Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-24 12:18:00    
Ina dalilin da ya sa sabuwar jam'iyyar Sharon take da makoma mai kyau ?

cri

Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Ina dalilin da ya sa sabuwar jam'iyyar Sharon take da makoma mai kyau ?

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 21 ga watan nan Ariel Sharom , Firayin Ministan kasar Isra'ila ya janye jikinsa daga Jam'iyyar Likud kuma ya kafa sabuwar jam'iyya don shiga babban zabe . Bisa wani sabon binciken da aka yi don neman ra'ayoyin jama'a , an ce , idan yanzu a yi zabe , sabuwar jam'iyyar Sharon za ta zama babbar jam'iyya ta farko . Kuma ana ganin cewa , Mr. Sharon shi kansa zai zama firayin minista mafi dacewa . Sabuwar jam'iyyar Sharon ta kafu ba da dadewa ba , sai ta sami goyon baya sosai , wannan ba ya rabuwa da manufofin siyasa da diplomasiya da kyakkyawan shugabancin Mr. Sharon .

An tsai da lokacin zaben shugaban Jam'iyyar Likud a ran 9 ga watan Disamba . 'Yan takara guda 6 ciki har da Ben Jamin Netnyahu , tsohon ministan kudi da Shaul Mofaz , ministan tsaron kasar Isra'ila za su yi gasar zaman shugaban Jam'iyyar Likud .

Sabuwar jam'iyyar Sharon yanzu an ba ta sunan National Responsibility. Ita ce jam'iyyar masu rashin shiga kowane rukuni bisa ka'idodjin siyasa da tattalin arziki da na zaman al'umma . Musamman a kan matsalar Palasdinu manufofinsu suna da bambanci da na jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayoyi , kuma sin sha bamban da na jam'iyyu masu sassautan ra'ayoyi . Masanan binciken al'amuran duniya sun bayyana cewa , bisa fasahohin Mr. Sharon a wajen tafiyar da harkokin gwamnatin kasar Isra'ila a cikin 'yan shekarun da suka wuce , yana da tunanin tsare-tsaren musamman kan makomar kasarsa da yadda zai daidaita matsalar Falasdinu .

Game da shirin farfado da shawarwarin zaman lafiyar Gabas ta tsakiya , Mr. Sharon yana tsaya kan sharudan da ya kayyade , wato dole ne bangaren Palasdinu ta kai naushi ga ta'addanci kuma ya wargaza kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayoyi. Im ba haka ba shawarwarin tsakanin Isra'ila da Palasdinu ba zai sami hakikanin sakamako ba .

Ban da wannan kuma Mr. Sharon yana da kyakkyawan karfin siyasa da shugabanci wadanda 'yan takaransa suke karanci . Kafar watsa labaru ta kasar Isra'ila ta ce , Mr. Sharon wani shugaba ne wanda yake san yadda zai tsai da kuduri kuma yadda za a tafiyar da shi . Mutanen kasar Isra'ila suna ganin cewa , ba kawai Mr. Sharon yana da tunanin siyasa sosai ba , har yana da hannun siyasa mai kyau .

Amma duk da haka wasu ra'ayoyin jama'a sun dauka cewa , ko da ya ke Mr. Sharon yana da karfin siyasa , amma ba shi da cikakkun dalilai don cin nasara a cikin babban zaben da za a yi a shekara mai zuwa ba .

To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .( Ado)