Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-23 16:16:05    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(17/11-23/11)

cri
Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fayyace a nan birnin Beijing a ran 20 ga wata cewa, za a sayar da abubuwan fatan alheri na wasannin Olympic na Beijing 'yan jariran da ke kawo alheri wato the Friendlies a turance masu araha a farkon wata mai zuwa. Saboda an gabatar da wadannan abubuwan fatan alheri, shi ya sa kamfannonin musamman da suka sami yardar kirar kayayyakin wasannin Olympic za su fara ayyukansu, ta haka za a warware matsalar karancin 'yan jariran da ke kawo alheri. Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya kiyasta cewa, mutane masu yawa sun yi ta alla-alla domin sayen kayayyakin musamman na 'yan jariran da ke kawo alheri har zuwa ranar Sabuwar Shekara da sallar Bazara ta sinawa ta shekarar 2006.

An kammala gasar cin kofin zakara ta wasan kwallon raga wato volleyball ta mata ta duniya a birnin Nagoya na kasar Japan a ran 20 ga wata, kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Brazil ta ci nasara cikin dukan gasanni 5 ta zama zakara. Kungiyar kasar Sin kuma ba ta sake zaman zakara ba, ta zama na uku a wannan gami. Ta lashe kungiyoyin kasashen Poland da Korea ta Kudu da Japan, amma kungiyoyin kasashen Brazil da Amurka sun lashe ta. A kan yi wannan gasa sau daya a ko wadanne shekaru 4, inda kungiyoyin wasan kwallon raga da suka zama zakara cikin gasannin fid da gwani na nahiyoyi daban daban suka yi takara da juna. Za a ci gaba da yin wannan muhimmiyar gasa a kasar Japan a shekarar 2009.

Ran 20 ga wata, dan wasan dambe na kasar Sin Zou Shiming ya zama zakara a matsayin kilogram 48 a cikin gasar fid da gwani ta wasan dambe ta duniya ta karo na 13 da aka yi a birnin Mianyang na kudu maso yammacin kasar Sin. Wannan ne karo na farko da 'yan wasan dambe na kasar Sin suka zama zakarar duniya har zuwa yanzu. A cikin karon karshe, ya lashe wani dan wasan kasar Hungary da ci maki 31 da 13. Kafin wanan kuma, Mr. Zou ya taba lashe shahararrun 'yan wasa da dama. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta shirya gasar fid da gwani ta wasan dambe ta duniya, inda 'yan wasa daga kasashe da yankuna 87 suka yi takara da juna.

An kammala gasar cin kofin gwanaye ta wasan kwallon tennis ta shekarar 2005 a birnin Shanghai na kasar Sin a ran 20 ga wata, wadda muhimmiyar gasa ce da kungiyar ATP ta kan shirya a karshen ko wace shekara. A cikin karon karshe na gasar tsakanin namiji da namiji, dan wasan kasar Argentina David Nalbandian ya lashe shahararren dan wasan kasar Switzerland Roger Federer da ci 3 da 2, ya zama zakara. Wannan ne karo na farko da Mr. Nalbandian ya ci kofin gwanaye. Ko da yake Mr. Federer ya ci tura, amma ya tabbatar da zaman lambawan a jerin 'yan wasan kwallon tennis maza na duniya na shekarar 2005. 'Yan wasan kasar Faransa Michael Llodra da Fabrice Santoro sun zama zakaru cikin gasar tsakanin maza biyu biyu. Za a yi gasar cin kofin gwanaye sau 3 a jere a birnin Shanghai na kasar Sin daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2007.

Kungiyoyin wasan kwallon kafa na maza na kasashen Sin da Bulgaria sun yi kunnen doki a cikin gasar sada zumunta ta wasan kwallon kafa da aka yi a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin a ran 16 ga wata, wannan ne gasa ta karshe da kungiyar kasar Sin ta yi a gida a shekarar da muke ciki.(Tasallah)