Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-18 15:09:59    
Jawabi da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi a majalisar dokoki ta kasar Korea ta Kudu

cri
Ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi a majalisar dokoki ta kasar Korea ta Kudu wanda takensa shi ne " kara dankon aminci da kara karfin hadin guiwa don samun makoma mai kyau". A cikin jawabinsa, Mr Hu Jintao ya bayyana ra'ayoyin bangaren Sin a kan hulda a tsakanin Sin da Korea ta Kudu da halin da ake ciki a Asiya da batun nukiliya na zirin Korea da dai sauransu.

Mr Hu Jintao ya yi jawabinsa ne a dakin tattaunawa na majalisar dokoki ta kasar Korea ta Kudu, inda 'yan majalisar 200 suka saurari jawabin.

Bayan da ya waiwayi ci gaba da aka samu wajen yalwata huldar da ke tsakanin kasashen biyu tun da aka kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu, Mr Hu Jintao ya ce, a cikin shekaru 13 da suka wuce tun bayan kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da Korea ta Kudu, an yi ta samun babban ci gaba wajen bunkasa huldar nan. Yanzu lokaci ne mafi kyau ga huldar nan. Amincin da ke tsakanin kasashen biyu ya shiga cikin zukatan jama'a kwarai, abubuwa da za su wakana nan gaba game da huldar suna da kyaun gaske.

Mr Hu Jintao ya takaita sakamako da aka samu wajen yalwata huldar da ke tsakanin Sin da Korea ta Kudu daga duk fannoni, ya ce, "mu tsaya tsayin daka wajen gudanar da manufar aminci irin ta makwabtaka, mu yi kokri wajen kare zaman lafiya da zaman karo a kasashe da ke makwabtaka da mu, mu nemi samun ci gaba ta hanyar yin hadin guiwa bisa halin da ake ciki, mu yi kokari wajen neman samun bunkasuwa cikin lumana don samun moriyar juna, mu nace ga nuna girmamawa ga juna, mu amince da juna, mu yi zaman daidaici, kuma mu yi kokari wajen neman yalwata huldar da ke tsakanin kasashenmu biyu lami lafiya cikin dogon lokaci da zaman karko."

Bayan haka Mr Hu Jintao ya kara da cewa, neman zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa da neman hadin guiwa buri daya ne ga jama'ar kasashen Asiya. Yanzu, nahiyar Asiya ta sami damar farfado da ita har ba a taba ganin irinta ba a da, sa'an nan kuma tana fuskantar kalubale mai tsanani. Ya ce, "bisa sabon halin da ake ciki dangane da kasancewar dama da kalubale da wahalhalu da kyakkyawar makoma, wani babban aiki da gwamnatocin kasashen Asiya da jama'arsu ke fuskanta shi ne, yaya za su yi don mayar da duniya da ta zama wata duniya mai jituwa cikin hadin guiwarsu, inda ake sulhuntawa a fannin siyasa, a yi zaman daidaici don samun noriyar juna a fannin tattalin arziki, a amince da juna kuma a taimaki juna a fannin kare zaman lafiya, haka zalika a yi ma'amalar al'adu da yin koyi da juna. Sin da Korea ta Kudu dukansu kasashen Asiya ne masu muhimmanci. Sabo da haka ya kamata, su ba da babban taimakonsu wajen tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a Asiya."

Dangane da batun nukiliya na zirin Korea, Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, "kullum kasar Sin tana tsayawa kan matsayinta a fili kan batun nukiliyar zirin Korea. Muna nuna cikakken goyon bayanmu ga duk harkoki da ake yi wajen kare zaman lafiya da zaman karko a zirin nan. Ra'ayinmu shi ne a mayar da zirin Korea da ya zama yankin da babu makaman nukiliya a ciki, a daidaita batutuwa da ke jawo hankulan bangarori daban daban ta hanyar tattaunawa, kuma za mu yi kokari ba tare da kasala ba a kan wannan."

Kafin Mr Hu Jintao ya yi jawabi, Mr Kim One Ki, shugaban majalisar dokoki ta kasar Korea ta Kudu ya sake yin maraba da ziyarar da Mr Hu Jintao ke yi a kasar. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa. Ziyarar da Mr Hu Jintao ke yi a wannan gami tana da matukar muhimmanci. (Halilu)