Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-22 17:45:47    
An yi yawon shakatawa a tabkin Qinghai na kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a wannan shiri namu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayani da wakilin gidan redion kasar Sin ya taho da shi, bayan da ya kai ziyara a tabkin Qinghai na kasar Sin.

A arewa maso gabashin filaton Qingzang na kasar Sin, ya kasance da wani tabki mai sunan tabkin Qinghai, wanda fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu hudu da dari biyar. Tun da da can, tabkin Qinghai ya zama wani shahararren wurin yawon shakatawa. A tabkin, Ban da abubuwa masu ban sha'awa na halitta, har ma zaman da mutanen kabilu daban daban suke yi a bakin tabki shi ma yana jawo hankulan mutane da yawa.

Wakilinmu ya zo gundumar Gonghe mai cin gashin kai da mutanen kabilar Zang ke cunkushe. Shugaban hukumar yawon shakatawa ta gundumar Malam Li Yuanlin ya gabatar wa wakilinmu a kan yadda tabkin Qinghai ya kafu. Kafin shekaru miliyan 200, filaton Qingzang shi ne wani babban teku, sai an yi wata babbar girgizar kasa, sa'an nan manyan duwatsu sun tashi, sai tekun ya zama tabkuna daban daban, tabkin Qinghai shi ne daya da ke cikinsu.

Domin bautawa 'yan yawon shakatawa da kyau, gundumar Gonghe ta sayi manyan jiragen ruwa da yawansu ya kai 10. Malam Li Yuanlin ya bayyana cewa,

'A cikin jirgen ruwa a tabkin Qinghai, 'yan yawon shakatawa suna iya zagaya a wurare masu ban sha'awa guda biyu. Daya shi ne tsibirin tsuntsaye, inda ake fi samun tsuntsaye a kasar Sin har ire-irensu ya zarce 40; wani wuri daban shi ne dutsen Haixin, dutsun wurin shakatawa ne na addini wanda ke da dogon tarihi.'

Tsibirin tsuntsaye yana arewa maso yammacin tabkin Qinghai, fadinsa ya kai muraba'in kilomita 0.8. A lokacin bazara, tsuntsaye masu yawan gaske su kaura wurin daga kudancin kasar Sin da kudu maso gabashin Asiya, a watan Afrilu da na Mayu, tsuntsayen su fara haifar kwai, a watan Yuni da na Yuli, kananan tsuntsaye su fara girma, su tashi a nan, sun sauka a can?Tsibirin ya zama wata daular tsuntsaye.

Amma ina dalilin da ya sa tsibirin ya zama gidan tsuntsaye? Sabo da yanayinsa mai dumi ne, a cikin tabkin Qinghai, akwai kifaye da ciyawa na ruwa da yawa, dukkan wadannan su jawo hankulan tsuntsye sosai da sosai. Domin kare muhalli a tsibirin tsuntsaye da kallon tsuntsayen, gwamnatin wurin ta kafa wata tashar kallon tsuntsaye a tsibirin. Sai 'yan yawon shakatawa suna iya kallon tsuntsye sosai a tashar. Wata 'yar yawon shakatawa da ta zo daga lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin Malama Zhou Ying ta bayyana cewa,

'Ban taba zama tare da tsuntsaye da yawan haka ba, wannan shi ne abu na musamman gare ni. Ina godiya sosai ga wannan Aljanna ta tsuntsaye a duniya.'

Dutsen Haixin shi ne wuri daban mai ban sha'awa a tabkin Qinghai. A kan dutsen, akwai hasumiya da zane-zanen addinin Buddah. Kana iya hango dukkan tabkin Qinghai, wanda yake kamar wani kyakkyawan zane.

Ban da wadannan wuraren yawon shakatawa biyu, kana iya kallon yadda mutanen kabilun wurin suke zama.

Mutane na kalibu fiye da 20 suna zama a bakin tabkin Qinghai, amma babbar kabila ita ce kabilar Zang. Domin 'yan yawon shakatawa suna fahimatr al'adu na musamman na kabilar Zang, gwamnatin wurin ta shirya bukukuna da yawa a bakin tabkin Qinghai, kamar rera waka a bikin aure da matasa maza da mata suka yi domin 'yan yawon shakatawa.

A halin yanzu dai, wurare masu ban sha'awa da zaman da kabilun wurin ke yi suna kara jawo hankulan 'yan yawon shakatawa daga kasar Sin da kasashen waje. A ko wace shekara yawan 'yan yawon shakatawa ya karu fiye da kashi 50 bisa dari, a shekarar da ta gabata, yawansu ya kai dubu 50, da yawa da ke cikinsu su zo ne daga kasashen waje. Kyakkyawan tabkin Qinghai da jama'ar kabilun wurin suna maraba kuma suna jiranka..(Danladi)