Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-22 16:00:38    
Ziyarar da Bush takaitawa ce ga shawarwarin da aka yi a wannan shekara a tsakanin Sin da Amurka

cri

Daga ran 19 ga wannan wata, shugaba Bush na Amurka ya kawo ziyararsa ta karo na 3 a kasar Sin tun shekaru 5 da suka wuce na bayan da ya shiga cikin fadar white house wato fadar gwamnatin Amurka, kuma ya yi muhimman aikace-aikacensa a ran 20 ga wata a nan kasar Sin. A wannan rana, Mr. Bush da shugabannin kasar Sin wato Mr. Hu Jintao da Mr. Wen Jiabao sun samu ra'ayi daya mai muhimmanci kan batun ciyar da dangantakar hadin gwiwa mai amfani tsakanin Sin da Amurka a karni na 21 kuma daga duk fannoni. Dangane da ziyarar da Mr. Bush ya kawo wa kasar Sin a wannan gami, masanan kasar Sin sun bayyana cewa, ziyarar nan ta zama takaitawa ce ga shawarwarin da aka yi a wannan shekara a tsakanin Sin da Amurka kuma daga duk fannonni har ma ta kai wani sabo mataki. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan bayani.

A ran 20 ga wannan wata, Mr. Bush ya yi shawarwari a tsakaninsa da shugaba Hu Jintao da firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin bi da bi, bangarorin 2 sun yi musanyar ra'ayoyinsu don kara kyautata dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma sun samu ra'ayi daya mai muhimmanci. Shugabannin kasashen 2 gaba dayansu sun bayyana cewa, Sin da Amurka za su kara fahintar juna da kara samun ra'ayi daya da kara amince wa juna, da ciyar da dangantakar hadin gwiwa mai amfani tsakanin Sin da Amurka a karni na 21 kuma daga duk fannoni. A gun ganawar da aka yi tsakanin Mr. Bush da Mr. Wen, bangarorin 2 sun nuna hali mai yakini kan matsalolin da suka bullo cikin hadin gwiwar cinikayya da ake yi tsakaninsu. Bangarorin 2 kuma sun tsai da takardar "ba da shawara kan matakan da Sin da Amurka za su dauka tare domin fama da annobar murar tsuntsaye".

Kan mu'amalar da ake yi tsakanin shugabannin kasar Sin da Amurka a wannan gami, Mr. Liu Xuecheng, direktan ofishin binciken nahiyar Amurka ta cibiyar binciken matsalolin kasashen duniya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Shawarwarin da aka yi a wannan gami a tsakanin shugabannin koli na kasar Sin da Amurka ya zama takaitawa ce ga shawarwarin da aka yi a wannan shekara a tsakanin kasashen 2 kuma daga duk fannonni har ma ya kai wani sabon mataki, ba'idin haka kuma ya zama wani ci gaba ne da aka samu bayan ganawar da aka yi a watan Satumba na wannan shekara a birnin New York a tsakanin shugaba Hu da shugaba Bush."

Mr. Liu ya ci gaba da cewa, "Tun bayan da gwamnatin Bush ta hau kan karagar mulki a shekarar 2001 zuwa yanzu, hanyar da ake bi wajen dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka tana cike da kalmadai-kalmadai, musamman ma Amurka ta yi wani sauyin manufar da ta tsayar kan kasar Sin, wato shi ne ta canja matsayinta daga "mai yin gasa wajen muhimman tsare-tsare" zuwa "mai yin cudanya wajen samun moriya", wannan ya zama wani babban sauyi ne wajen muhimman tsare-tsare."

Kafin shekaru 30 da suka wuce, Mr. Bush ya taba hawa basukur a nan birnin Beijing, a gun wannan ziyarar kuma bisa matsayinsa na shugaban kasar Amurka ne ya sake hawa basukur a nan. Mr. Liu ya yi bayani a kan wannan batu cewa, "Hawan basukur ya zama wani aiki ne da Mr. Bush ke son yin sa, ya yi haka domin tunawa da kasar Sin a lokacin samartakarsa. Daga wani fanni daban kuma ya bayyana halin jituwa da ake ciki wajen dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka". (Umaru)