Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-19 21:07:14    
Raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ya zama ra'ayi daya ga rukunoni daban daban na bangarorin biyu

cri
A ran 19 ga wannan wata, shugaban kasar Amurka W.Bush zai soma  ziyara a kasar Sin, wannan ne ganawar da shugabannin kasashen biyu za su sake yi a cikin shekarar da muke ciki. Bisa matsayinta na kasa mai tasowa kuma kasa mafi girma da ka na  mafi wadata, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tana daya daga cikin hulda mai muhimmanci da ke tsakanin bangarori biyu a duniya, saboda haka ziyarar da W.Bush zai yi a kasar Sin ta jawo hankulan mutane sosai da sosai. Kwanan baya, manyan shugabanni da shahararrun mutane na kasashen biyu sun taru a nan birnin Beijing, inda suka yi bincike kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta a da kuma a yanzu da  nan gaba. Mai da hankali ga babban fanni, da kuma zaunar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu da yalwata ta ya riga ya zama ra'ayi daya ga rukunoni daban daban na kasar Sin da na Amurka da ke halartar taron .

Ziyarar da W.Bush zai yi a kasar Sin za ta zama ziyara ta karo na uku tun daga lokacin da ya ci zaben zama shugaban kasa har zuwa yanzu, wannan ne karo na farko da shugabannin kasar Amurka suka yi wajen yi wa ksar Sin ziyara . A lokacin da W.Bush ya hau kujerar shugaban kasar Amurka a karo na biyu, kasar Sin da kasar Amurka sun riga sun sami ra'ayi daya mai muhimmanci a kan yunkurin raya huldar hadin guiwa mai amfani a tsakaninsu.

Kwanan baya, mashahurin dan diplomasiya kuma tsohon ministan harkokin waje na kasar Sin Qian Qichen ya bayyana a gun taron tattaunawa da aka shirya a kan batun huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka cewa, a cikin 'yan shekarun nan biyu da suka wuce, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta sami yalwatuwa da kyau a dukan fannoni, wannan ba ma kawai yana da amfani ga bangarorin biyu ba, hatta ma na da amfani ga zaman lafiya da bunkasuwa na duk duniya da na shiyya shiyya. Ya ce, kara dankon huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ya yi jagorar karuwar tattalin arziki ta shiyya shiyya da ta duk duniya, bisa kokari tare da aka yi a tsakanin kasar Sin da Amurka da sauran bangarori daban daban ne, shawarwarin da ke tsakanin bangarori 6 kan batun nukiliyar Zirin Korea ya kuma sami ci gaba, sa'anan kuma kasar Sin da kasar Amurka suna ta yin shawarwari da daidaituwa a kan sauran batutuwa, saboda haka yana ganin cewa, lokacin da za a daidaita huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, ya kamata kasashen biyu su mai da muhimmancinsu ga manyan tsare-tsare na duniya, kuma kasashen biyu su yi kokari don dacewa da gudanarwar zamani da kuma kara inganta hadin guiwarsu da samun moriyar juna, wannan ya dace da babbar moriyar jama'ar kasashen biyu.

Tsohon shugaban kasar Amurka George Bush shi ma ya bayyana cewa, shi da dansa W.Bush dukansu suna ganin cewa, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tana kasancewa cikin hali mafi kyau a tarihi, kuma a madadin dansa ne, tsohon Bush ya bayyana cewa, ya yi fatan bangarorin biyu wato Sin da Amurka za su yi kokari tare don cika damar samun fahimtar juna da suka taba rasa ta a da . Ya ce, kodayake za a bi rikitacciyar hanya wajen raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, amma makomarta tana da haske. Ta hanyar kokarin da za mu yi, tabbas ne za a kawar da rashin fahimta a tsakanin bangarorin biyu, abubuwan tarihi sun gaya mana cewa, kasar Sin da kasar Amurka bai kamata ba su zama abokan gaba.

Amma ya kamata a amince cewa, ya kasance da sabani a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Game da wannan, ya kamata bangrorin biyu su kara wa juna fahimta da neman ra'ayi daya tare da kasancewar bambancin ra'ayi,mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jechi ya bayyana cewa, batun Taiwan yana jibinci mallakar kasa da cikakken yankin kasa na kasar Sin, in a daidaita batun da kyau, to za a iya samun babban tabbaci ga raya da zaunatar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu. (Halima)