha kashi, kuma ya bayyana cewa zai girmama burin jama'a wato zai amince da wannan sakamako.
An shefe shekaru da yawa ana ta yin kwaskwarima ga tsarin mulki na kasar Kenya. Muhimman abubuwan da ke cikin tsarin mulki na yanzu na kasar su ne tsarin mulkin da aka kaddamar a shekarar 1964. Bayan da aka fara tafiyar da tsarin mulki tsakanin jam'iyyu da yawa daga watan Disamba na shekarar 1991, sassa daban-daban kullum suna ta neman yin kwaskwarima ga tsarin daga duk fannoni. Daga baya shugaban Moi na kasar a wancan lokaci ya yi shelar wargaza majalisar kasa, sabo da haka an tsayar da aikin yin kwaskwarima ga tsarin mulki cikin wani lokaci.
Cikin zaben da aka yi a watan Disamba na shekarar 2002, kawancen da ke hade da jam'iyyu masu yin adawa guda 14 ya ci nasara kan kawancen kasar Kenya kuma ya hau kan karagar mulki, Mr. Kibaki kuma ya ci zaben zama shugaban kasar. Daga watan Afril na shekarar 2003 kuma ya sake yin kwarskwarima ga tsarin mulki, amma sabo da bambancin ra'ayin da aka samutsakanin rukunonin da ke cikin kawancen kan matsalar rarraba ikon shugaban kasa da na firayim ministan kasar, shi ya sa aikin yin kwaskwarima ya sake shiga cikin halin kaka ni ka yi, majalisar kasar Kenya kuma ta tsai da kudurin jefa kuri'ar raba gardama a ran 21 ga wannan wata.
Manazarta sun bayyana cewa, bayan da aka yi watsi da wannan sabon tsarin mulki, Jam'iyyar Liberal Democratic Party da kawancen Kenya African National Union za su dukufa kan aikin sa kaimi ga majalisar dokokin kasar don ta yarda da shirin tsarin mulkin da suka rubuta bisa tunanin "firayim minista yana da babban iko, daga bayan kuma sai shugaban kasar", wannan ya kara kawo babban matsi ga gwamnatin Kibaki wadda kullum take nufin tattara duk iko ga shugaban kasa.
Manazarta kuma sun bayyana cewa, bayan da aka yi watsi da wannan sabon tsarin mulki, ko da yake gwamnatin Kibaki tana fuskantar matsaloli da yawa ciki har da daidaita sabani tsakanin rukunonin zaman al'umma da kyautata hadin kai da ake yi cikin gwamnatin, amma ba mai yiwuwa ba ne a girgiza matsayin mulkin gwamnatin. Dalilin da ya sa haka shi ne,
Na farko, shugaba Kibaki yana da babban kwarjini. Na 2, har ila yau Jam'iyyar NAP tana kan matsayin shugabanci cikin majalisar dokokin kasa, rukunoni masu yin adawa da kyar za su hamburar da shugaban kasa ta hanyar jefa kuri'ar rashin amincewa ko ta hanyar tsige shugaban kasar. Ban da wannan kuma gwamnatin Kibaki ta dauki jerin matakai domin sassauta sabanin da ke tsakanin fannoni daban-daban wadanda a ciki har da kara yawan albashin 'yan majalisa da daidaita matsalar yankunan kasar, kuma ta riga ta samu sakamako a gwargwado. (Umaru)
|